Ba a yin nasara kan gaskiya, saidai awahalar da ita !



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KA QARA JURIYA KAMAR YADDA 'DAN'UWANKA SAYYID ZAKZAKY (H) YAYI

Da ace azzalumai na daukar darasi to, da zuwa yanzu haka babu wani sauran zalunci a doron qasa, sai dai har duniya ta qare ba za su wa'azantu ba saboda hanyar kenan wacce ba ta canzawa.

Annabi Ibrahim (A.S) har Rijiyar wuta aka tona masa aka sanya shi ciki amma hakan bai sa azzalumai sunyi nasara kansa ba kuma shima bai canza daga aqidarsa ba. Tarihin Annabi Musa (A.S) ma bai buya ga al'umma ba, domin babu irin nau'in zalunci da ba a qulla masa tare da cutar da mabiyansa ba, amma a hakan shi yayi nasara kan azzalumai da zaluncinsu.

Na qarshen cikinsu daga Manzanni (A.S) shine Annabi Muhammad (S.A.W.W) kuma wanda yafi kowa matsayin wajen Allah, yafi kowa tunani da hikima wajen isar da saqon Allah, amma shi yafi kowa cutuwa daga cikin masu da'awar kadaita Allah da aiwatar da adalci. Da ace hikimar wa'azi ce ke hana a cutar da mutum, to, haqiqa da ko kallon banza ba za ayi masa ba ballantana ace ayi nufin kashe shi.

Idan kaga malami na da'awa bai sami qalubale daga sauran 'yan'uwansa masu da'awa ba, kuma bai ci karo da zaluncin mahukunta ba, wannan malamin ba magajin Annabawa bane kuma ba irin aikinsu yake yi ba, domin qaryarka kace hikimar wa'azinsa ne da iya mu'amala ta hana a cutar da shi.

Babu irin nau'in mataqi na kawo qarshen rayuwar mutum wacce Gwamnatin zalunci ta Muhammadu Buhari bata dauka don ganin bayansa ba, amma Allah ya nuna musu cewa mutuwa da rayuwa a Hannunsa take.

Tabbas gaskiya na shan wahala, amma kuma ba a yin nasara a kanta, kuma ba a iya lullubeta. Da ace ana iya lullube gaskiya a kasa fahintarta to, da yanzu ba a san haqiqanin wasiyyan Manzon Allah (S.A.W.W)ba, kuma da ba a san iyalan Annabi (A.S) sunfi kowa daraja ba.

Wannan jarrabawa da ka fada cikinta sakamakon kyawawan ayyukanka ne, kuma Allah ya fi kowa kishinka da sanin halin da kake ciki, amma ya barka a haka kamar yadda yabar Sayyid Zakzaky (H) cikin matsayi mafi muni fiye da naka har tsahon shekaru shida ba kadan, amma bisa iko naSa ga shi ya fito kuma da'awarsa bata canza ba, kuma azzalumai sun dau qasqanci.

ALLAH YA QARA TSARE KA DA TAIMAKONKA DA SANYA MAKA HAQURI DA JURIYA IRIN TA SAYYID ZAKZAKY (H).

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

8th December, 2021/ 4th Jimada-Ulah, 1443.

4 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post