Yau Latala 2/11/2021 ne Al'umma Masoya Annabi Muhammad (Saww) Suka Gudanar da Zagayen Ralin Mauludi a Garin Sabuwar Rijiya Dake Jihar Neja, Daruruwan Jama'a ne Maza da Mata Yara da Manya suka samu Halarta wan nan Taron Domin Nuna Soyayyar su ga Manzon Tsira Annabi Muhammd (S).
Mahalarta Taron Sun Hada "Yan Dariqar Tujjaniyya da Khadiriyya da kuma 'Yan Uwa Al'majiran Sayyid Zakzkay (H) na Garin, Kamar dai Yanda zaku iya gani a cikin Hotona Irin Yanda "Yan uwan Al'majiran Sheikh Ibrahim El'Zakzaky (H) suke Taka Fareti na Girmamawa ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (Saww).
An Fara wan nan Zagayen ne Tun da Safiyar Yau Talata Taron ya Dauke Tsawon Lokaci Yana Gudana inda Taron ya samu Muhallin Kammala shi a Primary School Dake Cikin Garin na Sabuwar Rijiya, inda nan ne aka Rufe Taron Ayi Lafiya kuma An'kammala Lafiya.
Ga Kadan daga cikin Hotonan da Wakilan Shafin Kontagora Media Forum suka dauko maku nan, da Fatan Allah ya Maimaita mana ya Nuna muna na Badin badada Lafiya.
@Shana Islam.
2/11/2021.