Daga Almustapha A Abdullahi.
Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) na da'irar talatan mafara sun gabatar da khataman maululidin Manzon Allah (S) a safiyar yau Lahadi.Babban bako mai jawabi shine Wakilin yan uwa na yankin Jos da kewaye wato Sheikh Adamu Tsoho Jos.
Sheikh Adamu Tsoho Jos sun dauki dogon zango suna tafiya Amman duk da wannan doguwar tafiyar Sheikh beyi kasa a gwuwa ba ya amsa gayyatar su kuma yazo ya isar da sakon Maulud dana Harka Islamiyya.
Daga cikin yankin jawabin da Sheikh ya gabatar ya tabo bayani akan zalincin da ake wa yan arewa musamman ma na wannan yankin zamfara da kewaye inda suka kulle "Network" ba daman ka gaisa da Dan uwan ka dake wani waje kuma babu daman asan kashe kashe da yan ta'adda suke yi, a lokaci guda ga tashin hankali da ake fama dashi mutum zai fita neman abinci amman yana fargaban kar a sace shi kar a kashe da dai sauransu.
To Sheikh ya fadi hanyar da za'abi a sami saukin wannan fargaba da ake ciki kaman dai yadda ya saba fada a sauran guraren taruka kalan wannan inda yake cewa matukar ana so aga daidai to wajibi ne a komo zuwa ga littafin Allah a saki komai a kama Addini to anan Allah zai tausayawa wannan Al'ummar abubuwa zasuyi sauki komai zai dawo daidai arziki zai yalwata.
1/Rabi'ul Sani/1443H
7/November/2021