Yadda aka gudanar da kayataccen Mauludin Manzon Allah (S) a halkar Imam Zainul-Abideen Kudan


'Yan 'uwa Musulmi Almajiran sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na halƙar Imam Aliyu zainul abidin sun, gudanar da taron mauludin fiyayyan halita Annabi Muhammad (S) acikin garin Kudan ajiya litini ne suka gudanar da taron mauludin da suka saba shirwa duk shekara.

Bayan buɗe fili da addu'a an gabatar da karatun Alqur'ani mai girma, sai Ittuhadin shu'ar mawaƙan sautul huda suka gudanar da baituka da gwala-gwalan bai tika, da yabo ga Manzon rahama (S) sanan wakilin 'yan uwa malam Muhammad Junaidu sani Kudan inda ya gabatar da babban baƙo mai jawabi Shaikh Ibraheem Aƙilu zariya, kafin zuwan mai jawabin shehin malamin ya yi bayani akan Shaikh Ibraheem Aƙilu inda yake cewa malam aƙilu yana ɗaya daga cikin mutanan da Shaikh Zakzaky (H) ya tura su, ƙasar waje yin karatu tare da su Hamza lawal ataƙaice.

Shehin malamin, Shaikh aƙalu ya fara jawabi da taɓo martabar Manzo Allah inda yake cewa lallai wannan babbar rahama ce da Allah ya ba musulmi duniya gaba ɗaya, Allah (T) yana mai farin ciki da masu murna da ranar haihuwar Manzon rahama (S), bisa wannan ne nake cewa Allah ya sakawa Shaikh Ibraheem Zakzaky da alkairi sanan ainihin 'yan uwa na matasa sumiƙe tsaye wajan nuna farin cikinsu da nai man ilimi.

Shaikh Ibraheem Aƙilu zariya ke nan cikin jawabin sa acikin garin Kudan da ya gabatar ajiya Litinin .








Daga wakilinmu na Kudan

 Faruq Sani kudan 

16/11/2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post