Siffofin Waɗanda Imani Bai Shiga Zukatansu ba !


 DUK WANDA KAGA YA DAMU DA GANIN LAIFIN WANI BA MUMINI BANE 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Sau da yawa aikin mutum shi ke fassara shi wanene, idan mutumin kirki ne ayyyukansa ne zasu bayyana shi. Haka kuma idan ba mutumin kirki bane ayyukansa ne za su bayyana shi wanene ba tare da sai ka ce wani abu a kansa ba.

Za ka tarar aikin wasu a kowanne lokaci shine su bibiyi sirrin mutum don suga gazawarsa har ya zama makami na yaqarsa ba tare da cewa su suna bibiyar tasu gazawar ba.

Manzon Allah (S.A.W.W) ya gargadi masu wannan siffa kamar yadda yazo cikin hadisin dake biye.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

19333- حَدَّثَنَا أَسْوَدُ بْنُ عَامِرٍ شَاذَانُ , أَخْبَرَنَا أَبُو بَكْرٍ يَعْنِي ابْنَ عَيَّاشٍ , عَنْ الْأَعْمَشِ ، عَنْ سَعِيدِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ جُرَيْجٍ ، عَنْ أَبِي بَرْزَةَ الْأَسْلَمِيِّ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " يَا مَعْشَرَ مَنْ آمَنَ بِلِسَانِهِ , وَلَمْ يَدْخُلْ الْإِيمَانُ قَلْبَهُ ، لَا تَغْتَابُوا الْمُسْلِمِينَ ، وَلَا تَتَّبِعُوا عَوْرَاتِهِمْ ، فَإِنَّهُ مَنْ يَتَّبِعْ عَوْرَاتِهِمْ يَتَّبِعْ اللَّهُ عَوْرَتَهُ ، وَمَنْ يَتَّبِعْ اللَّهُ عَوْرَتَهُ يَفْضَحْهُ فِي بَيْتِهِ " .

Aswadu Bn Aamir Shaazani ya bamu labari, Abubakar (Ibn Ayyash) ya bamu labari, daga A'amashi, daga Sa'eed Bn Abdullahi Bn Juraij, daga Abu Barzatal-Aslamiyyi yace: Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" YAA KU TARON WANDA KAYI IMANI DA HARSHENSA ALHALI IMANI BAI SHIGA ZUCIYARSA BA ! KADA KUYI GIBAR (backbiting) MUSULMAI, KUMA KADA KU BIBIYI AL'AURARSU (sirri nasu), DOMIN SHI WANDA YA BIBIYI SIRRINSU TO, ALLAH ZAI BIBIYI (nasa) SIRRIN. KUMA DUK WANDA ALLAH YA BIBIYI NASA SIRRIN ZAI RISKE SHI (har) CIKIN 'DAKINSA."

(Musnad Ahmad, hadisi mai lamba 19,333)

              DARASI

          ____________

Kamar yadda Allah ke rufa mana asirin mu duk da cewa muna butulce Masa , haka ya kamata ace muma muna kauda kai daga ganin laifi ko gazawar waninmu. Domin yin hakan zai sa mu mance da tamu gazawar ballantana mu gyara.

Kuma matuqar aikinmu ya zama shine a kullum binciken qwaqwab ga dan'uwanmu wanda ayyukan aikhairinmu bai yi kusan nasa ba, to, Allah zai iya rufa masa asiri ya kuma bibiyi namu. Idan kuwa Allah ya bibiyi namu babu inda za muje ba tare da ya risko mu ba.

Ba zai zama laifi ba don ka binciko munanan ayyukan wanda aka ce shine wai shi za kabi ka shiryu a addini alhali shi din ba ahlin hakan bane, domin bayyanar da gazawar tasa ita za ta tabbatar da cewa ashe dai shi ba madubi (mirror) bane.

Amma in ya zama dama babu wanda yace shine madubinka, to, bibiyar ganin gazawarsa rashin imani ne. Domin yin hakan ba zai amfanar dakai ba ballantana ya amfanar da waninka, idan kuwa babu ko daya (1) daga cikin biyun nan, to, bibiyar tasa ma sharri ne zai zama gare ka.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

9th November, 2021/ 5th Rabi'us- Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post