Ruwayoyin da suka tabbatarda da Halifa Umar Bn Khaddabi ya fi kowa yiwa Annabi (S) rashin mutumci daga cikin Sahabbai


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BA ZA SU TABA IMANI BA HAR SAI KAI KAKE YIN HUKUNCI A TSAKANINSU......

Muhammad (S.A.W.W) shine mafifici kuma shugaba cikin dukkan Annabawa da Manzanni (A.S) wanda ba ya magana ko aiki bisa son zuciyarsa. Duk wani abinda kaga yayi ko kaji ya fada, to, umarni ne daga Allah wanda ba a tambayarsa abinda ya aikata.

Ya zo cikin Alqur'ani mai tsarki inda Allah (T) ke cewa;

وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ (٣ )

إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٞ يُوحَىٰ (٤)

" KUMA BA YA MAGANA BISA SON ZUCIYA."

" (Maganarsa ko aikinsa) BAI KASANCE BA FACE WAHAYI NE A KAYI MASA."

      (Suratul-Najmi:3-4)

Wadannan ayoyi na nuna mana ne cewa idan kaga yayi wani aiki ko yayi umarni, to, kabi kawai matuqar kana da imani, domin umarnin Allah mai yin abinda yaga dama yake bi.

Duk hukuncin da yayi sai ka sallama ko da kuwa bai zo daidai da son ranka ba, idan kuma kayi naka hukuncin ba ka zama mai imani ba.

Allah (S.W.A) ya bayyanar mana kamar haka;

وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٖ وَلَا مُؤۡمِنَةٍ إِذَا قَضَى ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ أَمۡرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ ٱلۡخِيَرَةُ مِنۡ أَمۡرِهِمۡۗ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلٗا مُّبِينٗا (٦٣)

" BA YA KASANCEWA GA MUMINI KO MUMINA IDAN ALLAH DA MANZONSA YA HUKUNTA WANI AL'AMARI YA ZAMA AKWAI WANI ZABI GARE SU DAGA AL'AMARINSU. DUK WANDA YA SABAWA ALLAH DA MANZONSA, HAQIQA YA BACE BATA BAYYANANNIYA!"

         (Ahzab, aya 36)

Amma wani abin mamaki shine, babu wani abinda Annabi (S.A.W.W) zai yi na aiki ko umarni sai Umar Bn Khaddab yayi masa jayayya ta hanyar yi masa gyara da nufin ya fi shi sanin daidai.

Wannan kuwa ya auku ko muce ya zo cikin manyan littafai na Sunnah kan abubuwa daban-dabam masu yin nuni game da haka. Saboda haka za mu kawo ko da misali biyu ne a matsayin hujja da toshe bakin maqaryata masu ganin Umar ya fi Manzon Allah (S.A.W.W).

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(1)-

حدثني زهير بن حرب حدثنا عمر بن يونس الحنفي حدثنا عكرمة بن عمار قال حدثني أبو كثير قال حدثني أبو هريرة قال كنا قعودا حول رسول الله صلى الله عليه وسلم معنا أبو بكر وعمر في نفر فقام رسول الله صلى الله عليه وسلم من بين أظهرنا فأبطأ علينا وخشينا أن يقتطع دوننا وفزعنا فقمنا فكنت أول من فزع فخرجت أبتغي رسول الله صلى الله عليه وسلم حتى أتيت حائطا للأنصار لبني النجار فدرت به هل أجد له بابا فلم أجد فإذا ربيع يدخل في جوف حائط من بئر خارجة والربيع الجدول فاحتفزت كما يحتفز الثعلب فدخلت على رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال أبو هريرة فقلت نعم يا رسول الله قال ما شأنك قلت كنت بين أظهرنا فقمت فأبطأت علينا فخشينا أن تقتطع دوننا ففزعنا فكنت أول من فزع فأتيت هذا الحائط فاحتفزت كما يحتفز الثعلب وهؤلاء الناس ورائي فقال يا أبا هريرة وأعطاني نعليه قال اذهب بنعلي هاتين فمن لقيت من وراء هذا الحائط يشهد أن لا إله إلا الله مستقينا بها قلبه فبشره بالجنة فكان أول من لقيت عمر فقال ما هاتان النعلان يا أبا هريرة فقلت هاتان نعلا رسول الله صلى الله عليه وسلم بعثني بهما من لقيت يشهد أن لا إله إلا الله مستيقنا بها قلبه بشرته بالجنة فضرب عمر بيده بين ثديي فخررت لاستي فقال ارجع يا أبا هريرة فرجعت إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فأجهشت بكاء وركبني عمر فإذا هو على أثري فقال لي رسول الله صلى الله عليه وسلم ما لك يا أبا هريرة قلت لقيت عمر فأخبرته بالذي بعثني به فضرب بين ثديي ضربه خررت لاستي قال ارجع فقال له رسول الله صلى الله عليه وسلم يا عمر ما حملك على ما فعلت قال يا رسول الله بأبي أنت وأمي أبعثت أبا هريرة بنعليك من لقي يشهد أن لا إله إلا الله مستيقنا بها قلبه بشره بالجنة قال نعم قال فلا تفعل فإني أخشى أن يتكل الناس عليها فخلهم يعملون قال رسول الله صلى الله عليه وسلم فخلهم 

Zuhri Bn Harb ya namu labari, Umar Bn Yunus Al-Hannafiy ya bamu labari, Ikrimata Bn Ammar yace: Baban Katheera ya bani labari yace: Abu Hurairata ya bani labari yace: 

" Mun kasance zaune a gefen Manzon Allah (S.A.W.W), tare damu akwai Abubakar da Umar cikin jama'ar, sai Manzon Allah (S.A.W.W) ya tashi a tsakaninmu ya bace daga ganinmu, sai muka ji tsoron kada ya yanke (mu bar ganinsa) tsakaninmu. Sai muka firgita muka tashi, na kasance nine farkon wanda na fara firgita, na fita ina neman Manzon Allah (S.A.W.W) har ma tafi wani shingen Ansar na Baniy Najjar, na kewaya shi ko zan sami qofa (na shiga), amma ban samu ba. Sai ga Rabi'a yana shiga (shingen) ta gefensa daga wata rijiya daga waje. Shi kuwa Rabi'a mai qiba ne, sai yayi sanduwa (stealthily) kamar yadda Dila ke yin sanduwa, sai ya shiga zuwa ga Manzon Allah (S.A.W.W). Sai yace: 

" ABU HURAIRATA NE ?" Nace: Eh yaa Ma'aikin Allah ." Sai yace:

" ME KE TAFE DA KAI ?" Nace: Ka kasance a tsakaninmu sai ka tashi ka buya daga ganinmu, sai muka ji tsoron kada ka rabu damu. Shine muka firgita, na kasance farkon wanda ya fara firgita, shine nazo wannan shinge nayi sanduwa ( very stealthily) kamar yadda Dila ke yin sanduwa , kuma wadannan mutane na biye dani. Sai yace:


" YAA ABU HURAIRATA ! (ya kira ni) ya bani takalmansa yace:

" KA TAFI DA WADANNAN TAKALMA NAWA ! DUK WANDA KA SAMU DAGA BAYAN WANNAN SHINGE WANDA KE SHAIDAWA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH, KUMA ZUCIYARSA NA GASKATATA, TO, KAYI MASA ALBISHIR DA ALJANNAH."

Na kasance farkon wanda na fara haduwa da shi shine Umar, sai yace:

" Wadannan takalma biyun fa na menene yaa Abu Hurairata ?" Sai nace: Wadannan takalma biyun na Manzon Allah (S.A.W.W) ne. Ya aiko ni dasu ne (a matsayin shaida) cewa duk wanda na hadu da shi yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma zuciyarsa na mai imani game da hakan nayi masa albishir da gidan Aljannah. 

Sai Umar ya doki qirjina da hannunsa, sai na fadi (qasa) kan 'Duwawuna. Sai yace (min):

" Ka koma yaa Abu Hurairata !" Sai na dawo zuwa ga Manzon Allah (S.A.W.W) na fashe da kuka (bust into tears), sai ga Umar na biye dani. Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace min:

" MENENE GARE KA YAA ABU HURAIRATA (na ganka haka firgice kana kuka)?" Nace:

" Na hadu da Umar ne na ba shi labarin abinda ka aiko ni da shi (na umarnin busharar Aljannah ga wanda na hadu da shi yana mai imani na gaskiya), shine ya doki tsakanin nonuwana wanda dukan nasa ya kayar dani (qasa) kan duwaiwaina (my bottoms) yace na koma. Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace masa:

" YAA UMAR ! MENENE YA 'DAUKE KA NA YIN ABINDA KA AIKATA ?" Yace;

" Yaa Manzon Allah ! Fansar uwata da ubana, shin kai ka aiki Abu Hurairata da takalmanka cewa duk wanda ya hadu da shi yana shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma zuciyarsa na da yaqini kan haka yayi masa albishir da gidan Aljannah ?" Yace:

" EH (ni na fada masa)." (Umar) Ya cewa (Annabi):

" Kada ka aikata haka, domin ni ina jin tsoron kada mutane su dogara da ita (wannan busharar su qi yin wani aiki), ka bar su kawai suyi aiki (ba sai anyi musu wata bushara ba)! Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" KA BAR SU (yaa Abu Hurairata kada ka yiwa wani wannan busharar)!"

(Sahihul-Muslim, Kitabul Iman, babin wanda ya mutu da imani zai shiga Aljannah, hadisi mai lamba 31).

Kunga abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, Annabi (S.A.W.W) ya yiwa Abu Hurairata umarni da cewa duk wanda ya hadu da shi mai imanin gaskiya yayi masa busharar Aljannah, amma Umar Bn Khaddab ya doki dan aiken har yana kuka a gaban Annabi (S.A.W.W) amma saboda abinda yayi daidai ne ko fada bai yi masa ba, wanda hakan ke nuna Annabi (S.A.W.W) yayi sanadin an zalunci Abu Hurairata tunda shi ya sanya shi wannan aiki.

Sannan kuma ana qara karantar damu ne cewa Umar yana iya hana abinda Allah ya umarci Manzonsa da aikatawa, domin kowa ya san ba ya magana ko aiki da son zuciyarsa. Wannan umarnin da ya yiwa Abu Hurairata kuwa umarni ne na Allah bisa sigar riwayar.

Lalle ko lakacin da Annabi (S.A.W.W) ya aika 'yan saqo da takardu zuwa ga wasu Sarakunan kafirai a farkon muslimci basu doki wadannan 'yan saqon ba, amma ga shi mai amsa sunan musulmi ya doki dan saqon Annabi (S.A.W.W) a gabansa !

(2)- Riwayar Bukhari kuma na cewa;

غزوة الفتح

وما بعث به حاطب بن أبي بلتعة إلى أهل مكة يخبرهم بغزو النبي صلى الله عليه وسلم 

(4274) - حدثنا قتيبة بن سعيد: حدثنا سفيان، عن عمرو بن دينار قال: أخبرني الحسن بن محمد: أنه سمع عبيد الله بن أبي رافع يقول: سمعت عليا رضي الله عنه يقول: بعثني رسول الله صلى الله عليه وسلم أنا والزبير والمقداد، فقال: (انطلقوا حتى تأتوا روضة خاخ، فإن بها ظعينة معها كتاب، فخذوه منها) قال: فانطلقنا تعادى بنا خيلنا حتى أتينا الروضة، فإذا نحن بالظعينة، قلنا لها: أخرجي الكتاب، قالت: ما معي كتاب، فقلنا، لتخرجن الكتاب، أو لنلقين الثياب، قال: فأخرجته من عقاصها، فأتينا رسول الله صلى الله عليه وسلم فإذا فيه: من حاطب بن أبي بلتعة، إلى ناس بمكة من المشركين، يخبرهم ببعض أمر رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال: رسول الله صلى الله عليه وسلم: (يا حاطب، ما هذا؟) قال: يا رسول الله، لا تعجل علي، إني كنت امرءا ملصقا في قريش، يقول: كنت حليفا، ولم أكن من أنفسها، وكان من معك من المهاجرين، من لهم قرابات يحمون أهليهم وأموالهم، فأحببت إذ فاتني ذلك من النسب فيهم، أن أتخذ عندهم يدا يحمون قرابتي، ولم أفعله ارتدادا عن ديني، ولا رضا بالكفر بعد الإسلام فقال: رسول الله صلى الله عليه وسلم: (أما إنه قد صدقكم) فقال عمر: يا رسول الله، دعني أضرب عنق هذا المنافق فقال: (إنه قد شهد بدرا، وما يدريك لعل الله قد اطلع على من شهد بدرا فقال: اعملوا ما شئتم فقد غفرت لكم) فأنزل الله السورة: "يا أيها الذين آمنوا لا تتخذوا عدوي وعدوكم أولياء تلقون إليهم بالمودة وقد كفروا بما جاءكم من الحق - إلى قوله - فقد ضل سواء السبيل" 

Qutaibata Bn Sa'eed ya bamu labari, Sufyan ya bamu labari daga Amruu Bn Deenar yace: Hassan Bn Muhammad ya bani labari cewa ya ji Ubaidullahi Bn Abiy Raafi'a yana cewa: Na ji Aliyu (R.A) yana cewa:

" Manzon Allah (S.A.W.W) ya aike ni, ni da Zubair da Miqdaad, yace: " KU TAFI HAR SAI KUN ISA RAUDHATUN KHAAKH, A WAJENTA AKWAI ZA'EENATU, TARE DA ITA AKWAI WATA TAKARDA, KU KARBE TA DAGA GARE TA ." Yace:

" Sai muka tafi har muka isa Raudhata, sai ga mu da Za'eenatu, muka ce mata: " Ki fito mana da wannan takarda !" Tace;

" Babu wata takarda tare dani ." Sai muka ce: " Ko dai ki fito da takardar ko kuma muyi miki tsirara." Yace: " Sai ta fito da ita daga kitsonta. Sai muka zowa Manzon Allah (S.A.W.W), sai ga shi cikinta (takardar an rubuta) : 

" Daga Haadib Bn Abiy Balta'ata zuwa ga mutanen dake Makkah daga mushirikai." Yana ba su labarin game da sashen wani al'amarin Manzon Allah (S.A.W.W) .

Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" YAA HAADIB, MENENE WANNAN ?" Yace:

" Yaa Ma'aikin Allah kada kayi gaggawa a kaina, lalle ni wani mutum ne wanda yake da aminci cikin Quraishawa." Yana cewa:

" Na kasance halifa ne, amma ban kasance daga cikinsu ba, kuma ya kasance daga cikin wadanda ke tare da kai daga Muhajiruna, akwai wanda ke da dangi wanda ke kishin iyalansu da kuma dukiyarsu. Sai naso idan hakan ya kubuce min daga nasaba cikinsu, zan sami dama a wajensu wadanda za suyi kishin makusantana, amma ba nayi hakan don yin Ridda daga addinina bane, kuma ba don yarda da kafirci bayan muslimci ba."

Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" AMMA LALLE SHI HAQIQA YAYI MUKU GASKIYA ."

Sai Umar yace:

" Yaa Ma'aikin Allah ! Ka qyale ni na fille wuyan wannan munafukin ! " Sai (Manzon Allah) yace:

" AI SHI LALLE YA HALASCI BADR, KUMA ME YA SANAR DA KAI KO ALLAH YAYI TSINKAYE NE AKAN WANDA YA HALASCI BADR ? " YACE: " KUYI ABINDA KUKA SO, HAQIQA ALLAH YA GAFARTA MUKU ?"

Sai Allah ya saukar da Surah: " YAA KU WADANDA KU KAYI IMANI ! KADA KU RIQI MAQIYINA KUMA MAQIYINKU MASOYI, KUNA JEFA SOYAYYA GARE SU ALHALI HAQIQA SUN KAFIRCE DA ABINDA AKA ZO MUKU NA DAGA GASKIYA-----" Har zuwa fadinSa---" HAQIQA SUN BACE DAGA HANYAR DAIDAI."

(Bukhari, Kitabul-Magaazeey, Babun Gazwatul-Fath, hadisi mai lamba 4274)

Taqaitaccen darasin dake cikin wannan riwaya dai shine, Annabi (S.A.W.W) ya gaskata Haadib bisa hujjar da ya kawo na dalilin tura saqonsa zuwa ga mutanen Makkah, amma kuma Umar ya qi yarda da wannan gaskatawar da Annabi (S.A.W.W) yayi masa, har ma yana cewa a ba shi dama ya fille masa wuya don munafiki ne. Wato Allah bai nunawa Manzonsa cewa munafuki bane sai Umar ne yasan haka. Har ma a qarshe aka saukar da aya wacce ke goyon bayan maganar Umar.

Idan kuwa hakane me yasa Allah bai sanar da shi wannan sirri wanda matar ta tafi da shi ba sai Annabi ne ya sani ?

Wannan ba wani abu bane face tsantsan raina Manzon Allah (S.A.W.W) da cin mutuncinsa. Allah (T) na cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَشَآقُّواْ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلۡهُدَىٰ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗا وَسَيُحۡبِطُ أَعۡمَٰلَهُمۡ ٢٣ ۞يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَلَا تُبۡطِلُوٓاْ أَعۡمَٰلَكُمۡ ٣٣ 

" LALLE WADANDA SUKA KAFIRTA (bayan sun furta imaninsu da farko) KUMA SUKA KANGE (mutane) DAGA (bin) TAFARKIN ALLAH SANNAN SUKA SABAWA MANZO BAYAN SHIRIYA TA BAYYANA GARE SU, (to, yin hakan nasu) BA ZAI CUTAR DA ALLAH DA WANI ABU BA, KUMA DA SANNU AYYUKANSU ZA SU BACI."

" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KU YIWA ALLAH 'DA'A KUMA KU YIWA MANZO 'DA'A, KUMA KADA KU BATA AYYUKANKU."

    (Suratul-Muhammad: 32-33)

Kuma kun san daga murya gaban Annabi (S.A.W.W) na bata ayyuka, INA kuma ace Annabi yayi umarni wani ya hana aiwatar da wannan umarnin ? Ko kuma ya gaskata magana sannan wani yace qarya ne ?

NA'UZU BILLAHI MIN ZALIKA !!!

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

16th November, 2021/ 11th Rabi'us-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post