Mata: 'Mu yi koyi da Sayyidah Khadaijah; kada mu zam cikin masu nunawa miji fushi ƙarara'


 IDAN RAN MACE YA BACI SAI TA NUNAWA MIJINTA QARARA !!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MATA KUYI KOYI DA SAYYIDAH KHADIJAH (S.A)

Yau ina son yin taqaitacciyar nasiha ce ga 'yan'uwa mata da ma dukkan mata musulmai masu imani da Allah da kuma sallama al'amransu ga ManzonSa (S.A.W.W).

Ba zan ce dukka ba, amma dai in ka tara mata za ka sami 80% daga cikin su ba sa yin koyi da Nana Khadijah ko Sayyidah Fatimah (S.A), domin duk dadin zaman da suke yi da mazajensu in sun sami matsala sai sun nunawa mazajen nasu qarara a aikace cewa suna jin haushinsu saboda su (matan) ba Ma'asumai bane.

Abinda dai ya tabbata cikin riwayoyi ingantattu shine, tunda Annabi (S.A.W.W) ya auri Nana Khadijah (S.A) ba a taba samun wata matsala ta gitta tsakaninsu ba har ta koma ga mahaliccinta. Kamar haka Sayyidah Fatimah (S.A) ta kasance, ita ma har ta koma ga mahaliccinta bata taba yin wani abu na sabawa ga mijinta Imam Ali (A.S) ba, domin ita Ma'asumiya ce wacce Allah (T) ya katangeta daga aikata abinda dukkan abinda ba ya so. Sai dai an qirqiro wani hadisi na qarya cikin Bukhari don a nuna cewa tana sabawa mijinta don a sanya ta cikin hadisin nan da Annabi (S.A.W.W) ke cewa duk wanda ya fusata Ali shi ya fusata.

Amma sauran mata za ayi musu uzuri saboda su ba ma'asumai bane, kuma an sami wadanda suka fi su sun nuna fushinsu ga fiyayyen halitta (S.A.W.W). 

Riwaya ce cikin Musnad na Ahmad Bn Hambal inda yake cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

23463- حَدَّثَنَا عَبَّادُ بْنُ عَبَّادٍ ، عَنْ هِشَامِ بْنِ عُرْوَةَ ، عَنْ أَبِيهِ ، عَنْ عَائِشَةَ أَنّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ لَهَا : " إِنِّي أَعْرِفُ غَضَبَكِ إِذَا غَضِبْتِ ، وَرِضَاكِ إِذَا رَضِيتِ " ، قَالَتْ : وَكَيْفَ تَعْرِفُ ذَلِكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ ؟ قَالَ : " إِذَا غَضِبْتِ قُلْتِ : يَا مُحَمَّدُ ، وَإِذَا رَضِيتِ قُلْتِ : يَا رَسُولَ اللَّهِ " .

Abbadu Bn Abbadin ya bamu labari daga Hishaam Bn Urwata, daga babansa, daga A'ishata cewa: Lalle Manzon Allah (S.A.W.W) na ce mata:

" LALLE NI INA SANIN FUSHINKI IDAN KI KAYI FUSHI, DA KUMA YARDARKI IDAN KIN YARDA." Tace:

" Ta yaya kake gane haka yaa Ma'aikin Allah? " Yace:

" IDAN KIKA FUSATA KIKAN CE : " Yaa Muhammadu !" IDAN KUMA KIKA YARDA KI KANCE : " Yaa Ma'aikin Allah !"

(Musnad Ahmad, hadisi mai lamba 23,462)

Kunga wannan ba dabi'a ce abin koyi ba, domin ko Allah (T) wanda ya halicce shi ba ya kiransa kai tsaye da sunansa don girmama shi, guri daya (1) kawai ya kira sunansa, amma ba tsayawa yayi ba sai da ya bada labari game da sunan da ya kira. Ga shi kamar haka;

مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَى ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِم مِّنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ .................

" MUHAMMADU MANZON ALLAH NE !....................."

(Suratul-Fath, aya ta 29)

Kunga anan ma ba shi ya kira kai-tsaye ba, labari yake bawa bayinsa game da matsayinsa, wanda hakan siga ce ta girmamawa.

Amma kiran suna mutum kai-tsaye rashin girmamawa ne, shi yasa mata ke yiwa mazajensu Alkunya (baban wane), hakama mazan ke girmama su da cewa (Mamar wane).

A duk randa kaji matarka ta kira sunanka kai-tsaye alhali a baya ba haka take kiranka ba, to, ka sani tana fushi da kai ko da kuwa ba laifi kayi mata ba, domin kyawun dabi'u babu kamar Manzon Allah (S.A.W.W) ballantana ace yayi abinda zai fusata wani, amma duk da hakan ana kiran sunansa kai-tsaye da nufin wai ana fushi da shi.

MATA KU JI TSORON ALLAH WAJEN AIKATA ABINDA ZAI BATA MUSU RAI.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

17th November, 2021/ 12th Rabi'us-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post