Mafita 1 da ta rage wa Buhari, hausawa sun ce, 'Ba a mugun sarki sai mugun bafade' me yasa duka biyun suka hadu kan Buharin daura?



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MAFITA GA PRESIDENT MUHAMMADU BUHARI 

Al'amarin jagorancin Muhammadu Buhari ya bawa dukkan 'yan qasa mamaki, domin babu wanda ya zace za aga abinda ke faruwa na qunci, zalunci, danne haqqi da bin ra'ayin wata qasa cikin mulkinsa, ashe ba haka abin yake ba domin al'amarin nasa ya wuce yadda kowa ke tsammani.

Anyi masa kyakkyawan zato sakamakon irin alqawuran da ya riqa yiwa al'umma, sai kuma daga baya ta bayyana cewa babu alkhairi cikin mulkinsa, wannan dalili yasa 91% na 'yan qasa ke yi masa tofin Allah tsine !

Sai dai kuma 9% daga cikin 'yan qasar na nema masa mafita da cewa shi mutumin kirki ne, sai dai bai yi sa'ar fadawa na gari bane, domin ba sa ba shi shawari mai kyau, kuma in shine ya kawo batu mai kyau ko bijiro ayyukan alkhairi ba a goya masa bawa. Wai wannan dalili yasa aka kasa samun nasara cikin mulkinsa.

To, wannan hujja ta mutane 9% zai iya samar masa da mifita ? Domin sanin amsar wannan tambaya sai ku biyo mu cikin hadisin da Ummul-Muminina A'isha ta kawo daga Manzon Allah (S.A.W.W).

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(23857)- حَدَّثَنَا حُسَيْنُ بْنُ مُحَمَّدٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا مُسْلِمٌ يَعْنِي ابْنَ خَالِدٍ ، عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ أَبِي بَكْرٍ ، قَالَ : أَخْبَرَنِي الْقَاسِمُ بْنُ مُحَمَّدٍ ، عَنْ عَائِشَةَ ، قَالَت : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " مَنْ وَلَّاهُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ ، مِنْ أَمْرِ الْمُسْلِمِينَ شَيْئًا ، فَأَرَادَ بِهِ خَيْرًا جَعَلَ لَهُ وَزِيرَ صِدْقٍ ، فَإِنْ نَسِيَ ذَكَّرَهُ ، وَإِنْ ذَكَرَ أَعَانَهُ " .

Imam Ahmad yace: Hussaini Bn Muhammad ya bamu labari yace: Muslim ya bamu labari, yana nufin Ibn Khaalid, daga Abdurrahman Bn Abiy Bakrin yace: Qasim Bn Muhammad ya bamu labari daga A'ishata, tace: Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" DUK WANDA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA JIBINTAR MASA WANI ABU DAGA AL'AMRAN MUSULMAI, KUMA YA NUFE SHI DA ALKHAIRI, SAI YA SANYA MASA WAZIRAI NA GASKIYA. IDAN YA MANTA SAI SU TUNA MASA, IDAN KUMA YA TUNA SAI SU TAIMAKA MASA."

(Musnad Ahmad, hadisi mai lamba 23,857)

                 NAZARI

               ___________

Idan wannan hadisi ya inganta sai muce, ashe ba wani abu ne ya hana cigaba da samun Fadawa na kirki cikin Gwamnatin Buhari ba sai dai don babu alkhairi tare da shi. Da ace akwai alkhairi tare da shi da ya taimake shi wajen samar masa Fadawa na kirki.

Sai dai kuma shi din ba na kirkin bane shi yasa Allah bai hada shi da mataimaka na kirki ba. Saboda haka za muce Hausawa sun fadi qasa warwas da yin wannan hausar tasu, domin ana mugun Bafade ne sakamakon mugun Sarki.

Wannan kuwa ya qara gaskata mana hadisin nan wanda Manzon Allah (S.A.W.W) ke cewa duk wanda ya nemi mulki ba tare da ba shi akayi ba, to, za a barshi ne da kansa. Amma idan ba shi akayi ba tare da ya nema ba sai Allah ya taimake shi.

BA A MUGUN BAFADE SAI DA MUGUN SARKI !

Daga wakilanmu na Bauchi zone

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

17th November, 2021/ 12th Rabi'us-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post