WANNE LAIFI SHEIKH ABDUL-JABBAR YAYI KUKE NEMAN SHEQAR DA JININSA ???
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
INA KAFA MUKU HUJJA DA IRIN HUJJAR DA USMAN BN AFFAN YA KAFAWA MAKASANSA
Ba ya tabba zama abin mamaki don kaga ko ka ji wasu na da'awar kisa ga wani bawan Allah mumini a wannan zamani, domin kuwa an sami irin wadannan ra'ayoyi cikin magabata wadanda ake cewa dukkansu Taurari ne.
Sayyid Zakzaky (H) da mabiyansa sune na garko a wannan qarni wadanda aka sami da'awowi daban-dabam masu halasta jinanansu ba bisa haqqi ba.
Ganin rashin nasara tasa aka juyo kan Sheikh Abdul-Jabbar wanda yake da'awa don tsarkake manyan littafan da ake riqo dasu a muslimci ana aiki dasu, alhali suna cike da datti wanda yarda da wannan dattin zai sa mutane su rasa imaninsu, a qarshe su tafi wuta ba tare da sun san ita ce makomarsu ba.
HUJJAR DA USMAN BN AFFAN YA KAFA
Duk da cewa ayyukan Usman Bn Affan ne suka jawo masa wannan kisa sakamakon rashin adalci cikin mulkinsa, amma kasantuwar kisa ba shine hukuncinsa ba sai ya kafa musu da abinda Annabi (S.A.W.W) ya fada don nuna matsayin jinin mutum musulmi.
Ku biyo mu cikin Sunan-Tirmidhi kamar yadda ya kawo.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
باب ما جاء لا يحل دم امرئ مسلم إلا بإحدى ثلاث:
«2311» حدثنا أحمد بن عبدة الضبي حدثنا حماد بن زيد عن يحيى بن سعيد عن أبي أمامة بن سهل بن حنيف أن عثمان بن عفان أشرف يوم الدار فقال أنشدكم الله أتعلمون أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: ((لا يحل دم امرئ مسلم إلا بإحدى ثلاث زنا بعد إحصان أو ارتداد بعد إسلام أو قتل نفس بغير حق فقتل به)). فوالله ما زنيت في جاهلية ولا في إسلام ولا ارتددت منذ بايعت رسول الله صلى الله عليه وسلم ولا قتلت النفس التي حرم الله فبم تقتلونني قال أبو عيسى: وفي الباب عن ابن مسعود وعائشة وابن عباس. وهذا حديث حسن. ورواه حماد بن سلمة عن يحيى بن سعيد فرفعه. وروى يحيى بن سعيد القطان وغير واحد عن يحيى بن سعيد هذا الحديث فأوقفوه ولم يرفعوه وقد روي هذا الحديث من غير وجه عن عثمان عن النبي صلى الله عليه وسلم مرفوعا.
Tirmidhi yace: Ahmad Bn Abdatul-Dhabbiy, Hammad Bn Zaid ya bamu labari daga Yahya Bn Sa'eed, daga baban Umamata Bn Sahl Bn Haneef, cewa wata rana (wasu jama'a) sun daukaka akan Usmana Bn Affan cikin gidansa (da nufin kashe shi), sai yace:
" Ina hada ku da Allah ! Shin, kun san cewa Manzon Allah (S.A.W.W) yace:
" JININ MUTUM MUSULMI BA YA HALATTA SAI BISA 'DAYAN ABUBUWA UKU.
- YIN ZINA BAYAN SAMOWA MUHSINI (katangagge),
- KO KUMA RIDDAH BAYAN MUSLIMCI,
L
- KO KUMA KASHE RAI BA TARE DA KASHE (wata) RAI BA TARE DA WANI HAQQIN BA, SAI A KASHE SHI DASHI ."
Na rantse da Allah ban taba yin zina a jahiliyya ba ko cikin muslimci, kuma banyi riddah ba tun daga lokacin dana yiwa Manzon Allah (S.A.W.W) mubaya'ah, kuma ban kashe rai wacce Allah ya haramta ba. To, da wacce hujja ce za ku kashe ni ?"
(SUNAN TIRMIDHI, KITABUL-FITANI, BABIN BA YAZO CIKIN JININ MUTUM MUSULMI BA YA HALATTA SAI BISA 'DAYAN ABUBUWA UKU, HADISI MAI LAMBA 2311)
Saboda ni ma mai wannan rubutu ina tuhumarku akan Sheikh Abdul-Jabbar da irin tuhumar da Usman ya tuhumi makasansa.
A ina kuka taba samunsa da aikata zina tun bayan aurensa?
Wacce rai ya taba kashewa cikin rayuwarsa tun lokacin da ya zama mukallafi ko da kuwa kafin zamansa mukallafin ne ?
Menene ya aikata wanda ya warware masa kalmar shahadarsa wacce yayi ta ta maida shi musulmi duk da cewa cikin muslimcin aka haife shi tare da kyakkyawar aqida ?
Kuji tsoron Allah ku dawo daga kan wannan mummuniyar aqidar taku tun kafin lokaci ya qure muku.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
18th October, 2021- 13th Rabi'u-Awwal, 1443.