Bidi'ah ce abin yaka ko kuma wanda ya soke Sunnar Annabi (S.A.W.W) ?


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

UMARNIN UBANA ZAN BI KO UMARNIN MANZON ALLAH (S.A.W.W) IN JI IBN UMAR

Cikin umarnin da Annabi (S.A.W.W) yayi mana akwai bin sunmarsa da kuma bin sunnar Halifofinsa shiryayyu masu shiryarwa, sannan kuma ya hane mu game da aikata mummuniyar bid'ah wacce ba a samun lada cikinta sai dai zunubi.

Duk da wannan umarni da hani nasa (S.A.W.W) an sami masu qoqarin hana bin sunnar tasa da kuma masu qoqarin aikata bid'ar, alhali kamaya yayi ace ka aikata sunnar ne ba wai ka soketa ko kuma ka hana mutane aikata ba saboda qarfin mulki ko kuma wata dama da ka samu.

Sai kuma ga shi an sami wasu gungun mutane da suke kiran kansu da sunan masu kawar da bid'ah da kuma tabbatar da sunnah.

Sai dai kuma qoqarin nasu ya zama sunnar ma suke kawarwa maimakon kawar da bid'ar. Wannan kuwa ya samo asali tun daga kan sarki Umar Bn Khaddab, domin shi ya qirqiro bid'ar jam'in tarawihi da kuma soke yin Tamattu'i na Hajji wanda Annabi (S.A.W.W) ya aikata, kuma bai hana ba har yayi wafati.

Bari dai mu kawo misalin don kada wani yayi zaton surutu muke yi marar tushe.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

19396- حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ جَعْفَرٍ ، حَدَّثَنَا سَعِيدٌ ، عَنْ قَتَادَةَ ، عَنْ مُطَرِّفِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ ، قَالَ : بَعَثَ إِلَيَّ عِمْرَانُ بْنُ حُصَيْنٍ فِي مَرَضِهِ ، فَأَتَيْتُهُ ، فَقَالَ لِي : إِنِّي كُنْتُ أُحَدِّثُكَ بِأَحَادِيثَ لَعَلَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَتَعَالَى يَنْفَعُكَ بِهَا بَعْدِي ، وَاعْلَمْ أَنَّهُ كَانَ يُسَلِّمُ عَلَيَّ ، فَإِنْ عِشْتُ فَاكْتُمْ عَلَيَّ ، وَإِنْ مِتُّ فَحَدِّثْ إِنْ شِئْتَ , وَاعْلَمْ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " قَدْ جَمَعَ بَيْنَ حَجَّةٍ وَعُمْرَةٍ ، ثُمَّ لَمْ يَنْزِلْ فِيهَا كِتَابٌ ، وَلَمْ يَنْهَ عَنْهَا النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ " ، قَالَ رَجُلٌ فِيهَا بِرَأْيِهِ مَا شَاءَ , حَدَّثَنَا عَبْدُ الرَّزَّاقِ ، أَخْبَرَنَا مَعْمَرٌ ، عَنْ قَتَادَةَ ، عَنْ مُطَرِّفٍ ، قَالَ : قَالَ لِي عِمْرَانُ بْنُ حُصَيْنٍ فَذَكَرَ مِثْلَهُ ، وَقَالَ : لَا تُحَدِّثْ بِهِمَا حَتَّى أَمُوتَ .

Imam Ahmad Bn Hambal yace: Muhammad Bn Ja'afar ya bamu labari, Sa'eed ya bamu labari daga Qatadata, daga Mudarrifi Bn Abdullahi yace: Imrana Bn Hussain ya aiko zuwa gare ni a halin rashin lafiyarsa, sai naje masa , sai yace min:

" LALLE NI ZAN BAKA LABARI DA WANI LABARI, WATAQILA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA AMFANAR DAKAI ITA A BAYANA. KA SANI, LALLE SHI YA KASANCE YANA YIN SALLAMA GARE NI, IDAN NA RAYU (daga wannan jinyar tawa) KA BOYE (wannan magana wacce zan fada maka), IDAN KUMA NA RASU, TO, KA BADA LABARI IN KA SO.

KA SANI LALLE MANZON ALLAH (S.A.W.W) YA HADA AIKIN HAJJI DA UMRA (Tamattu'i), SA'AN NAN KUMA LITTAFI BAI SAUKO A KANTA (don hani ba), KUMA ANNABI BAI YI HANI GAME DA ITA BA , WANI MUTUM NE KAWAI YAYI HANI GAME DA ITA BISA RA'AYINSA (na ganin ya fi Annabi)."

Abdurrazaq ya bamu labari, Ma'amar ya bamu labari daga Qatadata, daga Mudarrifi yace: Imrana Bn Hussain ne ya fada min. Sai ya ambaci misalin (riwaya ta sama) yace: " KADA KA BADA LABARI DA WANNAN (magana) HAR SAI NA MUTU (don ina jin tsoron kada Sarki ya azabtar dani) ."

(Musnad Ahmad, hadisi mai lamba 19,396)

Kaga wannan shine haqiqanin abinda aka sani daga Annabi (S.A.W.W) cewa ana hada aikin Hajji da Umra, amma sai wani ya hana a zamanin mulkinsa. Shi wannan mutumi kuwa shine Umar Bn Khadda.

Ku biyo mu don tabbatar da wannan magana cikin hadisin dake biye.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

«832» حدثنا عبد بن حميد أخبرني يعقوب بن إبراهيم بن سعد حدثنا أبي عن صالح بن كيسان عن ابن شهاب أن سالم بن عبد الله حدثه أنه سمع رجلا من أهل الشام وهو يسأل عبد الله بن عمر عن التمتع بالعمرة إلى الحج فقال عبد الله بن عمر هي حلال. فقال الشامي إن أباك قد نهى عنها. فقال عبد الله بن عمر أرأيت إن كان أبي نهى عنها وصنعها رسول الله صلى الله عليه وسلم أأمر أبي نتبع أم أمر رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال الرجل بل أمر رسول الله صلى الله عليه وسلم.

فقال لقد صنعها رسول الله صلى الله عليه وسلم." قال: هذا حديث حسن صحيح.

Abdu Bn Humaid ya bamu labari, Ya'aqub Bn Ibrahim Bn Sa'ad ya bani labari, banana ya bani labari daga Salih Bn Kaisaan, daga Ibn Shihaab cewa Saalim Bn Abdullahi ya ba shi labari cewa ya ji wani mutum daga mutanen Sham yana tambayar Abdullahi Bn Umar game da Tamattu'i da Umra zuwa Hajji, sai Abdullahi Bn Umar yace:

" AI ITA HALAL CE !"

Sai wannan mutumin Sham din yace: " Ai kuwa babanka yayi hani game da ita ."

Sai Abdullahi Bn Umar Yace:

" YANZU KANA GANIN DON BABANA YAYI HANI GAME DA ITA KUMA MANZON ALLAH (S.A.W.W) YA AIKATA, UMARNIN BABANA ZAN BI KO KUMA UMARNIN MANZON ALLAH (S.A.W.W) ZAN BA ?"

Sai mutumin yace: " A'a, umarnin Manzon Allah (S.A.W.W) ."

Sai (Ibn Umar) yace: " HAQIQA MANZON ALLAH (S.A.W.W) YA AIKATA."

Tirmidhi yace, wannan hadisi kyakkyawa ne kuma ingantacce.

(Sunan Tirmidhi, hadisi mai lamba 832).

To, yanzu dan Allah in dai gaskiya ake so kuma ake yi, wa ya kamata a yaqa don cigaban muslimci, mai hana aikata sunnar Annabi (S.A.W.W) ko kuma mai aikata bid'ah ? 

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

8th November, 2021/ 4th Rabi'u-Awwal, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post