Waki'ar Gyallesu ta yi kama da yakin Ahzaab !


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KAMANCECENIYAR MABIYAN SAYYID ZAKZAKY (H) DA SAHABBAN ANNABI (S.A.W.W)

A kullum tarihi ne kW maimaita kansa, duk wani abinda ya faru a zamanin Annabi (S.A.W.W) mai kyau ne ko mummuna, nasara ce ko rashinta, za ka ganta ta bayyana qarara cikin al'ummar Manzon Allah (S.A.W.W).

Cin dunduniya ne ko kuma yin zagon qasa, munafurci ne ko kuma gaskiyar mabiya da dakewarsu ? Duk suna nan kuma sun bayyana a wannan zamani.

Siffar abinda ya faru a yaqin Ahzaab shine abinda ya maimaita kansa daga ranar 12-14 ga watan December na shekarar 2015 a garin Zaria cikin unguwar Gyallesu.

Ba mutanen Madinah ne suka kai hari ba kuma ba tsokana suka yi ba, amma sai aka sami taron dangi na gangamin jagororin kafiran Makkah da suka hada kai da Yahudawan Madinah da kuma munafukan cikin Sahabban Annabi (S.A.W.W) su kayi gangami don murqushe da'awar Manzon Allah (S.A.W.W) da mabiyansa tsarkaka.
Ita wannan kamanceceniyar za mu same ta ne cikin Suratul-Ahzaab yadda ta bayyana mana komai dalla-dalla yadda Allah (T) ke cewa:

 سُورَةُ الأَحۡزَابِ

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

" يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ جَآءَتۡكُمۡ جُنُودٞ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا وَجُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرًا (٩)

" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! KU TUNA NI'IMAR ALLAH (wacce yayi) A KANKU YAYIN DA RUNDUNA (ta maqiya) TAZO MUKU (da nufin halakar daku) SAI MUKA AIKA ISKA A KANSU DA WATA RUNDUNA (ta Mala'iku) WADANDA BA KWA GANINSU (a matsayin gudumawarmu gare ku), KUMA ALLAH YA KASANCE MAI GANI GAME DA ABINDA KUKE AIKATAWA.

" إِذۡ جَآءُوكُم مِّن فَوۡقِكُمۡ وَمِنۡ أَسۡفَلَ مِنكُمۡ وَإِذۡ زَاغَتِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَبَلَغَتِ ٱلۡقُلُوبُ ٱلۡحَنَاجِرَ وَتَظُنُّونَ بِٱللَّهِ ٱلظُّنُونَا۠ (٠١)

YAYIN DA SUKA ZO MUKU TA SAMANKU DA KUMA TA QASANKU, KUMA YAYIN DA IDANUWA SUKA KARKATA KUMA ZUKATA SUKA KAI MAQOSA (saboda tsananin firgici da tsoro), KUMA KU KAYI TA ZACE-ZACE GA ALLAH (kun amsa kiranSa kuma yabar maqiya za su kashe ku).

" هُنَالِكَ ٱبۡتُلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَزُلۡزِلُواْ زِلۡزَالٗا شَدِيدٗا "(١١ )

ACAN NE MUKA JARRABI MUMINAI KUMA MUKA GIRGIZA SU GIRGIZAWA !

" وَإِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ مَّا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ إِلَّا غُرُورٗا " (٢١)

KUMA A LOKACIN DA MUNAFUKAI DA WADANDA AKWAI CUTA (ta munafurci) CIKIN ZUKATANSU KE KEWA: " BABU ABINDA ALLAH DA MANZONSA SU KAYI MANA ALQAWARI FACE RUDI (deceive) .

Anan za muga cewa tabbas Allah yayi jarrabawa ga muminai ta hanyar turo musu maqiya abokan gaba masu yawa da tsananin qarfi fiye da qarfin da su suke da shi. Har takai munafukai suna zargin Allah da Manzonsa (S.A.W.W) kan cewa sun kai su gurin da za a halakar dasu ne kawai domin babu abinda zasu iya yi musu na taimako.
Sai Allah ya gargade su da cewa;

" لَّقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِي رَسُولِ ٱللَّهِ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَذَكَرَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا ." (١٢)

" HAQIQA ABIN KOYI MAI KYAU YA KASANCE GARE KU DAGA (rayuwar) MANZON ALLAH GA WANDA YAKE FATAN SAMUN YARDAR ALLAH DA KUMA (sakamako mai kyau) LAHIRA, KUMA YA AMBACI ALLAH DA YAWA !"

Ma'ana ku duba wanne irin hali Annabi (S.A.W.W) ke ciki ? Firgita yayi ko kuma guduwa yayi ya barku ? Idan ya firgita kuma ya gudu sai ku ma ku gudu kamar yadda yayi. Amma in yana cikin nutsuwarsa da dakewa, to, haka ya kamata ku kasance masu yin koyi da shi.

A gaba kuma sai ya bayyana halayyar muminan cikinsu da irin sallamawarsu da dakewarsu tare da gaskata Allah da Manzonsa (S.A.W.W) kan cewa dama sunyi musu bayanin zuwan wannan rana don tantancewa tsakanin muminan cikinsu da munafukansu.

وَلَمَّا رَءَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلۡأَحۡزَابَ قَالُواْ هَٰذَا مَا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَصَدَقَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥۚ وَمَا زَادَهُمۡ إِلَّآ إِيمَٰنٗا وَتَسۡلِيمٗا (٢٢)

" KUMA YAYIN DA (su) MUMINAI SU KAGA WANNAN RUNDUNA (ta maqiya Allah dauke da muggan makamai) SAI SUKA CE: " AI WANNAN SHINE DAMA ABINDA ALLAH DA MANZONSA SU KAYI MANA ALQARI (na zuwansa), KUMA SUKA GASKATA ALLAH DA MANZONSA (kan wannan alqawari nasu). KUMA (zuwan wadannan rundunar maqiya) BATA QARA MUSU (wani abu na tsoro ko rauni ba) SAI DAI KAWAI IMANI DA SALLAMAWA."

(Suratul-Ahzaab, aya ta 9-12, 21-22)

ABINDA YA AUKU A ZARIA, GYALLESU
___________________________
Babu wani bambanci, domin su ma mabiya Sayyid Zakzaky basu bar muhallinsu zuwa wani guri da nufin cutar da wani ko kai masa hari ba, sai dai kawai binsu akayi zuwa nasu muhallin kamar yadda aka bi Manzon Allah (S.A.W.W) zuwa garin da yake da zama (Madinah).

Idan ka kwatanta yanayin zamanin baya na makaman da suke da shi kuma ka auna shi dana wannan zamani za ka iya cewa rundunar da tazo Gyallesu ta fi ta Ahzaab. Sannan kuma su ma ta kowacce fuska suka shigo Gyallesu kamar dai yadda Allah ya ambata mana siffar na Ahzaab.

HALIN MABIYA SAYYID ZAKZAKY (H)
_______________________________________
Tun kafin zuwan wannan rana Sayyid Zakzaky (H) ya sha ambata a gurare da dama cewa lalle cikin wannan tafiya akwai jarrabawa mai tsanani (kisa), har ma ya riqa cewa duk wanda bai shirya ba ya ja da baya, kamar yadda yadda Imam Hussain (A.S) ya fadawa Sahabbansa yayin da suka nufi Kufah.

An riqa fatan ganin zuwan wannan rana kafin zuwan nata, sai dai zuwan natan ya zo da jarrabawa wacce ta tantance imanin mabiya yadda ta bayyanar da munafukai da masu rauni da kuma masu tsantsar imani !
A daidai lokacin da wannan runduna ta shigo Gyallesu kuma aka fahinci haqiqanin manufarsu sai ya zama wasu daga cikin wadanda ke gurin suka riqa neman mafaka tare da zargin jagora da kuma yin da-na-sani na zuwa wannan waje.

Su kuwa muminan cikinsu sai suka tuna abinda jagora ya riga ya ambata musu tun kafin wannan rana, saboda haka maimakon rauni (weak) sai ya zamana imani ne ya qaru musu da kuma sallamawa !

Suka dubi wanne hali jagora ke ciki, guduwa yayi ko dakewa ? Da suka ga yana nan daram ko firgita baiyi ba ballantana ya gudu, sai su ma suka ce dole muyi koyi da kai domin kaine madadin Annabi (S.A.W.W) a wannan lokaci wanda za muyi dubi da kai ka zama abin koyi.

Daga nan aka cigaba da bada kariya ga jagora kamar yadda muminai suka bada kariya ga Manzon Allah (S.A.W.W). A qarshen al'amari sai zuwa yanzu kowa ya san Allah ya kawo taimakonsa yadda ya kunyata tare da qasqantar da wadannan runduna ta muggan azzalumai, domin sun buga kuma sun bar wadannan mabiya cikin izzah ! Su kuma suka dau qasqanci da kunyata a idon duniya, domin sun kasa yin abinda suka yi nufi na shafe Shi'ah da mabiyanta a wannan qasa Nigeria.

MADALLA DA WANNAN JAGORA ABIN KOYI

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

13th October, 2021/ 8th Rabi'u Awwal, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post