@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BAMBANCIN DAKE TSAKANIN AQIDAR SHI'AH DA SUNNAH
Sakamakon wannan sabani da aka samu cikin aqida yasa masu da'awar Sunnah ke ganin 'yan Shi'ah ba akan daidai suke ba don an sami sabani tsakaninsu cikin rukunan muslimci.
Cikin aqidar Shi'ah sun tafi kan cewa akai USULUD-DEEN kuma akwai FURU'UD-DEEN. Usul shine aqida wacce ya zama wajibi mutum ya san su kuma yayi imani dasu a qashin kansa ba tare da dogaro (TAQLIDI) da wata fahintar wani ba. Wannan kuwa shi ke mayar da mutum ya zama cikakken musulmi.
USULUL-DEEN
______________________
Abubuwa biyar ne da suka zama wajibi akan mutum matuqar shi musulmi ne, ga su kamar haka:
(1)- TAUHEED:- Shine mutum ya qudurci cewa Allah samamme ne kuma shi kadai yake ba shi da abokin tarayya. Da ace Allah na da abokin tarayya to, haqiqa da kuwa zai zama kowa mai cin gashin kansa ne ba tare da buqatar wani ba, sai ya zama samuwar na biyun ba shi da fa'ida.
Duk abinda ya zama yana da kishiya bai cancanci ya zama Allah ba. Wannan kuwa shine asalin tauhidi.
(2)- ADAALA:- Wannan shine yin imani kan adalcin Allah da kuma kore maza zalunci. Domin akwai wadanda suka yarda cewa Allah daya (1) ne, amma kuma suna zarginsa wajen fifita wasu kan wasu ta fuskacin arziqi ko ilimi ko kuma wani haqqi na wasu kamar wajen rabon gado. Ko kuma ta wajen ganin matsayinsu na mulki ko sarauta wacce ke sa su su aikata abinda su kaga dama bisa tunanin babu hukunci . Shi kuwa Allah mai taimakon wanda aka zalunta ne, kuma ba ya tauye haqqin wani komai qasqancinsa a idon mutane. Wannan na nuna mana ne cewa akwai bambanci tsakanin Tauhidi da Adalci.
(3)- NUBUWWA:- Annabtaka shine yin imani da cewa babu makawa ga Allah ya aiko Annabawa da Manzanni (A.S) domin su sanar da mutane umarni da hanin Allah, domin cikin tsarin Allah bai hukunta cewa Shi da kansa zai jagoranci isar da saqonSa ga bayinSa.
Na farkonsu shine Adam (A.S), na qarshensu kuma mafificinsu shine Muhammad (S.A.W.W).
To, shi kuma Annabi ko Manzo shine mai sanar da mutane abinda zasu aikata ko su nisanta, saboda haka sallah da Hajji wasu ayyuka ne dake qarqashin aikin da aka aiko Annabi ko Manzo dasu zuwa ga al'umma, don haka suka zama ayyuka ne dake qarqashin Annabta ba wai abubuwa masu cin gashin kansu ba ballantana a kira su wani rukuni cikin aqida.
(4)- IMAMA:- Allah bai yi nufin samar da Annabawa da Manzanni (A.S) har zuwa tashin alqiyama ba, saboda haka ya umarci Manzanni (A.S) da nasabta masu gadonsu wajen isar da saqon Allah kamar yadda suka koyar. Saboda hakane ma Annabi (S.A.W.W) bai bar duniya ba har sai da yace mana ya bar mana nauyayan abubuwa biyu wadanda za muyi riqo dasu a bayansa. Har ma ya qara da cewa ya hore mu da bin sunnarsa da Sunnar Khalifofinsa shiryayyu.
Kenan dole muyi imani da cewa Imamanci na daga cikin aqida wacce ke maida mutum cikakken musulmi.
(5)- MA'AD:- Ma'ad shine makoma wacce kowanne mai rai zai koma cikinta domin sake sabuwar rayuwa a gangar jiki bayan qarewarta. Allah zai tayar da kowacce rai daga qabarinta domin yayi mata hisabi kan dukkan abinda ta aikata.
Dalili kuwa shine, akwai masu ganin babu wata rayuwa bayan mutuwa, kuma babu wanda ya isa ya rayar da gangar jiki bayan ta rududduge.
Shine Allah (T) yace ai wanda ya samar da ita tun babu ita shi zai rayar da ita domin hisabi. Kuma yace mana kamar yadda aka fare mu muke komawa.
Saboda haka dole wannan ya zama aqida mai cin gashin kanta tunda akwai masu inkarin hakan.
RUKUNAN MUSLIMCI ___________________________
Cikin Sunnah kuma sun kira nasu ne da rukunan muslimci wadanda suka ce sune ke mayar da mutum ya zama musulmi. Wadannan rukunan kuwa sune:-
(1)- TAUHIDI:- Sun fasara tauhidi da cewa shine shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S.A.W.W) ManzonSa ne.
Wannan kuwa abubuwa ne guda biyu wanda kowanne ke cin gashin kansa, amma sai suka tsuke shi cikin abu guda wanda bai bada wata ma'ana ba.
(2)- SALLAH:- Sallah wani yanki ne daga cikin ayyukan da aka aiko Annabawa da Manzanni (A.S) dashi, domin tana daga cikin umarnin da Allah ya yiwa ManzanninSa kan cewa su isar da shi zuwa ga bayinSa. Saboda haka ma ai ya zama dole ka aikata ta matuqar dai ka yi imanin da Annabtaka.
(3)- AZUMI:-
(4)- ZAKKAH:-
(5)- HAJJI:-
Azumi, Zakkah da Hajji kamar sallah suke a matsayin ayyukan ibada wadanda Annabawa da Manzanni (A.S) ke zuwa dasu, shi yasa ba za muce komai a kansu ba tunda mun bada misali da sallah. Matuqar ka yarda da Manzon Allah (S.A.W.W), to, dole ka aikata su matuqar kana da iko.
ABIN LURA
________________
Hatta a Sunnar ma sun cire Zakkah da aikin Hajji kamar yadda suke cewa su ayyuka ne wadanda suka kebanta kawai ga masu iko, saboda haka Tauhidi da Sallah da Azumi sune mafiya qarfi.
Idan kuwa hakane, to, ai kuwa bai ma kamata a lissafo su cikin rukunan muslimci wanda ake cewa su ke maida mutum ya zama musulmi ba.
Uhmm, sun manta da cewa hatta ita sallar da azumin ma zusu iya faduwa kan mutum ba bisa lalura ?
Yanzu da ace mutum zai fada cikin wata jinya yadda ko cikin zuciyarsa ma ba zai iya bijiro siffarta ba ballantana ace za a iya yi masa alwala ya sallaci sallar a haka Allah ba zai kama shi kan laifin rashin yin nata ba ?
Kuma hakama azumin yake, da ace mutum zai mutu da bashin azumi a kansa kuma ya rasa masu biya masa daga cikin 'ya'yansa Allah ba zai kama shi da laifin rashin yin azumin ba matuqar da ba bisa ganganci ya kasa yi ba.
Amma ya kuka ga babun imani da Allah ko Manzo, da ace mutum zai mutu ba tare da yin imani dasu ba wuta za a kai shi !
ASHE DAI SALLAH, AZUMI, ZAKKAH DA HAJJI BASU CIKIÑ USUL.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
8th October, 2021/ 3rd Rabi'u Awwal, 1443.