Rahotannin marubuta; kaso 20 cikin 100 ne ke karanta Rubutun Marubuta a Soshiyal Midiya..!!!


 Wani rahotan binkice ya nuna cikin kaso ɗari ashirin ne kawai suke karanta labarai marubuta, saka makon yawaita masu sha'awar shiga aikin ''Midiya'', yanzu kusan kowa yana zama ɗan midiya ne saka makon idan mutum yaga yana da babbar waya a hannun sa sai ya yi sha'awar kama aikin midiya, hakan shi ne ya kawo yawan jama'a masu aiki da kafar sada zumunta facebook, whtsapp, telagrem. Mutane sun yawaita masu sha'awar wannan aikin hakan shine ya kawo karancin makaranta labarai acikin al'uma.

Rahotan ya nuna cewa idan da za' asamu yawan masu karanta labarai, su kuma marubutan cikin kaso 100/ su koma 40, kaga ansamu masu karanta labarai mutum (60), kenan to kaga hakan zai ƙarawa su marubuta ƙara sakin ƙaimi wajan sakar mu wasu abubuwa dake cikin duniya.

Amma yanzu kusan kowa ya zama ɗan midiya indai da waya a hannunsa to shi kawai ya zama mai bada labarai.

Shin mai sha'awar shiga wannan aikin kasan haɗarinsa, kasan ilimin da ke cikinsa kuwa, kasan sirin dake cikin wannan aikin da kake san shigarshi. To lallai sai ka kasance mai yawaita karatun wannan kafa sannan zaka san, abinda ake ciki aikin media yana buƙatar kuɗi da kayan aiki yana buƙatar sadau kar da aijuhunka dan mallakar kayan aiki, ka fin kashiga cikin wannan babban aiki da kake san kaga kashiga.

Afarko dole sai kasamu ilimi akansa sannan kuma sai kaji karfin yin sa, to yanzu kusan masu sha'awar shiga wannan aikin basu da ilimin abun kawai suna yin sa kara zube ne kawai basusan mai aiki nufi da da ''online Journalism'' ba.

Cikin rahotan marubutan mu da muke da su masu sha'awar wannan aikin, yawan cinsu basa riƙe sirin dake cikin aikin jarida, lallai aikin media baya buƙatar bai yana wani abu wanda shi yana buƙatar sirine. Ba ko wanne labari ne ake bai yana shiba.

Amma yanzu 'yan midiya da muke da su basa iya riƙe sirin dake tsakanin su wanda hakan yasaɓawa aikin jarida, da suke ƙoƙarin yinsa..

Kira ga waɗannan masu sha'awar shiga wannan aikin muna da buƙatar su kasance masu ilimi akan wannan aikin da suka sawa kansu, da bibiyar ''littatafai'' daban-daban dan samun ilimin mai ingancin atattare da su, da mallakar littafin ƙa'idojin Rubutun Hausa hakan zai tai maka muku sosai.

Allah ya yi mana Jagoranci Allah yasa muyi aiki da waɗannan abubuwa da muka anbata.

Faruq Sani Kudan (Abban Jidda)

14/10/2021-6-1443h

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post