HARIN YAN BINDIGA: ANA CI GABA DA KISA,SATAR MUTANE DA TARWATSA GARURUWA A YANKIN SHINKAFI
________________________________
A yankin Shinkafi dai lamurran tsaro sai kara tabarbarewa suke, kullum Yan bindiga sai matsa kaimi suke wajen kisan mutane,sace mutane da kuma tarwatsa garuruwa.
A Shinkafi a kullum babu bacci al'umma na kwana a bakin jeji domin kariyar kai daga hare-haren ta'addancin Yan bindiga da ya zama ruwan dare gama gari.
Tafiye-Tafiye a Shinkafi sun tsaya Chak! Wanda babu amincin ko da tafiyar kilomita daya daga wajen garin Shinkafi,Yan bindiga a kowane lokaci ka iya rufe hanya su kashe na kashi su sace na sata! Abubuwan sai dai a ce Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!
Gwamnatin Jihar Zamfara ta kasa bayar da tsaro koda akan hanya ce,a kullum wani sanannen mashigar Yan bindiga wurin da akafi sani da suna "KWANAR JALAF" tun ranar 15th September,2021(Ranar da aka kashe wani fitaccen dan Kasuwa Mai sana'ar Shinkafa Malam Sanusi Bala) zuwa yau da nake wannan rubutun kullum sai an kashe rayukka kuma an sace mutane!
A jiya Lahadi ma a wannan wurin da ake kira da 'Kwanar jalaf' an kashe akalla mutane 4 an harbi 5, an sace mutanen da zuwa yanzu da muke wannan rubutun bamu kammala hada alkalumman ba,kama daga Maza,yara da ma mata!
Kwamitin tsaron Shinkafi sunyi iya kokarinsu nayin tattaki zuwa Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara duk da rashin kyawon hanyar domin ganin duk wadanda lamurran tsaro suka rataya akansu domin neman jami'an tsoron da zasu tsare wannan hanya musamman wannan wurin da kisan mutane ya zama ruwan dare.
Kwamitin tsaron Shinkafi basuyi kasa a guiwa ba wajen neman wannan bukata domin kare mutuncin al'ummar Shinkafi da ma matafiyan da ke karakaina akan hanyar,amma zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton babu wani abunda Gwamnatin Jihar Zamfara hadi da Kwamishinan Yan sandan Jihar Zamfara sukayi akai! A kullum kawai suna cewa ne an shirya jami'an tsoron da zasu zauna akan hanyar zama na dindindin,amma dai abun har yanzu babu ko jami'in tsaro daya a wannan kwanar jalaf din da ta kasance 'Lahirar matafiya'
A bangaren mazauna karkara kuwa wadanda mulkin Yan bindiga bai Kai ga mamayewa ba kuwa al'umma sai gudun hijara sukeyi zuwa garin Shinkafi wanda shima garin na Shinkafi baya da tabbas!
A ranar Assabar din nan ma sun aukawa Kauyukkan KAYAYE ta 3 da ta 4 da rana tsaka inda suka kashe mutane 3 suka raunata wasu.Su wadannan Kauyukkan tazararsu da Shinkafi bai wuce kilomita daya ba(1 kilometer),bayan kashe mutane sun shiga gida-gida suna kwashe ragowar dabbobin da ke hannun mazauna kauyen.
Zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton al'ummar Kauyukkan sunyo gudun hijara zuwa garin Shinkafi domin tsoron abinda ka iya biyo baya! Al'ummar Kauyukkan dai sun koka da irin yanda basa samun taimakon jami'an tsoro idan Mahara sun auka masu duk da dimbin jami'an tsoron da ake yita jibgewa a garin na Shinkafi.
A dai dai wannan lokacin da muke hada wannan rahoton wasu mazauna Kauyukkan KAYAYE din sunyi Yunkurin komawa Kauyukkan Wanda a baya haka sukeyi,su yini a Kauyukkan su kwana a Shinkafi! Amma a yau abun ya faskara saboda a dai dai lokacin da suke Yunkurin komawa anyita jin karar harbe-harbe a iyakokin garin Shinkafi wanda ake sa ran Maharan ne da Sojoji suke musayar harbe-harbe.
Muna kira da kakkausar murya ga Gwamnatin tarayyar Nigeria da kuma Gwamnatin Jihar Zamfara da suji tsoron Allah su takawa wannan ta'addancin burki,su tuna Allah madaukakin Sarki zai tambayesu akan al'ummar da suke jagoranta.
Gwamnatoci suyi abinda ya dace wurin ceto rayukkan al'umma wadanda suke ci gaba da salwanta a kullum!
Al'umma na cikin matsanancin halin rayuwa! Ga tsoro da fargaba a koyaushe ga kuma tsananin yunwa da wahalhalun rayuwa,wanda zuwa yanzu sabbin barayin cikin gari na ci gaba da addabar al'umma sakamakon mawuyacin halin da Gwamnati ta jefa al'umma,kasuwanci ya tsaya Chak saboda rufe kasuwanni da sauran tsauraran matakan da Gwamnati ta kakabawa al'umma da nufin yakar Yan bindiga Wanda abubuwan suna karewa ne ga talaka tunda babu abinda Yan bindiga suka fasa zuwa yanzu.
Muna kira zuwa ga Gwamnati da ta lalabi sabbin dabarun yaki da Yan Bindiga idan da gaske take yi ta bude al'umma domin neman abinci! Idan aka ci gaba da tafiya a haka idan Yan bindiga basu karasa al'umma ba to babu shakka yunwa zata kashe kowa.