Ko Sayyid Zakzaky bai je asibiti ba zai iya samun lafiya: Jinya sila ce ta samun waraka, amma Allah ne mai warkarwa


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KO SAYYID ZAKZAKY (H) BAI TAFI ASIBITI BA ZAI IYA SAMUN LAFIYA

'Dabi'a ce ta dan Adam wacce Allah ya bashi dama da iznin neman magani don magance wata cutar data shafe shi, amma dai ba maganin ne mai warkarwa ba sai da iznin Allah.

Za mu iya sanin haka ta hanyar ganin yadda jinya kan kama mutum kuma komai kudinsa yayi ta magani har fita qasashen waje, amma a qarshe ya mutu ba tare da dukiyar tasa ko maganin ya warkar dashi ba. Haka kuma takan iya kama talaka ya rasa abin neman magani ko kuma ya kasa samun haqiqanin abinda ya kamata ya samu don magance cutar tasa, amma a qarshe kuma sai kaga Allah ya warkar dashi.

ANNABI AYUBA (A.S) BAI SHA MAGANI DON CUTA BA

Duk wani abinda ka gani ya shafi bayin Allah muminai, to, jarrabawa ce wacce yayi musu domin ya daukaka matsayinsu zuwa matsayin da ba kowa ne ke samun irinsa. Su jarrabawarsu takan bambanta data kowa, domin su din wasu irin bayi ne na dabam daga cikin bayinSa.

An jarrabi Annabi Ayuba (A.S) da cuta wacce takai har gabobin jikinsa (some parts of his body) yana yankewa ya fadi zuwa qasa, wani bangaren ma tsotsotsi ne ke cinye shi. Sanin cewa jarrabawa ce daga Allah bai tashi yana fadi-tashi wajen neman magani ba, sai dai a qarshen al'amari addu'ah kawai yayi Allah ya yaye masa.

Wannan abu kuwa an tabbatar mana ne cikin Alqur'ani kamar yadda Allah (T) ke cewa:

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

وَأَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلضُّرُّ وَأَنتَ أَرۡحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ (٣٨ )

" DA KUMA AYUBA, YAYIN DA YA KIRA UBANGIJINSA (cewa) " LALLE CUTA FA TA SHAFE NI (bisa saninka, ba wai ina sanar dakai bisa rashin sani bane), KUMA KAINE MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYAWA .

'Dabari yace:

يقول تعالى ذكره لنبيه محمد صلى الله عليه وسلم: واذكر أيوب يا محمد، إذ نادى ربه وقد مسه الضر والبلاء.وكان الضر الذي أصابه والبلاء الذي نزل به، امتحانا من الله له واختبارا.

Allah (T) yana fada ne wajen ambatawa Annabinsa Muhammad (S.A.W.W): Sai ya ambaci Ayuba (cewa), yaa Muhammad ! (Ka tuna) Lokacin da ya kirayi Ubangijinsa cewa cuta da bala'i sun shafe shi. Cutar data shafe shi da kuma bala'in da ya sauko masa jarrabawa ce daga Allah zuwa gare shi (A.S).

فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ فَكَشَفۡنَا مَا بِهِۦ مِن ضُرّٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ أَهۡلَهُۥ وَمِثۡلَهُم مَّعَهُمۡ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَذِكۡرَىٰ لِلۡعَٰبِدِينَ (٤٨)

" SAI MUKA AMSA MASA (abinda ya roqa), KUMA MUKA KWARANYAR DA ABINDA KE TARE DASHI NA CUTA, KUMA MUKA ZO MASA DA IYALANSA (wadanda ya rasa su a matsayin jarrabawa) DA MISALINSU TARE DASU, RAHMA DAGA WAJENMU, DA KUMA AMBATO GA MASU IBADA ."

(Suratul-Ambiya:83-84)

Kwaranyar da cutar data shafe shi ba a sami sabani ba, domin kowa ya gani da idanunsa a wajen lokacin. Sai dai batun dawo masa da iyalin nasa ne aka sami sabani. Shin, asalin iyalansa da ya rasa ne aka dawo masa dasu anan duniya ko kuma dai a lahira ne aka dawo masa da su ?

Wasu suka ce ai asalin iyalan nasa ne wadanda ya rasa su aka dawo masa da su nan duniya da kuma qarin wasu. Wasu kuma suka ce, a'a, ba anan duniya aka dawo masa da su ba, a lahira ne.

To, ko ma menene dai Allah ya tabbatar mana da cewa ya yaye masa wannan cutar data shafe shi ta hanyar addu'ar da yayi, kuma an dawo masa da iyalansa gaba dayansu wadanda ya rasa tare da qarin wasu.

BA MAGANI NE YA DAWO DA RAN SAYYID (H) BA_

___________________________________

Shigen abinda ya sami Annabi Ayuba (A.S) ne ya sami Sayyid Zakzaky (H), domin ya rasa mafi yawa daga cikin iyalansa, kuma an lalata masa wasu gabobi (parts) na jikinsa. Qari kuma shine har ransa (soul) ya rabu da gangan jikinsa !

Bisa iko ne na Allah ya dawo masa da ransa da kuma jinin jikinsa har ya kai wannan lokaci da muke tare da shi.

Da ace zuwa asibiti ne ko shan magani, to, da tuntuni babu shi sai dai tarihinsa (H), amma ga shi nan yana raye kuma yana magana muna amfana daga gare shi.

Saboda haka ko hukuma ta bar shi ya tafi asibiti don neman qarin lafiya ko ta hana shi, hakan ba zai hana samun cikakkiyar lafiyarsa kuma ba zai hana shi yin abubuwan da yake yi kafin fadawa cikin wannan jarrabawa ba.

Amma tunda Allah ne ke saukar da jinya ko cuta kuma ya tanadar da magungunanta, sai kuma ya bamu damar zuwa wani gurin da muke ganin za a iya samun maganin wadannan cututtuka. Saboda haka haqqinmu ne ko kuma haqqinsa ne ya nemi a bashi damar zuwa wajen neman magani kamar yadda kowa ke nema har ma da azzalumai da mujurimai !

MUNA QARA GODIYA GARE KA YAA ALLAH DA KA DAWO MANA DA RAN JAGORANMU KUMA KA RAYAR DASHI HAR ZUWA WANNAN LOKACI.

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

15th October, 2021/ 10th Rabi'u Awwal, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post