Daga: Faruq Sani Kudan
A irin wannan rana ne Bature ya yi batanci da tutar Musuluncin mai ɗauke da sunan (Allahu), Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya yi bayani dan gane da wannan rana cikin bayanin na sa, ga shinan ƙasa.
Amma in ka ce eh zan je in sakawa kyanwar nan ƙararrawa, amma saboda kare ƙasata, saboda kishin ƙasar mu, to shi kenan ka ga ba addini kake ba kenan, idan ka je kyanwa ta lanƙwame ka, in aka taso ranar alƙiyama, ƙasa sai ta baka Aljanna. Shi ya sa ba zan bada rai na saboda in an tashi ranar alƙiyama, ba yadda za a yi Nijeriya ta ce ina 'ya'ya na? imma da za ta taso a ce ga Nijeriya can, Wallahi zubawa a guje za ayi.
In da za a ce ga wata can , a ce mecece? A ce Nijeriya ce, yanzu za ka ga ya tashi ya danna a guje, ya ce kar ta jawo mishi masifa. Saboda in ta ce ɗan ta ne, ya san ya shiga wuta ya gama. Nijeriya ta fito tana neman 'ya'yan ta, kana tsammanin akwai wanda zai je wajen ta ne? Kowa zai nemi wajen tserewa ne, don ya san ba za a ƙarea lafiya ba. Saboda haka ba zai yiyu na bada rai na saboda Nijeriya ba.
Saboda Nijeriya ba ta da wuta ba ta da Aljanna, Ba za ta saka min da komi ba, kuma anan a duniya ma ba za ta tsinana min komi ba, To ku gaya min waɗanda suka sadaukar da kansu don kare ƙasa, me aka musu? Har yanzu akwai waɗanda suka yi yaƙin Nijeriya, ba su gama mutuwa ba, suna nan suna garari a gari. An nuna su abin tausayi a Abuja, babukulawa, kuma wai ya bada ran sa ne don kare ƙasar nan, ba don shi ba da babu ƙasa.
Amma yanzu an yi banza da shi, wanda ya mutu, ya yi shahada don kare Nijeriya, me ake yi wa iyalansa? To don meye ne zan sadaukar da kai na saboda ƙasa? Na magani da mene? Ƙasar da a duniyar nan ma ba za ta tsinana maka komai ba. Kuma ba ta da komai a lahira. Amma saboda Allah fa, zan iya bada raina? eh, ƙwarai kuwa. Waye ya maka rana? Ok! In na bayar yaya ka gani malam? Zan sakamako. Saboda haka, in saboda Allah ne zan iya bada rai na. Don haka mu ba zai yiyu mu yi da'awa ba da sunan addini ba.
Ko da yake wanda yake baya addinin mu zai iya musharaka da mu, in shi Yana neman gaskiya, 'CONCIUOS' ɗin sa ne, yana son 'truth', yana iya kasancewa tare da mu, amma mu fa addini muke. In ba domin Addinin ba, ba zai yiwu mu yi abin da muke yi ba, domin kana cire addini zan ga shikenan, babu yadda za ayi in yi wani motsi, don shi ana son ya zama kowane motsi na ka.
Kamar yadda ya zo, 'Inna salatiy wa nuskiy wa mahya wa mamati lillahi rabbil alamin, la sharikalah wa bi zalika umurtu....' da sallah ta, da munasaka ta, dama rayuwa ta gabaɗaya. Ka ga wannan salatihi suna cikin Hanyat. amma wannan ainihin kawo tasisin abu daga ami kenan .
~Faruq Sani Kudan ( Abba Jidda )
1/10/2021-1443