@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DALILAN DA SUKA TABBATAR DA CEWA ANNABI (S.A.W.W) NE FARKON HALITTA
Ni dai ban san haqiqanin dalilin da yasa wasu ke qaryata cewa Manzon Allah (S.A.W.W) shine farkon halitta kafin Adam (A.S) ba, jahilci ne ko kuma qiyayyah ? Cikin biyu dai ba za a rasa daya ba.
Dalilai sun tabbata cikin Alqur'ani da hadisai masu nuna cewa Annabi (S.A.W.W) ne farkon halitta, domin sanin hujjijin sai kuyi haqurin biyo mu cikin wannan rubutu namu.
الآيات آل عمران (81)
" وَ إِذْ أَخَذَ اللَّهُ مِيثاقَ النَّبِيِّينَ لَما آتَيْتُكُمْ مِنْ كِتابٍ وَ حِكْمَةٍ ثُمَّ جاءَكُمْ رَسُولٌ مُصَدِّقٌ لِما
مَعَكُمْ لَتُؤْمِنُنَّ بِهِ وَ لَتَنْصُرُنَّهُ قالَ أَ أَقْرَرْتُمْ وَ أَخَذْتُمْ عَلى ذلِكُمْ إِصْرِي قالُوا أَقْرَرْنا قالَ فَاشْهَدُوا وَ أَنَا مَعَكُمْ مِنَ الشَّاهِدِينَ ."
" KUMA A LOKACIN DA ALLAH YA RIQI ALQAWARIN ANNABAWA : " YAYIN DANA BA KU (wani abu) DAGA LITTAFI DA HIKIMA, SA'AN NAN KUMA (wani) MANZO YAZO MUKU, MAI GASKATA ABINDA KE TARE DAKU ; (cewa) LALLE NE ZA KU GASKATA SHI KUMA ZA KU TAIMAKE SHI." YACE: " SHIN, KUN TABBATAR (game da wannan alqawari naku), KUMA KUN RIQI ALQAWARINA ?" SUKA CE: MUN TABBATAR ! " YACE: " TO, KUYI SHAIDA , KUMA NI A TARE DAKU INA DAGA MASU SHAIDA ."
(Al-Imraan, aya ta 81)
'Dabari ya kawo qarqashin Tafsirin wannan ayar cewa:
: {قال أأقررتم} لأنه ابتداء كلام على نحو ما قد بينا في نظائره فيما مضىوأما قوله: {قالوا أأقررنا} فإنه يعني به: قال النبيون الذين أخذ الله ميثاقهم بما ذكر في هذه الآية: أقررنا بما ألزمتنا من الإيمان برسلك الذين ترسلهم مصدقين لما معنا من كتبك وبنصرتهم..القول في تأويل قوله تعالى: {قال فاشهدوا وأنا معكم من الشاهدين} يعني بذلك جل ثناؤه، قال الله: فاشهدوا أيها النبيون بما أخذت به ميثاقكم من الإيمان بتصديق رسلي التي تأتيكم بتصديق ما معكم من الكتاب والحكمة، ونصرتهم على أنفسكم، وعلى أتباعكم من الأمم إذ أنتم أخذتم ميثاقهم على ذلك، وأنا معكم من الشاهدين عليكم وعليهم بذلك.
" YACE: " SHIN, KUN TABBATAR ?"
Yace; domin shine farkon magana bisa gwargwadon yadda akayi bayani cikin nazarinta cikin abinda ya gabata. Amma fadinSa (S.W.A):
" SUKA CE: " EH ! MUN TABBATAR (da wannan alqawari namu)." To, shi abinda yake nufi dashi : Yace, Annabawa ne wadanda Allah ya riqi alqawarinsu da abinda aka ambato cikin wannan aya:
" Mun tabbatar da abinda aka lazimta mana na daga imani da ManzanninKa wadanda ka aiko su suna masu gaskata abinda ke tare damu na daga littattafanKa, da kuma taimakonsu..."
Magana kuma cikin Tawilin fadinSa madaukaki:
" TO, KU SHAIDA ! KUMA NI TARE DAKU INA DAGA MASU SHAIDA."
Yana nufi ne da hakan wanda yabonSa ya daukaka cewa, Allah ya ce:
" Ku shaida yaa ku taron Annabawa game da abinda Ku kayi riqo da shi na alqawarinku na daga imani da kuma gaskata ManzanniNa wandandaza su zo muku da gaskata abinda ke tare da ku na littafi da hikima, kuma za ku taimake su akan kawukanku, dama wadanda ke biye daku daga al'ummu, yayin da kuka riqi alqawarinsu game da hakan, kuma Ni ma ina tare daku daga masu shaidawa a kanku da kuma a kansu kan hakan.
(Tafsirul-'Dabari)
الأعراف - (172)
" وَ إِذْ أَخَذَ رَبُّكَ مِنْ بَنِي آدَمَ
مِنْ ظُهُورِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَ أَشْهَدَهُمْ عَلى أَنْفُسِهِمْ أَ لَسْتُ بِرَبِّكُمْ قالُوا بَلى شَهِدْنا أَنْ تَقُولُوا يَوْمَ الْقِيامَةِ إِنَّا كُنَّا عَنْ هذا غافِلِينَ أَوْ تَقُولُوا إِنَّما أَشْرَكَ آباؤُنا مِنْ قَبْلُ وَ كُنَّا ذُرِّيَّةً مِنْ بَعْدِهِمْ أَ فَتُهْلِكُنا بِما فَعَلَ الْمُبْطِلُونَ ."
" KUMA A LOKACIN DA UBANGIJINKA YA KARBI (alqawari) DAGA 'YA'YAN ADAMU A BAYAYYAKINSU A ZURIYARSU, KUMA YA SHAIDAR DASU AKAN RAYUKANSU, (cewa) " ASHE BA NINE UBANGIJINKU BA ?" SUKA CE : " NA'AM, MUN SHAIDA (kaine Ubangijinmu), (Yace), " DON KADA KUCE A RANAR ALQIYAMA; " LALLE MU, GAME DA (wannan alqawarin) GAFALALLU NE ."
(A'araaf: 172)
الشعراء - (218-219)
" الَّذِي يَراكَ حِينَ تَقُومُ وَ تَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ ."
" WANDA YAKE GANINKA A LOKACIN DA KAKE TASHI TSAYE (cikin dare domin ibada). DA KUMA JUJJUYAWARKA A CIKIN MASU YIN SUJADAH."
(Shu'ara:218-219)
2242 » وابن أبي حاتم من طريقين عن ابن عباس أنه قال في هذه الآية يعني تقلبه من صلب نبي إلى صلب نبي أخرجه نبيا
Ibn Abiy Haatim ya kawo ta hanyoyi guda biyu daga Ibn Abbas (R.A) cewa ya ce cikin wannan aya. Ai abinda ake nufi shine jujjuyawarsa daga tsatson Annabi zuwa tsatson (wani) Annabin, har ya fitar dashi Annabi (a tsatson mahaifinsa Abdullahi (A.S)."
(Tafsir na Ibn Katheer)
Wannan kuwa na tabbatar mana ne da cewa da ace ba shine farkon halitta ba da kuwa ba zai biyo cikin mahaifan Annabawa (A.S) har zuwa mahaifar mahaifansa (S.A.W.W) ba, domin wanda dama babu shi ba zai biyu hanya ba , sai dai kawai a fitar dashi a inda aka so.
الأحزاب- (7-8)
" وَ إِذْ أَخَذْنا مِنَ النَّبِيِّينَ مِيثاقَهُمْ وَ مِنْكَ وَ مِنْ نُوحٍ وَ إِبْراهِيمَ وَ مُوسى وَ عِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ وَ
أَخَذْنا مِنْهُمْ مِيثاقاً غَلِيظاً. لِيَسْئَلَ الصَّادِقِينَ عَنْ صِدْقِهِمْ وَ أَعَدَّ لِلْكافِرِينَ عَذاباً أَلِيماً ."
" KUMA A LOKACIN DA MUKA RIQI ALQAWARIN ANNABAWA DAGA GARE SU, KUMA DAGA GARE KA , KUMA DAGA NUHU, DA IBRAHIMA DA MUSA DA ISAH 'DAN MARYAMA, KUMA MUKA RIQI WANI ALQAWARI MAI KAURI DAGA GARE SU.
DOMIN YA TAMBAYI MASU GASKIYA AKAN GASKIYARSU, KUMA YA YI TATTALIN WATA AZABA MAI RADADI GA KAFIRAI !"
(Ahzaab:7-8)
'Dabari yayi sharhi kan wannan ayar don a fahinci haqiqanin ma'anarta kamar haka:
:21609- حدثنا بشر، قال: ثنا يزيد، قال: ثنا سعيد، عن قتادة، قوله: {وإذ أخذنا من النبيين ميثاقهم ومنك ومن نوح} قال: وذكر لنا أن نبي الله صلى الله عليه وسلم كان يقول: "كنت أول الأنبياء في الخلق، وآخرهم في البعث " ، {وإبراهيم وموسى وعيسى ابن مريم، وأخذنا منهم ميثاقا غليظا} ميثاق أخذه الله على النبيين، خصوصا أن يصدق بعضهم بعضا، وأن يتبع بعضهم بعضا.حدثنا محمد بن بشار، قال: ثنا سليمان، قال: ثنا أبو هلال، قال: كان قتادة إذا تلا هذه الآية {وإذ أخذنا من النبيين ميثاقهم ومن نوح} قال: كان نبي الله صلى الله عليه وسلم في أول النبيين في الخلق.
Bashar ya bamu labari, yace: Yazid ya ambata yace; Sa'ed ya ambato daga Qatadata, fadinSa:
" KUMA A LOKACIN DA MUKA RIQA DAGA ANNABAWA ALQAWARINSU DA KUMA KAI DA NUHU." Yace: An ambata mana cewa Annabi (S.A.W.W) ya kasance yana cewa:
" NA KASANCE FARKON ANNABAWA A HALITTA, KUMA NA QARSHENSU A AIKO DA SAQO."............................
Muhammad Bn Bashar ya bamu labari yace: Sulaiman ya ambato, yace; Baban Hilaal yace, " Idan Qatadata ya karanta wannan ayar:
" KUMA A LOKACIN DA MUKA RIQA DAGA ANNABAWA ALQAWARINSU, DA KUMA NUHU."
Yace, Annabi (S.A.W.W) ya kasance farkon Annabawa a halitta."
(Tafsir na 'Dabari)
Kunga anan abinda ake qara tabbatar mana kenan, Annabi (S.A.W.W) shine farkon halitta daga Annabawa, wanda hakan ke nuna mana yana gaba da Annabi Adam (A.S), domin shi ma Annabi ne.
Idan kuma muka koma cikin Tafsir na Furat Bn Ibrahim za mu gani kamar haka;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
فر، تفسير فرات بن إبراهيم عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ الْفَزَارِيِّ بِإِسْنَادِهِ عَنْ قَبِيصَةَ بْنِ يَزِيدَ الْجُعْفِيِ قَالَ: دَخَلْتُ عَلَى الصَّادِقِ ع وَ عِنْدَهُ ابْنُ ظَبْيَانَ وَ الْقَاسِمُ الصَّيْرَفِيُ فَسَلَّمْتُ وَ جَلَسْتُ وَ قُلْتُ يَا ابْنَ رَسُولِ اللَّهِ أَيْنَ كُنْتُمْ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ اللَّهُ سَمَاءً مَبْنِيَّةً وَ أَرْضاً مَدْحِيَّةً أَوْ ظُلْمَةً أَوْ نُوراً قَالَ
كُنَّا أَشْبَاحَ نُورٍ حَوْلَ الْعَرْشِ نُسَبِّحُ اللَّهَ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ آدَمَ ع بِخَمْسَةَ عَشَرَ أَلْفَ عَامٍ فَلَمَّا خَلَقَ اللَّهُ آدَمَ ع فَرَّغَنَا فِي صُلْبِهِ فَلَمْ يَزَلْ يَنْقُلُنَا مِنْ صُلْبٍ طَاهِرٍ إِلَى رَحِمٍ مُطَهَّرٍ حَتَّى بَعَثَ اللَّهُ مُحَمَّداً ص ."
Daga Ja'afar Bn Muhammad Al-Fazaariyyi, da isnadinsa, daga Qabeesata Bn Yazeeda Al-Ju'ufiy yace:
" Na shiga wajen Sadiq (A.S), kuma a tare da shi akwai Ibn Zabyaan da Qaasimul-Sairafiy, sai nayi sallama kuma na zauna, kuma nace; Yaa dan Manzon Allah ! A ina kuke kafin Allah ya halicci sammai ginannu, da kuma Qasa shimfidaddiya ? Ko kuma duhu ko haske ? Yace:
" MUN KASANCE HASKE NE A GEFEN AL-ARSHI MUNA TSARKAKE ALLAH TUN GABANIN YA HALICCI ADAMU (A.S) DA SHEKARU DUBU GOMA SHA BIYAR (15,000). YAYIN DA ALLAH YA HALICCI ADAMU (A.S) SAI YA SANYA MU CIKIN TSATSONSA (mahaifa), BAI GUSHE BA YANA CIRO MU DAGA TSARKAKEKKEN TSATSO ZUWA MAHAIFA MAI TSARKI, HAR ALLAH YA TAAR DA MUHAMMAD (S.A.W.W)."
تفسير فرات: 207.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda
(08137925034)
12th October, 2021/ 7th Rabi'ul-Awwal, 1443.