Ci na gaba da Sallah, ba sallah ce ke gaba da ci ba



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ITA NUTSUWA NA DAGA CIKIN SHARADIN KARBAR SALLAH

Ba batun matsayi a wajen Allah ake nufi ba domin sallah wajiba ce, shi kuma ci halas ne. Saboda haka da za kabar sallah bisa inkari ko kuma ka mutu baka yinta saboda bitsara da wuta za ka tafi.

Shi kuwa ci abu ne wanda ba a yin sakamako saboda yinsa ko rashin yinsa, sai dai kuma da za kaqi ci da gangan har ka rasa qarfin bautawa Allah da kuwa ka aikata babban sabo (sin).

Nutsuwa na daga cikin sharadin karbar sallah, in da ace za kayi sallah babu nutsuwa cikinta da kuwa ta zama aikin da babu lada cikinsa.

An sami hadisi daga Manzon Allah (S.A W.W) wanda Ummul-Muminina Ummus-Salamata (R.A) ta bada labari kamar haka:

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

25988- حَدَّثَنَا يَعْقُوبُ ، قَالَ : حَدَّثَنَا أَبِي ، عَنِ ابْنِ إِسْحَاقَ ، قَالَ : حَدَّثَنِي عَبْدُ اللَّهِ بْنُ رَافِعٍ مَوْلَى أُمِّ سَلَمَةَ ، عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَ : سَمِعْتُهَا تَقُولُ : سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ : " إِذَا حَضَرَتْ الصَّلَاةُ ، وَحَضَرَ الْعَشَاءُ ، فَابْدَءُوا بِالْعَشَاءِ "

Ya'aquba ya bamu labari yace: Babana ya bamu labari daga Ibn Ishaq yace: Abdullahi Bn Rafi'ata bararren bawan Ummus-Salamata ya bani labari daga Ummus-Salamata matar Annabi (S.A.W.W) yace: Na ji ta tana cewa: " Naji Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;

" IDAN (lokacin) SALLAH TAZO KUMA AKA ZO DA ABINCI (a lokacin), TO, KU FARA DA (cin) ABINCIN (kafin yin sallah) ."

(Musnad Ahmad, Musnad Ummus-Salamata, hadisi mai lamba 25,988)

                ABIN LURA

           _________________

Lokacin salloli na da yalwa yadda takai ana cewa tana da lokacin Muktari dana Lalura, kuma cikin kowanne daga cikinsu ka sallaci sallah ta karbu wajen mai karbar (Allah). Kai ! Har ma bayan lokacin Lalurar tata ana karbarta.

Saboda haka cikin kowanne lokaci kayi za a karbe ta, sai dai kawai ace anfi so ayi ta cikin farkon lakaci, kuma kawanne lokacin ma bata karbuwa sai anyi ta cikin nutsuwa.

Abinci ma ana iya cinsa cikin kowanne lokaci, amma dai sanin kowane matuqar sun hadu lokaci guda da sallah sai an sami rinjayen jan hankali daga abinci. Saboda haka cin abincin a farko shi zai bada nutsuwa cikin sallar. Amma matuqar ana ganin abinci kuma tare da yunwa, to, ba za a sami cikakkiyar nutsuwa cikin sallar ba. Idan aka rasa nutsuwa kuma an rasa sallah.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

22nd September, 2021/ 16th Safar, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post