'Yan uwa Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na Jasaz ammar bini yasir zone, sungudanar da taron tunawa da ranar haihuwa Sayyid Ahmad wanda ya gudana acikin garin Kudan.
Bayan buɗe fili da addu'a wanda wakilin matasa na 'yan kin Gabas malam Murtala Sani Kudan shi ne ya buɗe taro da addu'a kafin ashiga cikin filin jawabai akan Sayyid Ahmad da gwala-gwalan jawabai dan gane da rayuwa Shahid Commander Ahamd.
Babban baƙo mai jawabi Malam Isma'il Samuru wanda ya ɗauko rayuwar Sayyid Ahmad ya yi bayani dan gane da yadda aka haifi Sayyid Ahmad tun, daga yarintarsa har zuwa girmansa da yadda ya gudanar da karatunsa amakarantu tungada fodiyya har zuwa illah, masha Allah.
Sannan yaƙara da cewa shi Sayyid Ahmad ya babban ta da sauran duk kanin wani matahi, tundaga ibadarsa harzuwa loƙacin da ya yi shahada, akawai akin da yake gaban mu wanda shahid Ahmad ya ke yawan ce mana musani yanzu babban aikin dake gabanmu shine dole sai munsadaukar da komai namu to shi ne addini yake da iko da mu.
Akwai jagora acikin mu nauyin kare wannan jagoran, yana cikin mu ne bawai yana cikin wasu mutane ba.
Ga kaɗan daga cikin hotunan da muka ɗauko muku.
Faruq Sani Kudan
Tare Da
Abbakar Ibrahim kudan
Kudan media Forum
15/10/2021-81443h