Halin da Kabilar Fulani ke ciki a Yankin Mashegu (Log) Jihar Neja Abun ya yi muni Sosai ana Kisan Rashin Imani ga Kabilar Fulani a Jihar Neja Mashegu (Log), a bun Bai tsaya ga Maza ba ya Kai ga Mata duk da Hakan kuma Bai tsaya a Mata ba abun ya kai ga Jarinrai na Goye Ana Yanka su irin yankaCikkakenn da akewa Dabbobi.
Wata Mata Bafulatana da 'Yan Banga da Yan Sakai da Sauran Al'ummar Gari suka tarar a Daji, inda Suka Tarar da Baiwar Allah tana Goye da Jariri kawai Suka Karbi Jinjirin Suka Yanka shi gaban'ta tana Kallo', Mahaifiyar Jinjirin tayi Yunkurin Ceton Rayuwar Dan nata ya yin da take Yunkurowa Domin Ceton Rayuwar Dan'ta kawai Suka Bege Matar da Bindika ta Fadi Kasa Suka Halbe ta take rai ya yi halinsa.
Wan Nan Mummanan Zaluncin da akewa Kabilar Fulani ya biyo Bayan wani Hari ne da "Yan Bindiga Suka Kai a wani Masallaci Dake wani Gari Yankin na Mashegu, inda "Yan Bindigar suka Kashe Mutum Takwas Khana sukayi Awon Gaba da wasu daga cikin Masallatan Suka Tafe da su Jeji, wan nan Harin ne ya yi Sanadiyar wan nan Kisan da akewa Fulani Kisan na Gilla.
Kamar Yanda Rahotanni ke Nunawa cewa Chiyaman na Mashegun ne ya bada Umarnin cewa duk inda akaga Bafulatani a kashe shi kwai ba Babba ba Yaro, komai zaman Dan Fulani Kankana A kashe shi Domin Kawai ana Zargin Kabilar ta Fulanin tana da Hannu a cikin Haraharen da ake Kai a Garuruwan Yankin na Mashegu.
Yanzu Halin da ake ciki a Yankin Duk inda akaga Bafulatani Kashe shi akeyi ba tare da wani Bincike ba, ba Ruwan su da cewa sai an tabbatar da Mutum Barawo ne san nan za a Kashe Shi a a idan dai mutum Bafulatani ne tou Hunkuncin Kisa ne akan'sa.
A farkon Fara wan nan Aikin Mutanen Gari masu Fadin Ra'ayoyin su A cikin Kashi 100% Sama da 90% suna tare da Aikin cewa Haka ya yi dai dai, Amma izuwa yanzu ganin Yanda ake gudanar da aikin ba Imani Kisan Gilla kawai akan Wadda Bai jiba ba gani ba, yasa Cikin Mutum 90% din nan sama da 85% sun Janye akan wan nan ra'anin nasu na ganin Kisan Fulanin Dai dai ne.
Yanzu suna Fadin cewa Gaskiya Abunda ake ba Dai dai bane har wasu na fadin cewa Zalunci ne kawai, har suna Baiyana cewa ai In barayi Za ayi Magani an san dajin da suke, ai ba cikin Gari suke ba amma yaza ace Azo gari adinga kisan wanda baiji ba bai gani ba, gaskiya wan nan Abun Zalunci ne idan "Yan Bindiga za a Kashe Ai ansan inda za aje a tarar dasu bawai azo gari ko Ruga ana Kisan Jama'a ba.
Wan nan Ra'ayin Al'umman Yanken ne daga cikin masu ganin Abunda ake bai dace ba kuma Zalunci ne, sai dai duk da Al'umma sun fara fahimtar Hukuncin baiyi ba har yanzu ba wani Babba a Neja da yafito yayi magana ya Nuna Rashin Dacewar Hakan.
Idan ka karanta Rubutun nawa kafin kace komai ka tuna mi Allah yace dangane da kashe Mumini, idan kace ai Bafulatani ne sai nace maka waye ya gaya maka ana Haihuwar Jinjiri ba Mumini ba? Bari Nayi maka Misali dai dai da Hankalin ka cewa ko Fasto ya Haihu Tou Yaron da ya Haifa Mumini ne Bawan Allah da an taba shi Allah Zaiyi Fushi, Mai karatu kayiwa kanka Alkalanci.
Tushe: Shafin Gaskiya Daya ce
Sunday/ Act/301/10/2021.