_________________________________
A ci gaba da kaddamar da hare-haren ta'addancin da ke gudana a Shinkafi da kewaye,jiya Maharan sun harbe mutane biyu a garin Shinkafi har lahira.
Al'amarin ya faru ne a lokacin da suke gabatar da aikin gona a karkarar "RANJI" da ke Shinkafi,karkarar na makwabtaka da garin Kamarawa dake Karamar hukumar mulkin Isa ta Jihar Sakkwato,garin da yanzu ya kasance hannun Yan bindigar,kuma babbar Shalkwatar Yan bindiga a yankin.
Maharan sun yiwa daya daga cikin mamatan harbi uku,harbi daya a kafa biyu kuma a hannu.An garzaya da shi zuwa babbar asibitin Gwamnati dake garin Shinkafi (General Hospital Shinkafi) inda aka cire harsasan kuma akayi mashi abinda ya dace.Daga bisani kuma Allah yayi mashi cikiwa.
Dayan mamacin kuma Yan Bindigar sun kama shi ne suka tafi da shi,daga bisani suka kashe shi.Zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton ba a samu dauko gawarsa ba.
Wadanda wannan harin ta'addancin ya rutsa da su sun hada da:-
1. Abdulmutallib Abubakar Liman Shinkafi.
2. Iliyasu Sabon Gari Shinkafi.
Zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton an gabatar da janazar Abdulmutallib Abubakar Liman bisa koyarwar addinin Musulunci.Babban Limamin Masallacin Juma'a na daya ne Liman Mahmoud Muhammad ya jagoranci sallar janazar.
Allah ya jikansu da Rahama ya karbi Shahadarsa,su kuma makisan da masu daukar nauyin kisa Allah ya bimuna kadin jinanan Yan uwanmu da suke zubarwa a kullum ba tare da hakkin Shari'a ba sai dai saboda Zalunci.
Allah gatan bawa
ReplyDelete