Zamfara Update:- Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji Biyu a Garin Badarawa Dake karamar Hukumar Mulkin Shinkafi Dake Jihar Zamfara

 


_________________________________

Ma''asumah Nigeria  News Update 

Rahotannin da ke fitowa daga garin Shinkafi na Jihar Zamfara na nuna cewa Mahara Yan Bindiga sun kashe sojoji biyu a garin Badarawa da ke karamar hukumar mulkin Shinkafi ta Jihar Zamfara.


Yan ta'addar sun kashe sojojin ne a lokacin da suke gabatar da Sallar isha'i inda suka budewa Sojojin wuta! Bayan fatattakar da suka yiwa Sojojin sun rutsa kai cikin mazauninsu suka sace gaba dayan abincin Sojojin.


A karamar hukumar mulkin Shinkafi dai an wayi gari a kullum sai an kashe mutane kuma sai anyi garkuwa da wasu! 


Zuwa yanzu dai akwai daruruwan mutane a hannun Yan bindigar wadanda suke garkuwa da su.


Al'umma dai na ci gaba da kokawa bisa takurar da suke ciki a Jihar Zamfara.Wasu ma suna furta cewa wannan hali da Gwamnati ta sanya al'umma Yunkurin karasa al'ummar ne baki daya.


Zuwa yanzu dai ana ci gaba da kwashe ragowar Sojojin da ke akwai a Shinkafi,Wanda hakan shiri ne na ganin bayan al'umma baki daya.


Muna neman addu'oinku bisa Yunkurin Gwamnatin Buhari da Gwamnatin Jihar Zamfara na ganin bayan al'ummar Jihar Zamfara.

MA'ASUMAH TV

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post