Muqabalar Imam Ali (A.S) da yahudawan Khaibara



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ANNABI (S.A.W.W) SUKA NUFA SAI SUKA SAMI ABUBAKAR

Yau muna tafe ne da wata Muqabala wacce Yahudawan Khaibara suka sami Abubakar Bn Quhafata da ita ya kasa amsawa, saboda haka sai ya tura su zuwa ga Imam Ali (A.S) don gudun jin kunya.

Ga yadda ta fara da kuma yadda aka qare ta ;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

الخصال أَبِي عَنْ سَعْدٍ عنْ أَحْمَدَ بْنِ الْحُسَيْنِ بْنِ سَعِيدٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَبِيهِ رَفَعَهُ إِلَى بَعْضِ الصَّادِقِينَ مِنْ آلِ مُحَمَّدٍ ص قَالَ: جَاءَ رَجُلَانِ مِنْ يَهُودِ خَيْبَرَ وَ مَعَهُمَا التَّوْرَاةُ مَنْشُورَةً يُرِيدَانِ النَّبِيَّ ص فَوَجَدَاهُ قَدْ قُبِضَ فَأَتَيَا أَبَا بَكْرٍ فَقَالا إِنَّا قَدْ جِئْنَا نُرِيدُ النَّبِيَّ لِنَسْأَلَهُ عَنْ مَسْأَلَةٍ فَوَجَدْنَاهُ قَدْ قُبِضَ فَقَالَ وَ مَا مَسْأَلَتُكُمَا قَالا أَخْبِرْنَا عَنِ الْوَاحِدِ وَ الِاثْنَيْنِ وَ الثَّلَاثَةِ وَ الْأَرْبَعَةِ وَ الْخَمْسَةِ وَ السِّتَّةِ وَ السَّبْعَةِ وَ الثَّمَانِيَةِ وَ التِّسْعَةِ وَ الْعَشَرَةِ وَ الْعِشْرِينَ وَ الثَّلَاثِينَ وَ الْأَرْبَعِينَ وَ الْخَمْسِينَ وَ السِّتِّينَ وَ السَّبْعِينَ وَ الثَّمَانِينَ وَ التِّسْعِينَ وَ الْمِائَةِ فَقَالَ لَهُمَا أَبُو بَكْرٍ مَا عِنْدِي فِي هَذَا شَيْ‏ءٌ ائْتِيَا عَلِيَّ بْنَ أَبِي طَالِبٍ ع قَالَ فَأَتَيَاهُ فَقَصَّا عَلَيْهِ الْقِصَّةَ مِنْ أَوَّلِهَا وَ مَعَهُمَا التَّوْرَاةُ مَنْشُورَةً فَقَالَ لَهُمَا أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع إِنْ أَنَا أَخْبَرْتُكُمَا بِمَا تَجِدَانِهِ عِنْدَكُمَا تُسْلِمَانِ قَالا نَعَمْ قَالَ:

Ya zo cikin Khisaal, daga Ahmad Bn Hussaini Bn Sa'eed, daga babansa daga Ja'afar Bn Yahya, daga babansa, ya daukaka shi (hadisin) zuwa sashen wadanda ake gaskata su Iyalan Muhammad (S.A.W.W) yace:

Wasu mutane biyu daga Yahudawan Khaibara tare dasu akwai Attaura shahararriya, suna nufin Annabi (S.A.W.W) ne sai suka same shi ya rasu (S.A.W.W). Sai suka jewa Abubakar suka ce :

" Lalle mu munzo ne da nufin samin Annabi muyi masa wasu tambayoyi, sai muka same shi ya rasu." Sai yace:

" MENENE TAMBAYOYIN NAKU ?" Sai suka ce:

" Ka bamu labari game da (ma'anar wadannan adadin lambobi) 1, da 2, da 3 da 4 da 5 da 6 da 7 da 8 da 9 da 10 da 20 da 30 da 40 da 50 da 60 da 70 da 80 da 90 da kuma 100 ?

Sai Abubakar yace musu:

" GASKIYA TARE DANI BABU WANI ABU NA AMSOSHIN WADANNAN (tambayoyi), KU JEWA ALIYU BN ABIY 'DALIB (A.S)."

Yace; sai suka je masa suka bashi labari tun daga farkonta , kuma tare dasu akwai Attaura shahararriya.

Sai Amirul-Muminina yace musu;

" IDAN HAR NA BAKU LABARI DA ABINDA KUKA SAME SHI A WAJENKU (cikin Attaura) ZA KU MUSLIMTA ?" Suka ce;

" Eh (za su muslimta) ."

Sai Imam Ali (A.S) yace musu;

" أَمَّا الْوَاحِدُ فَهُوَ اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ وَ أَمَّا الِاثْنَانِ فَهُوَ قَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَ‏:

" AMMA 1, SHINE ALLAH SHI KADAI YAKE BA SHI DA ABOKIN TARAYYA. AMMA KUMA 2 SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA;

" لا تَتَّخِذُوا إِلهَيْنِ اثْنَيْنِ إِنَّما هُوَ إِلهٌ واحِدٌ "

" KADA KU RIQI ABABAN BAUTA GUDA BIYU, ABIN SANI SHINE ABIN BAUTA GUDA 'DAYA (1)."

وَ أَمَّا الثَّلَاثَةُ وَ الْأَرْبَعَةُ وَ الْخَمْسَةُ وَ السِّتَّةُ وَ السَّبْعَةُ وَ الثَّمَانِيَةُ فَهُنَّ قَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ فِي أَصْحَابِ الْكَهْفِ‏ :

" AMMA UKU DA HUDU DA BIYAR DA SHIDA DA BAKWAI DA TAKWAS SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN LITTAFINSA GAME DA ASHABUL-KAHFI:

" سَيَقُولُونَ ثَلاثَةٌ رابِعُهُمْ كَلْبُهُمْ وَ يَقُولُونَ خَمْسَةٌ سادِسُهُمْ كَلْبُهُمْ رَجْماً بِالْغَيْبِ وَ يَقُولُونَ سَبْعَةٌ وَ ثامِنُهُمْ كَلْبُهُمْ‏."

" DA SANNU ZA SUCE UKU NE NA HUDUNSU KARENSU, KUMA SUNA CEWA BIYAR NE NA SHIDANSU KARENSU, SUNA TA SHACI-FADI NA GHAIBU, KUMA SUNA CEWA BAKWAI NE NA TAKWAS 'DINSU KARENSU ." (Musayar maganganu da jama'a ke yi game da adadin wadanda suka zauna cikin Kogo, As'habul-Khahfi).

 وَ أَمَّا التِّسْعَةُ فَهُوَ قَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏:

" AMMA TARA SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA:

" وَ كانَ فِي الْمَدِينَةِ تِسْعَةُ رَهْطٍ يُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ وَ لا يُصْلِحُونَ‏."

" YA KASANCE A CIKIN MADINAH AKWAI WASU JAMA'A GUDA TARA SUNA BARNA CIKIN QASA BA SA YIN GYARA ."

 وَ أَمَّا الْعَشَرَةُ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَ‏ :

AMMA GOMA SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA:

" تِلْكَ عَشَرَةٌ كامِلَةٌ ."

" WADANCAN SUNE GOMA CIKAKKU ." (Wadanda Allah ya qarawa Annabi Musa (A.S) kan darare talatin na farko da ya bashi don yin miqatinsa).

وَ أَمَّا الْعِشْرُونَ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏:

AMMA ASHIRIN SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA:

" إِنْ يَكُنْ مِنْكُمْ عِشْرُونَ صابِرُونَ يَغْلِبُوا مِائَتَيْنِ‏."

" IDAN YA KASANCE DAGA CIKINKU AKWAI MUTANE ASHIRIN MASU HAQURI ZASU RINJAYE MUTANE 'DARI BIYU (200) ." (Magana kan hana gudu wajen yaqi komai yawan abokan gaba (enemies) kafin ayi sassauci da cewa kowanne musulmi na daidai da arna guda biyu).

 وَ أَمَّا الثَّلَاثُونَ وَ الْأَرْبَعُونَ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏:

AMMA TALATIN DA ARBA'IN SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN LITTAFINSA:

" واعَدْنا مُوسى‏ ثَلاثِينَ لَيْلَةً وَ أَتْمَمْناها بِعَشْرٍ فَتَمَّ مِيقاتُ رَبِّهِ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً."

" KUMA MUKA YIWA MUSA WA'ADIN DARARE TALATIN SAI MUKA CIKA MASA DA GOMA SAI MIQATIN UBANGIJINSA YA CIKA DARARE ARBA'IN. " (Adadin dararen da Annabi Musa (A.S) yayi kenan yayin miqatinsa ga Ubangijinsa).

 وَ أَمَّا الْخَمْسُونَ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَ‏ :

AMMA HAMSIN SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA:

" فِي يَوْمٍ كانَ مِقْدارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ."

" CIKIN WANI YINI WANDA YAKE DAIDAI DA SHEKARU DUBU HAMSIN." (shekarun kana na duniya da ke daidai da yini daya (1) na lahira).

 وَ أَمَّا السِّتُّونَ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏ :

AMMA SITTIN SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN LITTAFINSA:

" فَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَإِطْعامُ سِتِّينَ مِسْكِيناً "

" GA DUK WANDA BAI DA IKO (na yin azumi) YA CIYAR DA MISKINAI SITTIN." (Adadin kwanakin kaffarar wanda ya karya azumi da gangan).

وَ أَمَّا السَّبْعُونَ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏:

AMMA SABA'IN SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN LITTAFINSA:

" وَ اخْتارَ مُوسى‏ قَوْمَهُ سَبْعِينَ رَجُلًا لِمِيقاتِنا ."

" SAI MUSA YA ZABI MUTANENSA (su) SABA'IN DOMIN MIQATINSA." (Adadin mutanen da Annabi Musa ya zaba daga cikin al'ummarsa don miqatin Ubangiji).

وَ أَمَّا الثَّمَانُونَ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏ :

AMMA TAMANIN SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN LITTAFINSA:

" وَ الَّذِينَ يَرْمُونَ الْمُحْصَناتِ ثُمَّ لَمْ يَأْتُوا بِأَرْبَعَةِ شُهَداءَ فَاجْلِدُوهُمْ ثَمانِينَ جَلْدَةً "

" KUMA WADANDA KE JIFAR KATANGAGGU (da qazafin yin zina) SA'AN NAN BASU ZO DA SHAIDU HUDU BA, TO, KUYI MUSU BULALA TAMANIN ." (Adadin bulalar da ake yiwa wanda ya yiwa dan'uwansa qazafi aikata Zina ba tare da ya kawo shaidu hudu (4) ba).

وَ أَمَّا التِّسْعُونَ فَقَوْلُ اللَّهِ 

عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏ :

AMMA CASA'IN SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN LITTAFINSA:

" إِنَّ هذا أَخِي لَهُ تِسْعٌ وَ تِسْعُونَ نَعْجَةً."

" WANNAN 'DAN'UWANA NE YANA DA YAKE DA TUMAKI CASA'IN DA TARA........." (Qissar wadanda suka kawo qara zuwa ga Annabi Dauda (A.S).

 وَ أَمَّا الْمِائَةُ فَقَوْلُ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فِي كِتَابِهِ‏:

AMMA 'DARI (100) SHINE FADIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA CIKIN LITTAFINSA:

" الزَّانِيَةُ وَ الزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ واحِدٍ مِنْهُما مِائَةَ جَلْدَةٍ."

" MAZINACIYA DA MAZINACI (wadanda basu taba yin aure ba) KUYI MUSU BULALA 'DARI ." (A matsayin haddin zina).

 قَالَ فَأَسْلَمَ الْيَهُودِيَّانِ عَلَى يَدَيْ أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ ع‏."

Yace, sai Yahudawan guda biyun suka muslimta a hannun Amirul-Muminina (A.S)

(1) الخصال 2: 148 و 149.

TABBAS, DA AN MIQA AL'AMARI GA AHLINSA TUN FARKO DA AL'UMMAR ANNABI (S.A.W.W) BASU FADA CIKIN DUHUN JAHILCI BA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

          (08137925034)

12th September, 2021/ 6th Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post