Matar da ta tsira daga masu garkuwa da mutane, tayi bayanin yadda ta wakana


 Ma'asumah Nigerian News Update

A shekaran jiya Asabar 4/9/2021. Mukaci karo da wata mata Mai suna Zuwaira wadda masu garkuwa da mutane (Kidnappers) suka sako!

Daya daga cikin wakilanmu ya tattauna da Zuwaira domin jin abinda ya faru da ita.

Matar take cewa "Alhamdulillahi nayi nasarar fita daga hannun miyagun mutane masu garkuwa da mutane", In ji ta.

Sunanta Zuwaira 'yar asalin garin 'Yar Tasha ce. Suna cikin gida suna barci kawai Sai Kara kawai sukeji anata harba bindiga kafin kace kwabo har sun kashe mutun 8 kafin su shiga cikin gidan nasu Zuwaira.

Yan bindigan sun kama Zuwaira da wasu mata guda biyu da maza biyu sukayi awon gaba dasu zuwa cikin daji.

Zuwaira ta kasance tanada Juna biyu (ciki) kuma tanada yaro kimanin Dan shekara ukku (3) harda yaron suka hada suka tafi dashi cikin daji har tsawon kwana 22 suna cikin daji.

Zuwaira ta shaida Mana cewa mazanda aka kamasu a tare dasu duk wannan kwanuka da aka dauka suna a daurene basa kwancesu, sannan suna basu abinci sau Daya a Rana.

A cikin wannan yanayi Zuwaira idan suka bata. Abincinta saita raba biyu domin ta ajewa yaronta zuwa anjima saboda tasan bazasu Kara masaba Sai kuma gobe, a haka suka share kwana 22 suna a tsare cikin daji ba tareda wani muhalli Mai kyauba.

Sun sakasu cikin wata bukka wadda idan ruwan sama yazo saidai su kwana a tsugune Babu barci domin ruwa ya jike gurin Allah ya kyauta.

ABINDA YASA SUKA SAKENI @Zuwaira.

Duba da ina dauke da Juna biyu (ciki) kuma inada yaro Dan shekara ukku Sai sukace mani zasu tausaya Mani domin cikin yayi nauyi da yawa, wannan shine babban dalilin da yasa suka sakeni.

Sun kawoni bakin wani gari sukace mani in shiga garin in nemi temako a kaini gida, haka nayi kuma gashi har na tsinci kaina a gareku Allah ya baku ladan gudunmuwar da kukayi Mani Nagode.

Wakilanmu::: Ammar Abubakar Shadow.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post