@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN MAI QARA YA KAWO SHAIDU WANDA AKE TUHUMA YAYI RANTSUWA YA ZA KAYI ?
Bisa nassin da ake kawowa daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa yace; " KAWO SHAIDU NA GA WANDA YAYI QARA, KUMA RANTSUWA NA KAN WANDA YAYI MUSU."
Wannan hadisi ya zama abin dogaro ga masu zartar da hukunci in anzo musu da tuhuma kan laifin da wani ya aikata ko ake zarginsa da aikatawa.
Yadda abin yake shine, duk wanda yayi qarar wani bisa zarginsa da aikata wani abu ba daidai ba akan nemi shaida ne ko shaidu daga wajen mai qarar don tabbatar da abinda ya fada. Idan shaidu suka tabbata daga bangaren mai qara sai kuma wanda ake qarar yayi musu, to, sai ace masa yayi rantsuwa kan abinda yake fada don qaryata mai qara da kuma shaidunsa.
Da shike ba'a taba zartar da irin wannan hukunci a gabana ba, amma dai abinda ke daure min kai shine, idan aka sami shaidu daga mai qara sannan aka samu shaidu daga wanda ake tuhuma kuma bisa bincke sai aka samu shaidun kowa na da qarfi wanne irin hukunci za a yanke?
Ko kuma aka ce mai qara ya kawo shaidu shi kuma wanda ake tuhuma ya rantse kan cewa shaidar da shaidun suka bayar qarya ne ba gaskiya ba hukunci zai hau kan wanene?
Dalilin wannan tambaya shine, za a iya samun shaidu masu bada shaidar qarya kuma wanda ake tuhuma ya kasa kawo nasa shaidun da za su kare shi. Wataqila yayin da abin ya faru babu shaidu, ko kuma shaidun nasa su nuna cewa basu san wani abu kan abinda ake tuhumar tasa ba.
Kada wani yayi mamakin kasantuwar hakan, domin sanin hakan zai iya faruwa ne yasa Allah (T) yayi gargadi da cewa kada a boye shaida idan an kira mutum.
HUKUNCIN DA MU'AWUYA YA KA SA ZARTARWA BISA ILIMINSA
Ku biyo mu cikin wannan riwaya don sanin yadda ake yanke hukunci.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
المناقب لابن شهرآشوب ابْنُ بُطَّةَ وَ شَرِيكٍ بِإِسْنَادِهِمَا عَنِ ابْنِ أَبْجَرَ الْعِجْلِيِّ قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ مُعَاوِيَةَ فَاخْتَصَمَ إِلَيْهِ رَجُلَانِ فِي ثَوْبٍ فَقَالَ أَحَدُهُمَا ثَوْبِي وَ أَقَامَ الْبَيِّنَةَ وَ قَالَ الْآخَرُ ثَوْبِي اشْتَرَيْتُهُ مِنَ السُّوقِ مِنْ رَجُلٍ لَا أَعْرِفُهُ فَقَالَ مُعَاوِيَةُ لَوْ كَانَ لَهَا عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ فَقَالَ ابْنُ أَبْجَرَ فَقُلْتُ لَهُ قَدْ شَهِدْتُ عَلِيّاً قَضَى فِي مِثْلِ هَذَا وَ ذَلِكَ أَنَّهُ قَضَى بِالثَّوْبِ لِلَّذِي أَقَامَ الْبَيِّنَةَ وَ قَالَ لِلْآخَرِ اطْلُبِ الْبَائِعَ فَقَضَى مُعَاوِيَةُ بِذَلِكَ بَيْنَ الرَّجُلَيْنِ[1].
Ya zo cikin Manaqib na Ibn Shahar Ashub Ibn Buddata da Shareeki, da isnadinsu daga Ibn Abjaral-Ijliyyi yace:
" Na kasance a wajen Mu'awiyyah, sai wasu masu husuma biyu suka zo wajensa kan al'amarin wani tufafi (dress) . Sai dayansu yace; " TUFAFINA NE ." Kuma yazo da shaidu (don gaskata cewa wannan tufafin nasa ne). 'Dayan ma yace; " TUFAFINA NE NA SAYE SU A KASUWA WAJEN WANI MUTUM WANDA BAN SAN SHI BA."
Sai Mu'awiyyah yace; " INA MA ACE AKWAI ALIYU BIN ABIY 'DALIB (a wannan guri ya warware mana wannan rikicin)."
Sai Ibn Abjara yace, sai nace masa; " HAQIQA NA TABA GANIN ALIYU YAYI IRIN WANNAN HUKUNCI. HAKAN KUWA SHI YA BAYAR DA TUFAFIN NE GA WANDA YA KAWO SHAIDU. KUMA YA CEWA 'DAYAN; " KAJE KA NEMI WANDA YA SAYAR (don neman kudinka)."
Sai Mu'awiyyah yayi hukunci da haka tsakanin mutane biyun."
نوادر أحمد بن محمّد بن عيسى ص 60
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج101، ص: 290
Hukuncin da Imam Ali (A.S) ya zartar yayi daidai, domin kuwa zai iya kasance wanda ya sayar da kayan satarsu yayi ko kuma shima sayensu yayi daga hannun wanda ya sace su. Shi kuma wanda yayi da'awar cewa kayansa ne zai iya yiwuwa sace masa akayi kuma ya gansu hannun wannan mutumin.
Wannan hukunci kuma shi yake fassara mana cewa duk wanda ya sayi kayan sata har mai shi ya gani zai iya yin hasarar kudin da ya sayi wannan kaya, sai a bawa mai kaya kayansa. Amma ba ace lalle wannan mutumi ya zama Barawo ba kamar yadda a yanzu akeyi in har wanda aka samu da kaya ya kasa kawo wanda ya saya a wajensa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
3rd September, 2021/ 26th Muharram, 1443.