Dukkan hukunce-hukuncen Musulmi na gudana ne ta fuskoki 3, In ji Imam Ali (A.S)


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KASANCE TARE DA GIDAN ANNABTA DON SAMIN INGANTATTUN HUKUNCI

Sau da yawa wasu hukunce-hukunce kan bijiro cikin al'umma wadanda hukuncinsu bai bayyana qarara ba, sai kaga malamai na cikin al'ummar na fitar da wani hukunci na qashin kansu da sunan IJTIHADI.

Sai dai kuma cikin wannan IJTIHADIN nasu akan sami kuskure wanda kan kai a danne haqqin wani ko a zalunce shi.

To, saboda kaucewa fadawa cikin irin wannan rudani sai a kasance tare da Khalifofi sha biyu (12) na Annabi (S.A.W.W) wadanda yabar mana su kuma ya umarce mu da mubi sunnarsa da kuma tasu (A.S) don kada mu halaka.

Mu saurara muji abinda Imam Ali (A.S) ya fada game da hukuncin dake faruwa cikin al'ummar musulmi.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

الخصال أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنِ الْبَزَنْطِيِّ عَنْ أَبِي جَمِيلَةَ عَنْ إِسْمَاعِيلَ بْنِ أَبِي أُوَيْسٍ عَنْ ضَمْرَةَ بْنِ أَبِي ضَمْرَةَ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ قَالَ قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع‏ جَمِيعُ أَحْكَامِ الْمُسْلِمِينَ تَجْرِي عَلَى ثَلَاثَةِ أَوْجَهٍ شَهَادَةٌ عَادِلَةٌ أَوْ يَمِينٌ قَاطِعَةٌ أَوْ سُنَّةٌ جَارِيَةٌ مِنْ أَئِمَّةِ الْهُدَى‏[5].

Ya zo cikin Al-Kisal, daga Sa'adin daga Barqiy, daga Bazandiyyi, daga baban Jamilata, daga Isma'il Bn Abiy Awaisin, daga 'Damrata Bn Abiy 'Damrata, daga babansa daga kakansa yace: Ameerul-Mumunina (A.S) yace;

" DUKKAN HUKUNCE-HUKUNCEN MUSULMI NA GUDANA NE TA FUSKOKI UKU:-

(1)- SHAIDUN ADILAI,

(2)- KO RANTSUWA YANKAKKIYA,

(3)- KO KUMA SUNNAH MAI GUDANA DAGA LIMAMAN SHIRIYA ."

(بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏101، ص: 290

1- Wato abu na farko shine shaida daga adilai ba daga maqaryata ko maha'innata ba, idan aka samu shaida daga adilai sai a zartar da hukunci. Amma ba a la'akari da shaidar wanda ba adali ba don ba zai bada shaidar gaskiya ba. Shari'ar su Sayyid Zakzaky (H) data Sheikh Abdul-Jabbar babban abin misali ne, domin dukkan shaidun masu qara ba adilai bane.

2- Idan aka rasa shaidu adilai daga wanda yayi qara kuma wanda ake tuhuma ya rasa adilan da zasu kare shi sai a buqaci wanda ake tuhumar yayi rantsuwa don kubutar da kansa.

3- Abu na uku kuma shine hukuncin da Limaman shiriya suka riqa zartarwa bayan wafatin Annabi (S.A.W.W) tunda yayi umarni kan cewa bayan sunnarsa abi tasu sunnar.

Hakan kuwa na faruwa ne idan ya kasance an sami wani al'amari daya auku na rikici wanda bai faru a zamanin Annabi (S.A.W.W) ballantana hukuncin abin ya bayyana. Saboda haka sai wadannan limaman shiriya suyi hukunci da abinda ya bayyana daga iliminsu. Wannan abinda suka aikata ya zama sunnah abin koyi.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

3rd September, 2021/ 26th Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post