Daga: faruq Sani Kudan (Abban Jidda)
Ga masu ɗaukar cewa za a ɗauki makami ne, daman mun san wannan kiran daga maƙiyan mu ya bullo, su ke neman su burkita mana addini, su ɗauka cewa, shi addinin nan, addinin ɗaukan makami ne. In mutum ya karanta tarihin Manzo Allah (s) zai ga cewa, a da'awar sa na makka, an sa makami an kashe mutane, shahidin farko, Sumayya, an kashe ta ne da makami. Ita ta fara shahada. Na ce mata shahidin farko, dan kar na ce ma ta shahidiyar farko, ku ɗauka akwai shahidin farko Namiji. Ita ta fara shahada.
An ce, gasa mashi aka yi, aka soka mata a al'aura, a loƙacin ba abin da Musulmai suka iya yi, ba su ɗauko makami ba, saboda ba marhalan su ɗauki makami ba ne, marhalan dauriya ne, sun yi ta daurewa ne da abin da aka musu, suna cijewa, suna dakewa Bayan wannan matakin da'awa da dauriya ya yi ƙamari, ana dauriya, har an nemi mafita, sai Manzon Allah (S) ya ce to ga mafita, wasu su tafi Habasha su tsira da addinin su, suka tafi Habasha, sannan shi ma ya yi Hijira zuwa Madina.
"To ka ga wannan marhalar kenan, har ya shekara goma sha uku a Makka ba za ka ga wata aya ta Jihadi ba, sai dai a ce ku tsaida sallah, ku bada Zakka. Zakkan ma, ana fassara shi da Zakkatun- Nafs ne, ba zakkan duniyoyi ba ne, in ka ga Zakka a makka, zakkan zuciya ne, ba Zakkan dukiya ba. A Madina ne Zakkan dukiya ta zo.
To sannan Manzon nan, sai aka biyo shi da yaƙi, akai ta ma kai musu hare - hare, duk da haka ba su mayar da martini ba, har sai da aya ta sauƙo, ta ce , "Uzina Lillazina yaƙataluna bi Annahum zalimu, wa Innallaha ala nasri him laƙadir" har ma su Sahabban Annabi suka ce, ya Rasulullah (S) haka nan za su yi ta kawo mana hari, ba za muyi wani abu ba? Ya ce ni ba a ce min komai dangane da wannan ba,.
Yana jiran umarni, ka ga in da ma za ka ce waye ya yi yaƙi? Annabi ne ya yaƙe su, ko su suka yaƙe shi? Su suka yaƙe shi. Sannan kuma, loƙacin da aka bada izinin, sannan aka samu aka yi ƙwamin Badar, suka zo da Uhud, kama-kama, duka Allah (T) ya bawa Manzonsa nasara. Sannan sai da daula ta kafu, sannan aka fara kawo mata barazana, sannan ta ɗauki mataki, na kare kanta, ta gefe, har da matakin kare kanta, ta kai hari.