Ci gaba 4: Rabon Gado A Muslunci


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BABU KASON (SHARE) KAKA CIKIN QUR'ANI

Matsayi ne wanda Allah (T) ya bawa Manzonsa (S.A.W.W) yadda zai iya hukunta wani al'amari kuma Allah ya zartar ko tabbatar da wannan hukunci. Hakan kuwa na tabbatar mana ne da cewa ashe matsayin Annabi (S.A.W.W) yafi na kowa wajen Allah, domin in ba shi ba babu wani wanda zai iya hukunta wani al'amari ko kuma ya qaro wani abu cikin hukuncin Allah kuma Allah ya tabbatar dashi.

Da Allah ya tashi yin rabon gado cikin bayinsa sai ya qayyade wajen ambaton wasu daga cikinsu kamar haka:-

(1)- IYAYE,

(2)- 'YA'YA,

(3)- 'YAN'UWA NA BANGAREN UWA DA UBA KO WADANDA UBA YA HADA DA KUMA 'YAN'UWA WADANDA SUKA HADA UWA DA MAMACI. Su kuma wadannan jinsi suna gadon mamaci ne idan ya rasu bai bar wani daga cikin mahaifa ko 'ya'ya ba. Sai kuma

(4)- MIJI DA MATA.

Idan ka dauke wadannan jinsin mutane dana ambato, duk wanda kaga ya sami gadon wani ya same shi ne bisa umarnin Manzon Allah (S.A.W.W).

Bari mu kawo misali da wani hadisi guda daya don musan cewa shi kaka (grandfather) ya sami shiga cikin jinsin magada ne sakamakon umarnin Manzon Allah (S.A.W.W).

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

بصائر الدرجات الْحَجَّالُ عَنِ اللُّؤْلُؤِيِّ عَنِ ابْنِ سِنَانٍ عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ عَمَّارٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ اللَّهَ أَدَّبَ نَبِيَّهُ ص عَلَى أَدَبِهِ فَلَمَّا انْتَهَى بِهِ إِلَى مَا أَرَادَ قَالَ لَهُ- إِنَّكَ لَعَلى‏ خُلُقٍ عَظِيمٍ‏ فَفَوَّضَ إِلَيْهِ دِينَهُ فَقَالَ‏ ما آتاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَ ما نَهاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا وَ إِنَّ اللَّهَ فَرَضَ فِي الْقُرْآنِ وَ لَمْ يَقْسِمْ لِلْجَدِّ شَيْئاً وَ إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ ص أَطْعَمَهُ السُّدُسَ فَأَجَازَ اللَّهُ لَهُ وَ إِنَّ اللَّهَ حَرَّمَ الْخَمْرَ بِعَيْنِهَا وَ حَرَّمَ رَسُولُ اللَّهِ ص كُلَّ مُسْكِرٍ فَأَجَازَ اللَّهُ لَهُ ذَلِكَ وَ ذَلِكَ قَوْلُ اللَّهِ- هذا عَطاؤُنا فَامْنُنْ أَوْ أَمْسِكْ بِغَيْرِ حِسابٍ‏."

Ya zo cikin Basa'irud-Daraja na Hajjalu, daga Lu'uluwiyyi, daga Ibn Sinaan, daga Ishaq Bn Ammar, daga Abu Abdullah (A.S) yace: 

" Lalle Allah ya ladabtar da Annabinsa (S.A.W.W) bisa ladabinsa, yayin da ya kai shi zuwa ga abinda yayi nufi (na qololuwar ladabtarwa) sai yace masa:

" LALLE KAI KANA KAN KYAWAWAN 'DABI'U MASU GIRMA !"

Sai ya fawwala masa addininsa kuma yace:

" ABINDA MANZO YAZO MUKU DASHI KU RIQE SHI, KUMA ABINDA YAYI MUKU HANI A KANSA KU HANU."

Kuma lailai Allah ya raba (gado) cikin Qur'ani amma bai yi kason (share) wani abu ga kaka (grandfather) ba. Kuma lalle Allah ya ba shi daya bisa shida (1/6) sai Allah ya tabbatar masa da shi. Kuma lalle Allah ya haramta Giya bisa asalinta, kuma Manzon Allah (S.A.W.W) ya haramta dukkan wani abu wanda ke sa maye (bugarwa/gusar da hankali), sai Allah ya tabbatar masa da shi. Hakan shine fadin Allah (T) :

" WANNAN KYAUTARMU CE (wacce ake yiwa wanda ake so), KAYI BAIWA (kayi kyauta ko bayar daga abinda Allah ya ba ka) KO KUMA KA KAME (wajen qin bayarwa) BA TARE DA HISABI BA."

بصائر الدرجات ص 111 و أخرج المفيد في الاختصاص ص 310 ضمن حديث طويل.

Wannan na qara tabbatar mana ne da cewa ashe dai duk abinda Annabi (S.A.W.W) yaga dama zai fada ko ya aikata ba tare da wani zarginsa daga Allah ba, amma kuma hakan bai hana idan yayi magana ko ya zartar da wani al'amari a sami gunaguni daga cikin Sahabbansa ba.

ALLAH YA QARA SHIRYAR DAMU BISA TAFARKI MADAIDAICI

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

11th September, 2021/ 5th Safar, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post