Sheikh Adamu Ahmad Tsoho |
RABON GADO A MUSLIMCI (INHERITANCE) !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BA A TAUYE WANI ABU DAGA CIKIN KASON MIJI KO 'DAN'UWA LI'UMMI
Cikin wannan rubutu namu mun dauko mas'alar rabon gado ne wanda ya hada Miji, 'Yan'uwa Li'ummai da kuma 'Yan'uwa Li'abai, wato 'yan'uwan da mamaci ya hada dangantaka dasu ta bangaren Uwa dana bangaren Uba.
Ga yadda kason zai kasance da iznin Allah.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
تفسير العياشي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ مُسْلِمٍ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: قُلْتُ لَهُ مَا تَقُولُ فِي امْرَأَةٍ مَاتَتْ وَ تَرَكَتْ زَوْجَهَا وَ إِخْوَتَهَا لِأُمِّهَا وَ إِخْوَةً وَ أَخَوَاتٍ لِأَبِيهَا قَالَ
لِلزَّوْجِ النِّصْفُ ثَلَاثَةُ أَسْهُمٍ وَ لِإِخْوَتِهَا مِنَ الْأُمِّ الثُّلُثُ سَهْمَانِ الذَّكَرُ فِيهِ وَ الْأُنْثَى سَوَاءٌ وَ بَقِيَ سَهْمٌ لِلْإِخْوَةِ وَ الْأَخَوَاتِ مِنَ الْأَبِ- لِلذَّكَرِ مِثْلُ حَظِّ الْأُنْثَيَيْنِ لِأَنَّ السِّهَامَ لَا تَعُولُ وَ لِأَنَّ الزَّوْجَ لَا يَنْقُصُ مِنَ النِّصْفِ وَ لَا الْإِخْوَةُ مِنَ الْأُمِّ مِنْ ثُلُثِهِمْ فَإِنْ كانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذلِكَ فَهُمْ شُرَكاءُ فِي الثُّلُثِ وَ إِنْ كَانَ وَاحِداً فَلَهُ السُّدُسُ وَ أَمَّا الَّذِي عَنَى اللَّهُ فِي قَوْلِهِ- وَ إِنْ كانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَ لَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ واحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ فَإِنْ كانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذلِكَ فَهُمْ شُرَكاءُ فِي الثُّلُثِ إِنَّمَا عَنَى بِذَلِكَ الْإِخْوَةَ وَ الْأَخَوَاتِ مِنَ
الْأُمِّ خَاصَّةً.
Ya zo cikin Tafsir na Ayyashi, daga Muhammad Bn Muslim, daga Abu Ja'afar (A.S) yace: Nace masa, " Me za ka fada game da matar data rasu ta bar Mijinta da 'yan'uwanta na bangaren Uwa da kuma 'yan'uwa maza da mata ta gangaren Ubanta ? Yace;
" MIJI YANA DA RABI 1/2 , SAI AYI KASO UKU, 'YAN'UWANTA NA BANGAREN UWA SUNA DA 'DAYA BISA UKU 1/3, SAURA KASO BIYU, DUKKA MAZA DA MATAN DAIDAI SUKE (wajen samun kaso ta yadda babu wanda zai fi wani). SAURAN KASON NA 'YAN'UWA MAZA DA 'YAN'UWA MATA NE NA BANGAREN UBA, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA MACE. DOMIN SHI KASON BA A YI MASA AULU (wato ba zai kasance ta yadda wani daga cikin miji ko 'yan'uwa Li'ummai su rasa wani abu cikin kason da Allah yace a basu ba), DOMIN SHI MIJI BA ZA A TAUYE SHI DAGA RABI 1/2 BA, HAKAMA 'YAN'UWA TA BANGAREN UWA BA ZA SU RASA WANI ABU DAGA CIKIN 'DAYA BISA UKUNSU 1/3 BA.
" IDAN KUMA (su 'yan'uwa Li'ummai) SUKA KASANCE SUNFI HAKA, TO, SAI SUYI TARAYYA CIKIN 'DAYA BISA UKU 1/3, IDAN KUMA (dan'uwan) SHI KADAI NE, TO, YANA DA 'DAYA BISA SHIDA 1/6."
TO, AMMA WANNAN WANDA ALLAH YAYI MAGANARSA CIKIN FADINSA (S.W.A) ;
" IDAN MUTUM YA KASANCE AN GAJE SHI BISA KALALA KO KUMA MACE , KUMA YANA DA 'DAN'UWA KO 'YAR'UWA, KOWANNE DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BIDA SHIDA 1/6, IDAN KUMA SUNFI HAKA, TO, SAI SUYI TARAYYA CIKIN 'DAYA BISA UKU 1/3."
TO, WANNAN (magana) TANA KAN 'YAN'UWA NE WADANDA AKA HADU DASU TA BANGAREN UWA KADAI ."
تفسير العيّاشيّ ج 1 ص 226.
MISALI
________________
Mata ce ta rasu tabar mijinta da 'yan'uwa maza da mata ta bangaren Uba, da kuma 'yan'uwa maza da mata ta bangaren Uwa, tare da dukiya #1,000,000
YADDA KASON ZAI KASANCE
_____________________________
To, anan shi miji yana da rabin abinda matar tasa ta bari ne tunda bashi da 'ya'ya kuma bashi da mahaifa, 'yan'uwansa ta bangaren Uwa kuma suna da kaso daya (1) ne cikin kashi uku na dukiyar. Su kuma 'yan'uwa wadanda suka hadu ta bangaren Uba za su sami saura ne bayan an cirewa kowa kasonsa kamar yadda Qur'ani ya fada.
Saboda haka sai kason ya zama kamar haka;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
MIJI LI'UMMAI LI'ABAI
1 1 👇🏾
____ __________ _______
2 3 saura
3 + 2 👇🏾
________________________
6
KASON MIJI
3 1,000,000
__ * ________= #500,000
6 1
KASON LI'UMMAI
2 1,000,000
___ * _________=#333,333
6 1
Cikin wannan kaso za muga Miji ya sami rabin abinda matarsa ta bari, shine #500,000 daga cikin #1,000,000, su kuma 'yan'uwa wadanda suka hadu ta bangaren Uwa sun sami kashi daya (1) daga cikin kashi uku na dukiyar, shine #333,333 daga cikin #1,000,000. Saboda haka zasu raba shi ne daidai-wa-daida tsakaninsu, babu fifiko tsakanin namiji da mace.
Idan muka hada kason miji dana 'yan'uwa ta bangaren Uwa za mu sami kamar haka;
#500,000
+ #333,333
__________
#833,333
___________
Abinda ya rage daga cikin #1,000,000 bayan an cire #833,333 shine #166,6667, to, wannan sauran shine kason 'yan'uwa wadanda suka hadu ta bangaren Uba, sai namiji ya dau kaso biyu na kason mace, domin su hukuncinsu iri daya ne da hukuncin 'ya'ya idan babu 'ya'yan kuma babu 'yan'uwan mamaci wadanda suka hadu kan Uwa da Uba.
ALLAH YASA MU DACE
🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
10th September, 2021/ 4th Safar, 1443.