Bin son zuciya shine babban maqiyin mutum fiye da abokan gabansa


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

HARSHE ABU NE MAI SAURIN KAI MUTUM ZUWA WUTA

Babu wani abu mafi saurin kai mutum ga halaka fiye da bin son zuciyarsa, domin al'ummun da suka gabata dana wannan zamani biyewa son zuciyarsu ce ta sanya su aikata mumanan ayyukan da Allah yayi hani a kansu har ya kai su ga halaka.

Shi kuwa harshe abu ne wanda ake koyon yin mu'amala da shi ko sarrafa shi fiye da yadda ake koyin sarrafa makami. Idan ba ka iya sarrafa shi ba sai ya dawo kanka maimakon yaje zuwa ga abokin gaban ka.

Yazo cikin Kafiy da Bihar daga Abu Abdullah (A.S) kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

الكافي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ عِيسَى عَنِ ابْنِ مَحْبُوبٍ عَنْ أَبِي مُحَمَّدٍ الْوَابِشِيِّ قَالَ سَمِعْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع يَقُولُ‏ احْذَرُوا أَهْوَاءَكُمْ 

كَمَا تَحْذَرُونَ أَعْدَاءَكُمْ فَلَيْسَ شَيْ‏ءٌ أَعْدَى لِلرِّجَالِ مِنِ 

اتِّبَاعِ أَهْوَائِهِمْ وَ حَصَائِدِ أَلْسِنَتِهِمْ‏[42].

Yazo cikin Kafiy, daga Muhammad Bn Yahya, daga Ahmad Bn Muhammad Bn Isah, daga Ibn Mahbub, daga Abu Muhammad Al-Wabishiyyi yace: Na ji Abu Abdullah (A.S) yana cewa;

" KUJI TSORON BIN SON ZUCIYARKU KAMAR YADDA KUKE JIN TSORON ABOKAN GABANKU, DOMIN BABU WANI ABU MAFI TSANANIN GABA DA MUTANE KAMAR BIN SON ZUCIYARSU, DA KUMA ABUBUWAN DA HARSUNANSU SUKE GIRBA ."

(1) الكافي ج 2 ص 137.

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏67، ص: 83

Duk wani aikin zunubi da kaga mutum ya aikata, to, biyewa son zuciyarsa ce ya jawo masa. Haka kuma harshen mutum kan iya fitar da mutum daga muslimci cikin gaggawa, ko kuma ya jawo masa abinda zai iya halakar dashi.

ALLAH KA BAMU IKON FIN QARFIN ZUCIYARMU DA IYA SARRAFA HARSHENMU KAN HANYAR DATA DACE.

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda

       (08137925034)

21st September, 2021/ 14th Safar, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post