Babbar Magana: Cin zarafin da maa ke yiwa junansu ya samo asali ne daga Ummuhaat



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

FURUCIN HAFSA GA SAFIYYAH BAI DACE BA

Babu riba mafi girma wacce mutum zai ci fiye da ace ya zauna qarqashin wani mumini kuma ya tarbiyyantu daga gare shi.

Allah ya kawo mana wani misali cikin Qur'ani game da wasu matan Annabawa (A.S) wadanda zamansu qarqashinsu bai amfanar dasu komai ba. Haka kuma ya kawo wani misali game da salihan matan da suka rayu qarqashin fajirai amma basu cutu daga gare su ba.

Matan Annabi (S.A.W.W) ne yafi cancanta a sami abin koyi daga gare su, amma dai ga abinda Tirmidhi ya kawo cikin sahihinsa.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

«4268» حدثنا إسحاق بن منصور وعبد بن حميد قالا: أخبرنا عبد الرزاق أخبرنا معمر عن ثابت عن أنس قال بلغ صفية أن حفصة قالت بنت يهودي. فبكت فدخل عليها النبي صلى الله عليه وسلم وهي تبكي فقال: ((ما يبكيك)). فقالت قالت لي حفصة إني بنت يهودي. فقال النبي صلى الله عليه وسلم: ((إنك لابنة نبي وإن عمك لنبي وإنك لتحت نبي ففيم تفخر عليك)). ثم قال: ((اتقي الله يا حفصة)).

قال أبو عيسى: هذا حديث حسن صحيح غريب من هذا الوجه.

Ishaq Bn Mansur da Abdu Bn Humaid sun bamu labari suka ce: Abdurrazaq ya bamu labari, Mu'ammar ya bamu labari daga Thaabit, daga Anas yace:

" Labari ya isowa Safiyyata cewa Hafsat tace mata ita 'yar Bayahude ce. Sai (Safiyyat) tayi kuka (na jin wannan magana da kishiyarta ta fada a kanta). Sai Annabi (S.A.W.W) ya shiga gare alhali tana cikin kuka 😭. Sai yace:

" KUKAN ME KIKE YI ?"

Sai tace: " Hafsat ce tace min ni 'yar Bayahude ce. "

Sai Annabi (S.A.W.W) yace:

" LALLE KE 'YAR ANNABI CE, KUMA MAHAIFIYARKI TA ANNABI CE, SANNAN KUMA KE A QARQASHIN ANNABI KIKE. TO, ITA FARIYARTA NA MEYE A KANKI ?"

Sa'an nan yace:

" KI JI TSORON ALLAH YAA HAFSATU !"

Abu Isah (Al-Tirmidhi) yace: Wannan hadisi mai kyau ne kuma ingantacce, baqo ta wannan fuska.

(SUNAN-TIRMIDHI, HADISI MAI LAMBA 4268)

Bai zama abin mamaki ba in kaga ana samun cin zarafin juna tsakanin matan Shehunai ko nace manyan malamai na wannan zamani ba, domin za ace koyi suka yi, sai dai koyi ne da na abinda bai kamata a koya daga mutum ba.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

19th September, 2021/ 12th Safar, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post