@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
UMARNIN ALLAH DA AKE KAUCE MASA DON RASHIN SANIN HADARIN DAKE CIKI
Duk abinda kaji Allah yayi umarni a kansa ko yayi hani akwai wani iliminsa ne cikinsa wanda bai bayyanar dashi ba, kuma rashin kiyaye shi kan jefa mutane cikin rigima.
Umarni ne na Allah da yace ayi rubutu ko kuma kafa shaida yayin bada bashi, amma sai ya zama wasu masu ganin sunfi Allah sanin ya kamata ko kuma rufa asiri suke gujewa wannan umarni. Masu wannan tunani na ganin rashin yarda ce mutum yace ayi rubutu ko nemo shaidu yayin basu bashi. Wasu kuma mummuniyar manufa ce cikin zuciyarsu yasa basa son kafa shaida ko rubutu.
Allah madaukakin Sarki na cewa;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
" يا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذا تَدايَنْتُمْ بِدَيْنٍ إِلى أَجَلٍ مُسَمًّى فَاكْتُبُوهُ وَ لْيَكْتُبْ بَيْنَكُمْ كاتِبٌ بِالْعَدْلِ وَ لا يَأْبَ كاتِبٌ أَنْ يَكْتُبَ كَما عَلَّمَهُ اللَّهُ فَلْيَكْتُبْ وَ لْيُمْلِلِ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ وَ لْيَتَّقِ اللَّهَ رَبَّهُ وَ لا يَبْخَسْ مِنْهُ شَيْئاً فَإِنْ كانَ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ سَفِيهاً أَوْ ضَعِيفاً أَوْ لا يَسْتَطِيعُ أَنْ يُمِلَّ هُوَ فَلْيُمْلِلْ وَلِيُّهُ بِالْعَدْلِ وَ اسْتَشْهِدُوا شَهِيدَيْنِ مِنْ رِجالِكُمْ فَإِنْ لَمْ يَكُونا رَجُلَيْنِ فَرَجُلٌ وَ امْرَأَتانِ مِمَّنْ تَرْضَوْنَ مِنَ الشُّهَداءِ أَنْ تَضِلَّ إِحْداهُما فَتُذَكِّرَ إِحْداهُمَا الْأُخْرى وَ لا يَأْبَ الشُّهَداءُ إِذا ما دُعُوا وَ لا تَسْئَمُوا أَنْ تَكْتُبُوهُ صَغِيراً أَوْ كَبِيراً إِلى أَجَلِهِ ذلِكُمْ أَقْسَطُ عِنْدَ اللَّهِ وَ أَقْوَمُ لِلشَّهادَةِ وَ أَدْنى أَلَّا تَرْتابُوا إِلَّا أَنْ تَكُونَ تِجارَةً حاضِرَةً تُدِيرُونَها بَيْنَكُمْ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُناحٌ أَلَّا تَكْتُبُوها وَ أَشْهِدُوا إِذا تَبايَعْتُمْ وَ لا يُضَارَّ كاتِبٌ وَ لا شَهِيدٌ وَ إِنْ تَفْعَلُوا فَإِنَّهُ فُسُوقٌ بِكُمْ وَ اتَّقُوا اللَّهَ وَ يُعَلِّمُكُمُ اللَّهُ وَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ."
" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! IDAN KUNYU MU'AMALAR BAYAR DA BASHI ZUWA WANI LOKACI (ajali) AMBATACCE SAI KU RUBUTA SHI. KUMA WANI MAI RUBUTU YAYI RUBUTU TSAKANINKU DA ADALCI. KUMA KADA MARUBUCIN YA QI RUBUTAWA KAMAR YADDA ALLAH YA SANAR DA SHI, YA RUBUTA.
KUMA WANDA BASHIN KE KANSA SAI YASA HANNU KUMA YA JI TSORON ALLAH UBANGIJINSA, KUMA KADA YA RAGE WANI ABU DAGA GARE SHI.
IDAN KUMA WANDA BASHIN KE KANSA YA KASANCE WAWA NE KO RARRAUNA, KO KUMA BA YA IYA SA HANNU, TO, SAI WALIYYINSA YASA HANNU BISA ADALCI, KUMA KU SHAIDAI DA SHAIDU BIYU DAGA CIKIN MAZAJENKU.
IDAN KUMA BASU ZAMA MAZA BIYU BA, TO, NAMIJI 'DAYA DA MATSHAIDU DAGA WADANDA KUKA YARDA DASU DAGA SHAIDUN, DOMIN 'DAYA TA TUNAWA 'DAYAR IDAN TA MANTA, KUMA KADA SHAIDUN SUQI ZUWA IDAN AN KIRA SU.
KUMA KADA KU QOSA DA RUBUTA SHI, QARAMI NE KO BABBA ZUWA LOKACIN (da akayi alqawarinsa) , HAKAN SHINE MAFI ADALCI A WAJEN ALLAH KUMA MAFI TSAYUWA GA SHAIDA, KUMA MAFI KUSA GA RASHIN SHAKKARKU.
SAI DAI IDAN YA KASANCE KASUWANCI NE HALARTACCE DA KUKE JUJJUYA SHI A TSAKANINKU, TO, BABU LAIFI A KANKU (in) YA ZAMA BAKU RUBUTA SHI BA. KUMA KU SHAIDAR IDAN KUNYI SAYAYYA. KUMA KADA A CUTAR DA MARUBUCIN KO SHAIDUN, KUMA IDAN KUN AIKATA SHI HAKAN FASIQANCI NE GAME DA KU.
KUMA KU JI TSORON ALLAH , KUMA YA SANAR DA KU. KUMA ALLAH MASANI NE GAME DA KOMAI."
سورة البقرة: 282.
MATSALAR RASHIN RUBUTU KO SHAIDA
Komai yarda akwai mutuwa, kuma halayyar mutane ta bambanta. Wanda ake bin bashin zai iya mutuwa, kuma wasu magadansa zasu iya yin tawaye ga bashin da ake binsa matuqar babu shaidu ko babu rubutu.
Dalili kuwa shine, akwai mutane marar sa tsoron Allah wadanda zasu iya yin qari kan abinda suke bi ko suyi qarya don a basu wani abu cikin dukiyarsa.
Idan hakan kuwa ta faru an fada cikin rikici kenan wanda kan iya kai mutane ga shari'a.
DAGA ANNABI (S.A.W.W)
___________________________
قرب الإسناد هَارُونُ عَنِ ابْنِ صَدَقَةَ عَنِ الصَّادِقِ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص أَصْنَافٌ
لَا يُسْتَجَابُ لَهُمْ مِنْهُمْ مَنْ أَدَانَ رَجُلًا دَيْناً إِلَى أَجَلٍ فَلَمْ يَكْتُبْ عَلَيْهِ كِتَاباً وَ لَمْ يُشْهِدْ عَلَيْهِ شُهُوداً ."
Ya zo cikin Qarrabul-Isnaad na Harunu, daga Ibn Sadaqata, daga Sadiq, daga iyayensa (A.S) yace: Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" WASU JINSI BA A KARBA (magana) DAGA GARE SU, DAGA CIKINSU AKWAI WANDA YAYI MU'AMALAR BASHI DA WANI ZUWA WANI LOKACI, KUMA BAIYI RUBUTU A KANSA BA, SANNAN KUMA BAI KAFA SHAIDU A KANSA BA ."
قرب الإسناد ص 83 و الحديث عن مسعدة بن زياد لا عن مسعدة بن صدقة فلاحظ.
Saboda haka lalle akwai hadari na sabawa Ubangiji cikin wannan al'amari, domin in har magada suka yi musu ko kuma wanda aka bawa bashin yayi musun cewa ba ka binsa bashi, to, ko a Kotu ne ba za kayi nasara ba.
Dalili kuwa shine fadin Manzon Allah (S.A.W.W) cewa:
" KAWO SHAIDU NA KAN WANDA YAYI DA'AWA, KUMA RANTSUWA NA KAN WANDA YAYI MUSU."
Kaga kuwa idan ba ka da shaida Kotu ba za ta karbi maganarka wajen tilasta mutumin ya biya ka ba, sannan kuma ba za ta tilasta shi kan cewa dole sai ya rantse ba, domin sharadin shine sai an kawo shaidu sannan wanda ake tuhuma yayi rantsuwa in bai yarda da shaidar shaidun ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
5th September, 2021/ 28th Muharram, 1443.