YAN BINDIGA SUN KASHE MUTANE BIYAR(5) SUN RAUNATA SHIDDA(6) A HARIN DA SUKA KAI A GARIN SHINKAFI JIYA ALHAMIS
__________________________________
A ci gaba da tabarbarewar tsaro a Jihar Zamfara musamman a yankin Shinkafi inda babban dan ta'adda Kachalla Bello Turji ke ci gaba da Kai hare-haren ta'addanci,jiya Alhamis ya kaddamar da wani harin ta'addancin a cikin garin Shinkafi da ke Jihar Zamfara.
Al'amarin ya faru ne a anguwar Yar Sankalawa dake cikin garin na Shinkafi, a lokacin da ake gabatar da Sallar Magrib.Maharan sun kawo samamen ne inda suka budewa masallata wuta babu kakkautawa,suka tsare masallacin duk wanda ya fito su harbe.
Zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton mutane hudu (5) sun rigamu gidan gaskiya. Wadanda maharan suka kashe sun hada da:-
1. Malam Dankashe
2. Muhammad Sarhabilu
3. Maigida Abbah
4. Hassan (Dandan Ta'addo)
5. Ahmad Ibraheem Yarkofa.
Zuwa wannan lokaci da muke hada wannan rahoton akwai mutane shidda(6) da ke kwance a asibitin Gwamnati da ke garin Shinkafi.
Cikin kaduwa da koke-kike aka gabatar da janazar mutane hudu Kai tsaye wanda shi na biyar din zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton ba a gabatar da janazar sa ba,saboda ya yi wafati ne bayan anyi janazar hudun.
Al'umma dai na ci gaba da kokawa akan halin da garin Shinkafi yake ciki na kisa babu sassautawa a irin wannan lokaci da Gwamnatin Jihar Zamfara ke ikirarin tana galaba akan Yan bindiga da suka addabi jahar.