Zo kaji ɗan uwa: Wasu abin lura game da Ittifada, da tarkon gwamnati


 Ma'asumah Nigerian News Update

Tare da Muh'd Aliyu Daud (Dansudan) 

070-32803940.

 Shi ITTIFADA wani alami ne wanda duk wanda ya sakashi yana alamta mutum ne cewa yana tare da Falesdinawa masu gwagwarmayar neman 'yancinsu, na danniya da kisa da Isra'ila take musu, wato yana alamta mutum a matsayin dan Gwagwarmaya Wanda bayason zaluncin Azzalumai.

 Shi ITTIFADA sakashi alami ne na nuna goyon bayan yunqurin Falesdinawa ne, don kare kansu daga zaluncin Isra'ila da take yi musu sama da shekaru masu yawa.

  ITTIFADA Sayyid Khamna'i ne ya fara amfani da ITTIFADA din a matsayin alamin nuna jinqai da tausayi, ga Falesdinawa da nuna cewa kana tare dasu, za ka tayasu alhinin zaluncin Isra'ila garesu, zaka tayasu Gwagwarmaya. Sai ya zama shi saka Ittifadan ma'anarsa ta zama haka! Ba wai ado bane da gaye ba.

  ITTIFADA Sayyid Khamna'i ne ya assashi ya zama alamin nuna goyon baya ga Faledinawa don ya sakashi da nunashi a matsayin alamin nuna goyon bayan Falesdinawa, na yunqurin da suka yi don kauda zaluncin Isra'ila gare su.

  Mu anan gida kuma Nigeria, mu 'yan'uwa ittifadan da muka shina shine Mai dauke da hoton su Sayyid Zakzaky (H). Wanda hakan ya dace gayar dacewa! Wanda su Sayyid Zakzaky (H) ne suka farkar damu kan lamarin Falesdinawa.

 Wanda mu anan gida Nigeria indai za a yi Ittifada mai hoto, Mai hoton su Sayyid Zakzaky (H) shine kawai ittifadan da ya fi dacewa ga 'yan'uwa, sabida dukanmu mu 'ya'ya ne ga Sayyid Zakzaky (H), kuma shine Jagoranmu, Shine Mujaddadin wannan qarnin, kuma Munsha fada gabaki dayanmu akan Zakzaky (H), mu bamu shakkar uban kowa! Sannan akan Zakzaky (H) sai dai a qarar damu. Dukanmu bamu da sabani ga hakan. Toh in hakane kuwa bai dace kuma mu bawa makiyanmu damar raba kanmu ba, ta yanda za suji dadin yaqarmu, sannan su wargazamu, harma suji cewa zasu iya wargaza Harka din gabaki daya.

  Ya kamata 'yan'uwa su dena yin gaban kansu kafin su yi abu su tuntuba, don gujewa fadawa tarkon makiyanmu, sunanan sun saka mana tarakuna da yawa don mufada mu rarraba! A dena yin abu gabankai ba tare da an tuntubi wa'yanda suka dace ba, mufa ba harigido bane ba kamar yadda su Sayyid Zakzaky (H) suka ce.

 Mutum kuma ya rinqa dogon tunani da nazari na duk abinda zai yi, kafin ya aikata shi, in yaga cewa, zai harfar da jayayya da rabuwarkai ga 'yan'uwa sai ya barshi, koda abun zai amfanar da shi ne. Idan yasan yinsa zai harfar da matsala ya barshi shi ya fi al-khairi. In har da gaske don Allah yake bin su Sayyid Zakzaky (H) bai kamata ya kawo abinda zai jawo cece-kuce da rabuwar kai na 'yan'uwa ba!

Imam Ali (A.S) yace "Khadibun Nasa qadari Uquluhum" Fassara "Ka yi magana da mutane dai-dai da hankalinsu"

Kaga kenan ya Dan'uwa ka yi komi a Harka dai-dai yanda kowa zai fahimta sannan bazai kawo cece-kuce ba, wanda zai bawa Gwamnati damar amfani da hakan ta cimma muradinta akan 'yan'uwa. Daman kullum burinta ta hadamu fada da Al'umar Gari, sannan ta hadamu fada a tsakaninmu, ta haddasa jayayya da gaba a tsakaninmu. Daga nan shikenan taci nasara akanmu.

 Manzon Allah ya ce "Jayayya tana cire Soyayya ne da qaunar juna"

 Mazon Allah ya hanemu da Jayayya don tana haddasa gaba ne, ta cire jinqai da soyayya.

 Kunga kenan ya kamata mu lura a yanayin da muke ciki. Kada mu bawa Gwamnati damar raba kanmu.

 Daga qarshe zan nusar damu cewa ita wannan Harka din su Sayyid Zakzaky (H) sun fada cewa, muba taron harigido bane ba, muna da tsari.

 Kaga kenan ya Kai Dan'uwa ya kamata mu yi riqo da tsarinnan kamar yadda su Sayyid suka ce muba taron harigido bane ba.

 Misali a bisa tsarin Harka dinnan, ta bangaren Ittihadu bai Hallasta ka yiwa kowa waqa ba, sai A'imma da Sayyid Zakzaky (H) kawai. 

 An fitar da tsarin ne, inka lura sosai sabida a kaucewa tarkon Gwamnati kada a bata damar raba kanmu. Da ace babu wannan tsarin da kaji wani ya yi waqa ma wani, sannan tuni za a samu wani ma ya yiwa wani. Shikenan daga nan farraqa ta samu. Amman Kuma alhamdulillah 'yan Ittihadu suna iya qoqarinsu akan haka basa waqa sai ga Ahlulbaiti ko su Sayyid Zakzaky (H).

 Kai hattama Fostar su Sayyid Zakzaky (H) akwai kwamiti mai kula da Fitowar Foster din, ta yanda daga ciki ana kula da yanayinta da kuma mi aka rubuta a jiki. Ba haka kawai ake buga Foster din su Sayyid ba. Don kaucewa fadawa tarkon Gwamnati.

 Ya kamata 'yan'uwa su dena biyewa son zuciya, ta yanda zai zama sun dena yin gaban kansu. Sabida sau tari yin gabankai yana harfar da matsala ne! Mu tuna da yaqin Uhud, kau cewa tsari ne ya jawo babbar matsala.

 Sannan kuma wanda ya yi ba dai-dai ba, ya aikata kuskure a rinqa amfani da lafasi mai kyau wajen yin tunasarwa. Don haka Allah yace muyi.

 Allah ya ce "Ud'uu ila sabili rabbika bil hikimati wal mau'izatul hasana" Fassara "Ka yi kira zuwa ga hanyar ubangijinka da hikima da wa'azi Mai kyau"

Mu rinqa amfani da lafuza masu kyau ga Yan'uwanmu, mu rinqa tunawa da tarkunan makiyanmu a kanmu na son wargazamu kada mu basu dama "please"👏👏👏👏👏.

 Allah yasa mudace wannan tunasarwa ce! In anga kuskure daga gareni ne, a yi hakuri. Sannan a nusar Dani.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post