Yana Da Kyau Muba Al'amarin Ashura Muhimmanci,

 


Da Sunan Allah Wanda Yayi Alkawarin Wanzar da Gaskiya Da Kuma Ruguza Karya Komi Karfi Da Yawan Mabiyan ta,


Tsira da Aminci Su Tabbata Ga Annabin da yafi kowa Jarabtuwa a Cikin Dukkan Halittu,Tare da Alayen sa Tsarkakakku,


Kamar yadda Yan Uwa suka sani cewa wannan wata ne Mai Cike da al'amarin bakin ciki da Nuna damuwa da Tsananta Nuna Goyon Baya ga imam Husaini,Tare da Nuna Kiyayya da gaaba Mai Tsanani Ga Makasan Imam Husaini da Mabiyan su da masu son su ta kowacce Hanya,tare da Wadanda Suka karanta Ko Suka Saurara Kuma suka yadda suka amince al'amarin ya Shura Yafaru Kuma Gaskiya ne Amma Basu nuna damuwa Kuma basu kokaba,bil Hasalima suna kallon rashin aikin yi ko kallon Banza ga masu Nuna Goyon Baya da alhini da Nuna bakin ciki da damuwar abinda yasami Zuriyar Manzon Tsira{s.a.w.w}


Al'amarin Ashura a bayyane yake,


Al'amarin Ashura ma'auni ne na banbance Mutum da dabba,


Al'amarin Ashura ma'auni ne na Banbance Mai Hankali da Mahaukaci,


Amma Hukuncin Zai Shafi Wadanda Suka Sani Ne,


Saboda ba abin Mamaki bane asami wanda/Wadanda labarin Imam Husain Bai Kai musu ba,


Mu Dauki Magana Daya Muyi amfani da ita Saboda Mu Fahimci Wadancan Maganganun    Nacewa al'amarin Ashura ma'auni ne na banbance Mutum da dabba,Sannan ma'auni ne na banbance Mai Hankali da Mahaukaci,


Akwai Masu Cewa Neman Mulki Imam Husaini Ya Fito Wanda Hakan Yayi Sanadiyyar Ajalin Sa Ta Hanyar Kisa Da Raba Kai da Gangar Jiki,


Miye/Minene Ma'anar Mulki???????


Ma'anar Mulki Shine Kanemi Wani Matsayi a Wurin Mutane Don Mulkar Su,Hakan Zai Iya Kasancewa da ganin daama ko son Ranka,ko yazama da Umarni ko Shawara ko Goyon Bayan Wasu,


To Mi Imam Husaini Zaiyi da Matsayin Mulkar Jama'a??????


Imam Husaini Dan Sayyida Fatima Zahra Ne,Matar Imam Ali Dan Uwan Manzon Allah {s.a.w.w}Ita Kuma Sayyida Fatima Zahra Yar Manzon Allah ce,To Mutumin Dayake Da Wannan Mahaifiya  Wannan Mahaifi da Wannan Kaka Mi Zaiyi da matsayi na Mulkar Jama'a,?????


Imam Husaini Jagora ne,Shugaba ne,Wasiyyi ne Kuma Khalifa ne a Cikin Khalifofin da Manzon Allah yabar Mana Su Fassara Mana AL-Qur'ani Su Fada Mana Maganganu da ayyukan kakan Su Annabi Muhammad {s.a.w.w} Sannan Su Koyar Damu addini Ingantacce,


Shi Yasa a daidai lokacin da Imam Husaini Yaga Ana Wasa,Wargi,Anbar Umarni da kyakkyawa Anbar Hani Ga Mummuna Sai Yayi Kokarin Sauyi da kawo Gyara,


Shiyasa Ba Mulki Imam Husain Ya Nema Ba,Kawo Sauyi da kawo Gyara  Cikin Al'amarin Addinin Asali Na Annabi Muhammad {s.a.w.w}Yayi,


Saboda Haka Yanada Kyau Musan Yadda Zamu Zama a Cikin Gidajen Mu,


Cikin Makarantun Da Muke Karatun Boko Tun Daga Primary Har Jamio'i


Wurin Sana'ar Mu,


Da Kuma Uwa Uba Wuraren Zaman Makokin Mu Na Imam Husain {a.s}


Bai Kamata Kabari Yaron ka Ya Kunna Kallon Wata Tasha ba Muddin ba akan Imam Husain a.s ake magana ba,Bai Kamata Kabada Labarin Da Yaaran Ka Zasu Saami Farin Ciki Suyi Nishadi Har Takai ga Sun Kyalkyata dariya ba,A Rage Yawan Ciye~Ciye da Shaye~Shaye Masu Dadi Ko Dafa abinci Masu Dadi,Saboda Hakan Zaisa Mutum Ya Rika Tunawa Da Halin dasu Imam Husain Suka Saami Kan Su,Mu Yawaita Sanya Bakaken Kaaya Don Alamta Bakin Ciki da alhini da daamuwa,Kada Mu Saki Fuska Ga Makiya Imam Husain,Yanada Kyau Bayan Yadda Abin Yake a Zuciyar Mu Kuma Mu Nuna Musu a Fuska Muna Cikin Bakin Ciki da alhini da daamuwa,


Yanada kyau mu Yawaita Sadakar Abinci Da Ruwan Sha Saboda Duk Wanda Yaci Ko Yasha Allah Zai Sabunta Tsinuwa da la'anta da Wadanda Suka Hana su  Imam Husain Ruwa Yasha,Suka Hanasu Abinci,Suka Cire Kayan Su Mazan Su Da Matan Su,Sannan Suka Azabtar Dasu


Innalillaahi Wa'inna Ilaihi Raji'un



Daga Group Din المؤمنون والمؤمنات Na WhatsApp Da Facebook,


Abdullahi Ibraheem Isah Dabai,


+2347036969346


Tuesday,10th August 2021=02/01/1443,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post