بسم الله الرحمن الرحيم.
Amincin Allah ya tabbata a gareku ya malamin mu mai girma.
Babban malami: MALLAM IBRAHIM ZAKZAKY- mujahidi mai kishin musulunci da karama da mutuntaka, mai kwadayin samar da yanci da qiyma da darajar dan-adam, AMINCIN ALLAH YA QARA TABBATA A GAREKU DA RAHAMAR SA DA ALBARKARSA.
tabbas ranar da kuka fito daga kurkukun zalunci ta cancanci ta kasance ranar farin-ciki ga muminai,-da kuma duk wanda yake ganin girman kokarin ku da kuke yi wajen taimakawa yanci da gyara yan-uwantaka a tsakanin mutane, kuma yake kokarin bayyana gaskiya da kawo adalci, kuma yaqi yarda a zalunce shi ko a zalunci mabiyan sa ko a zalunci kowa,shidai kawai yana son izzah da karama da yanci ga kowa, saboda haka ne ma yake fada da zalunci iyakar iyawar sa.
Ina taya ku murna akan kokarin ku da kuma hakurin ku akan cutarwa da ake yi muku akan tafarkin Allah, da kuma kunyata azzalumai, sakamakon kubuta da kuka samu daga duk abin da azzalumai suka yi kokarin jingina maku na abin da baku ji ba baku gani ba.
muna gode wa duk wanda ya taimaka muku a cikin musulmi da wanda ba musulmi ba, saboda yarda da kokarin ku wajen kare darajar mutum.
Allah ya Karo maku yawan lafiya Kai da matar ka, kuma Allah ya kewaye ku da kulawar sa,da rahamar sa, tare da kuke ganin girman sa, da dukkanin muminai maza da mata, Allah ya sanya kowanen ku cikin shingen sa da ya katange,inda yake sanya wanda yake so.
( AYATULLAH SHEIKH)
ISA AHMAD QASIM.
QUM
LITININ 22 ZUL HAJ.1442.
TARJAMAR:
Dr. Muhammad Sani Haruna kafin hausa.