@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RANAR GHADEEE CE MAFI GIRMAN IDI CIKIN AL'UMMAR ANNABI (S.A.W.W)
Mafi shahara kuma mafi girman ranar da Annabi (S.A.W.W) ya tabbatarwa al'ummarsa jagoransu kuma mai shiryar dasu a bayansa ita ce ranar Ghadeer, domin ranar da ya buqaci su ba shi abin rubutu ya rubuta musu a rubuce abinda matuqar sunyi riqo dashi a bayansa ba za su bata ba sai Umar ya hana tare da zarginsa kan abinda zai rubuta.
Ba tare da zurfafawa ba za mu kawo wasu riwayoyi don tabbatar da wannan magana tawa.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
الأمالي للصدوق ابْنُ السَّعِيدِ الْهَاشِمِيِّ عَنْ فُرَاتٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ ظَهِيرٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ الْفَضْلِ عَنِ الصَّادِقِ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص يَوْمُ غَدِيرِ خُمٍّ
أَفْضَلُ أَعْيَادِ أُمَّتِي وَ هُوَ الْيَوْمُ الَّذِي أَمَرَنِيَ اللَّهُ تَعَالَى ذِكْرُهُ فِيهِ بِنَصْبِ أَخِي عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ عَلَماً لِأُمَّتِي يَهْتَدُونَ بِهِ مِنْ بَعْدِي وَ هُوَ الْيَوْمُ الَّذِي أَكْمَلَ اللَّهُ فِيهِ الدِّينَ وَ أَتَمَّ عَلَى أُمَّتِي فِيهِ النِّعْمَةَ وَ رَضِيَ لَهُمُ الْإِسْلَامَ دِيناً ثُمَّ قَالَ ص مَعَاشِرَ النَّاسِ إِنَّ عَلِيّاً مِنِّي وَ أَنَا مِنْ عَلِيٍّ خُلِقَ مِنْ طِينَتِي وَ هُوَ إِمَامُ الْخَلْقِ بَعْدِي يُبَيِّنُ لَهُمْ مَا اخْتَلَفُوا فِيهِ مِنْ سُنَّتِي وَ هُوَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ وَ قَائِدُ الْغُرِّ الْمُحَجَّلِينَ وَ يَعْسُوبُ الْمُؤْمِنِينَ وَ خَيْرُ الْوَصِيِّينَ وَ زَوْجُ سَيِّدَةِ نِسَاءِ الْعَالَمِينَ وَ أَبُو الْأَئِمَّةِ الْمَهْدِيِّينَ مَعَاشِرَ النَّاسِ مَنْ أَحَبَّ عَلِيّاً أَحْبَبْتُهُ وَ مَنْ أَبْغَضَ عَلِيّاً أَبْغَضْتُهُ وَ مَنْ وَصَلَ عَلِيّاً وَصَلْتُهُ وَ مَنْ قَطَعَ عَلِيّاً قَطَعْتُهُ وَ مَنْ جَفَا عَلِيّاً جَفَوْتُهُ وَ مَنْ وَالَى عَلِيّاً وَالَيْتُهُ وَ مَنْ عَادَى عَلِيّاً عَادَيْتُهُ مَعَاشِرَ النَّاسِ أَنَا مَدِينَةُ الْحِكْمَةِ وَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ بَابُهَا وَ لَنْ تُؤْتَى الْمَدِينَةُ إِلَّا مِنْ قِبَلِ الْبَابِ وَ كَذَبَ مَنْ زَعَمَ أَنَّهُ يُحِبُّنِي وَ يُبْغِضُ عَلِيّاً مَعَاشِرَ النَّاسِ وَ الَّذِي بَعَثَنِي بِالنُّبُوَّةِ وَ اصْطَفَانِي عَلَى جَمِيعِ الْبَرِيَّةِ مَا نَصَبْتُ عَلِيّاً عَلَماً لِأُمَّتِي فِي الْأَرْضِ حَتَّى نَوَّهَ اللَّهُ بِاسْمِهِ فِي سَمَاوَاتِهِ وَ أَوْجَبَ وَلَايَتَهُ عَلَى مَلَائِكَتِهِ.
Ya zo cikin Amali na Sudduq Ibn Sa'eed Al-Hashimiy, daga Furaata, daga Muhammad Bn Zaheeri, daga Abdullahi Bn Fadl, daga Imam Sadiq, daga iyayensa (A.S) yace: Manzon Allah (S.A.W.W) ya fada ranar Ghadeer Khum (cewa);
" MAFIFICIN RANAR IDIN AL'UMMATA ITA CE RANAR DA WANDA AMBATONSA YA 'DAUKAKA YA UMARCE NI DANA NASABTA 'DAN'UWANA ALIYU BN ABIY 'DALIB TUTA GA AL'UMMATA, ZASU SHIRIYA DASHI A BAYANA , KUMA ITA CE RANAR DA ALLAH YA KAMMALA ADDINI A CIKINTA, KUMA YA CIKA AKAN AL'UMMATA NI'IMA, KUMA YA YARDAR MUSU DA MUSLIMCI ADDINI. "
Sa'an nan (S.A.W.W) yace;
" YAA KU TARON MUTANE ! LALLE ALIYU DAGA GARE NI YAKE KUMA NIMA DAGA ALIYU NAKE, AN HALICCE SHI DAGA LAKA TA CE, KUMA SHINE SHUGABAN HALITTU A BAYANA. ZAI BAYYANA MUSU ABINDA SUKA YI SABANI CIKINSA DAGA SUNNATA, KUMA SHINE SHUGABAN MUMINAI KUMA JAGORAN DUKKAN MASU SUJADAH, KUMA ABIN RIQON MUMINAI, KUMA MAFI ALKHAIRIN WASIYYAI, KUMA MIJIN SHUGABAR MATAN TALIKAI, KUMA BABAN JAGORORI MASU SHIRYARWA.
YAA KU TARON MUTANE ! DUK WANDA YAKE SON ALIYU ZAN SO SHI, KUMA WANDA YA QI ALIYU ZAN QI SHI, KUMA WANDA YA SADARWA ALIYU ZAN SADAR MASA, KUMA WANDA YA YANKE ALIYU ZAN YANKE SHI, KUMA WANDA YA WULAQANTA ALIYU ZAN WULAQANTA SHI, KUMA WANDA YA JIBINCI ALIYU ZAN JIBINCE SHI, KUMA WANDA YAYI GABA DA ALIYU ZANYI GABA DA SHI.
YAA KU TARON MUTANE ! NINE BIRNIN HIKIMA KUMA ALIYU BN ABIY 'DALIB QOFARTA, KUMA BA A ZUWA GA BIRNI SAI TA QOFARSA . DUK WANDA KE RIWAYA YANA SONA SANNAN KUMA YANA QIN ALIYU.
YAA KU TARON MUTANE ! NA RANTSE DA WANDA YA AIKO NI DA ANNABTA, KUMA YA ZABE NI AKAN DUKKAN MUTANEN KIRKI, BAN NASABTA ALIYU TUTA GA AL'UMMATA BA CIKIN QASA HAR SAIDA ALLAH YA WATSA SUNANSA CIKIN SAMMAI, KUMA YA WAJABTA WILAYARSA GA MALA'IKU !"
( أمالي الصدوق: 76 و 77 )
Idan kuma muka koma ga riwayar Sunnah sai muyi amfani da wannan aya kadai a matsayin misali. Ga ta kamar haka;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
" وَيَقُولُ الَّذِينَ كَفَرُواْ لَوْلا أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَةٌ مِّن رَّبِّهِ إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرٌ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ ."
" KUMA WADANDA SUKA KAFIRTA SUNA CEWA; " DON MENENE BA A SAUKA MASA DA AYA A KANSA BA DAGA UBANGIJINSA ? " ABIN SANI KAI MAI GARGADI NE, KUMA KOWACCE AL'UMMA AKWAI MAI SHIRYAR DA ITA ."
(SURATUL-RA'AD, AYA TA 7)
To, sai aka sami riwaya ingantacciya cikin riwayoyin Sunnah dangane da Tafsirin wannan aya kamar haka;
وقال أبو جعفر بن جرير حدثني أحمد بن يحيى الصوفي حدثنا الحسن بن الحسين الأنصاري حدثنا معاذ بن مسلم بياع الهروي عن عطاء بن السائب عن سعيد بن جبيرعن ابن عباس رضي الله عنهما قال لما نزلت « إنما أنت منذر ولكل قوم هاد » قال وضع رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم يده على صدره وقال أنا المنذر ولكل قوم هاد وأومأ بيده إلى منكب علي فقال أنت الهادي يا علي بك يهتدي المهتدون من بعدي."
Abu Ja'afar Ibn Jareer yace: Ahmad Bn Yahya ya bamu labari, Hassan Bn Hussaini Al-Ansari ya bamu labari, Mu'azu Bn Muslim Biya'i Al-Harwiy ya bamu labari daga Ada'i Bn Sa'ibi, daga Sa'eed Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R.A) yace:
" Yayin da aka saukar; " ABIN SANI KAI MAI GARGADI NE, KUMA GA KOWACCE JAMA'A AKWAI MAI SHIRYAR DA ITA." Yace:
" Annabi (S.A.W.W) ya dora hannunsa akan qirjinsa yace; " NINE MAI GARGADI, KUMA GA KOWACCE JAMA'A AKWAI MAI SHIRYAR DA ITA."
Sai yayi nuni da hannunsa zuwa kafadar Aliyu, sannan yace:
" KAINE MAI SHIRYARWA YAA ALIYU ! DA KAINE MASU SHIRIYA ZASU SHIRYU A BAYANA ."
(TAFSIR NA IBN KATHEER, SURATUL-RA'AD, AYA TA 7)
Kenan duk wanda ya riqi wani ba Imam Aliyu (A.S) ba a bayan Annabi (S.A.W.W) batacce ne, domin bai riqi mai shiryarwa a bayan Manzon Allah (S.A.W.W) ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th August, 2021/ 25th Zul-Hijjah, 1442.