Gareku Sister: Fitar Da Tsaraici Da Mai Da Kanki A Araha Bazai Jawo Miki Kowa Ba Sai Ƙattin Banza


 Fitar Da Tsaraici Da Mai Da Kanki Araha (Kowa Na Kulaki) Bazai Jawo miki Kowa Ba Sai Ƙattin Banza(Ƴan wasting time). Kunyar Mace baya Tauye mata komai cikin Kamalarta, Kai kara mata kyau yake da tsada,

 Ta yadda Matsiyaci bazai iya Taya Farashinta ba.

Dan haka Ƴar Uwatah kiji Tsoron Allah,

 Kunya da kamewa shine Sifofin Tsadarki wajen Mutanen kirki.Annabi Shu'aibu(Mahaifinta) Ya Tarbiyantar Da ya'yansa Kunya,

 Sai Allah Ta'ala Ya Karrama shi ya kuma Karrama Ya'yansa,

 Ya Kawo Musu Annabi Musa (A S) a matsayin siriki ya musu kiwon Dabbobi a matsayin sadaki.MEYE ABU MAFI TSADA GAME DA MACE??

Na jima ina Nazari dan in Gano "Me Annabi Musa yaga a Jikin Budurwar nan ta Madyana, Har ya yadda yai Shekara 10 yana aiki a Matsayin Sadakinta??

Sidi Abba Aliyu 

22 August, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post