@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ALLAH KAN JARRABCI BAYINSA MUMINAI NE DON YA BASU LADA BA TARE DA ZUNUBI B
Sunnar Allah ba ta canzawa, kamar yadda wasu daga cikin Sahabban Annabi (S.A.W.W) suka zarge shi da cewa ya kai su guraren halaka (yaqoqi) aka karkashe su, alhali yana da damar kaucewa wannan yaqoqi ta hanyar yin sulhu da kafirai hakama wasu na baya suka zargi Imam Hussaini (A.S) da cewa shi ya kai kansa ga halaka a yaqin Karbala.
Abin bai tsaya kansu ba har zuwa kan wasu na wannan zamani suna ganin laifinsa da cewa ai wasu daga manyan Sahabbai sun ba shi shawari kan cewa ya kaucewa wannan tafiya tasa ta zuwa Iraqi.
Wannan tunani nasu ya ba su dama ta ganin wai shi bai bi sunnar dan'uwansa Imam Hassan (A.S) ta yin maslaha ba, har ma suna tuhuma da cewa wannene cikinsu yayi daidai ?
Tafiyar tayi nisa har takai wasu na ganin cewa in har kaga an yiwa mutum wani abu wanda ake ganinsa a matsayin zalunci shi ya jawowa kansa. Har suka zargi Sayyid Zakzaky (H) da almajiransa da cewa su suka jawo akayi musu abinda akayi na zalunci a Zaria. Yanzu kuma irin wannan zargin suke yiwa Sheikh Abdul-Jabbar da cewa shi ya jawowa kansa wannan abinda ya same shi, basu san cewa haka Sunnar Allah take ba.
Za mu leqa cikin wata riwaya don muga cewa shin, duk wani abinda ya sami mutum na musiba sakamakon aikinsa ne? Ga riwayar kamar haka;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
معاني الأخبار أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ عِيسَى عَنِ ابْنِ مَحْبُوبٍ عَنِ ابْنِ رِئَابٍ قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع عَنْ قَوْلِ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ- وَ ما أَصابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِما كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَ يَعْفُوا عَنْ كَثِيرٍ أَ رَأَيْتَ مَا أَصَابَ عَلِيّاً وَ أَهْلَ بَيْتِهِ هُوَ بِمَا
كَسَبَتْ أَيْدِيهِمْ وَ هُمْ أَهْلُ بَيْتِ طَهَارَةٍ مَعْصُومُونَ فَقَالَ إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ ص كَانَ يَتُوبُ إِلَى اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ وَ يَسْتَغْفِرُهُ فِي كُلِّ يَوْمٍ وَ لَيْلَةٍ مِائَةَ مَرَّةٍ مِنْ غَيْرِ ذَنْبٍ إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَخُصُّ أَوْلِيَاءَهُ بِالْمَصَائِبِ لِيَأْجُرَهُمْ عَلَيْهَا مِنْ غَيْرِ ذَنْبٍ[5].
Ya zo cikin Ma'ani Akhbaar, daga Sa'eed, daga Ibn Isah, daga Ibn Mahbuub, daga Ibn Ri'ab yace: Na tambayi Abu Abdullah (A.S) dangane da fadin Allah mai girma da daukaka;
" KUMA ABINDA YA SAME KU NA MUSIBA SAKAMAKON ABINDA HANNAYENKU SUKA AIKATA NE, KUMA YANA YIN YAFIYA GA ABUBUWA MASU YAWA."
' Kana ganin abinda ya sami Aliyu da Iyalan gidansa (A.S) sakamakon abinda hannayensu suka aikata ne, alhali sune Iyalan gida tsarkakakku katangaggu (daga aikata sabo) ?
Sai yace:
" LALLE MANZON ALLAH (S.A.W.W) YA KASANCE YANA TUBA ZUWA GA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA KUMA YANA NEMAN GAFARARSA CIKIN KOWANNE YINI DA DARE SAU 'DARI (100) BA TARE DA YA AIKATA ZUNUBI BA. LALLE ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YANA KEBANCE MASOYANSA DA WATA MUSIBA (mummuniyar jarrabawa) DOMIN YA BASU LADA A KANTA BA TARE DA ZUNUBI BA."
معاني الأخبار ص 383 و 384.
Wannan hadisi na karantar damu ne cewa ashe ba aikin zunubi ko laifi bane ke sa kaga ana cutar da wani bawan Allah ko bayin Allah, sai dai kawai jarrabawa daga Allah wacce yake yi a kansu don yayi musu sakayya da mafificiyar lada.
Shi yasa muka ga an cutar da Manzon Allah (S.A.W.W) a zamaninsa ba tare da yin wani laifi ko rashin iya wa'azi ba, kuma aka cutar da Iyalan gidansa (A.S) ba tare da su suka jawowa kansu ba.
Sanin wannan ma'ana tasa Imam Aliyu Zainul-Abideen ya kawo wadannan ayayi gaban Yazeed (L.A) yayin da aka kaisu Fadarsa.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
مَآ أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ أَن نَّبۡرَأَهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ ٢٢ لِّكَيۡلَا تَأۡسَوۡاْ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمۡ وَلَا تَفۡرَحُواْ بِمَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخۡتَالٖ فَخُورٍ (٣٢)
" BABU WATA MUSIBA DAKE AUKUWA CIKIN QASA KO KUMA CIKIN KAWUKANKU FACE YANA NAN CIKIN LITTAFI (rubuce) KAFIN A BAYYANAR DA ITA. WANNAN KUWA MAI SAUQI NE AGUN ALLAH.
(Yana yin hakanne gare ku) " DON KADA KUYI BAQIN CIKI BISA ABINDA YA KUBUCE MUKU (na haqqoqinku), KUMA KADA (ku fajirai) KUYI FARIN CIKI NA DAGA ABINDA AKA BAKU (na mulki ko dukiya), KUMA ALLAH BA YA SON KOWANNE MAI GIRMAN KAI MAI ALFAHARI."
(Suratul-Hadid:22-23)
Amma da shike Yazeed (L.A) fajiri ne mujrimi azzalumi maimakon jikinsa yayi sanyi ya sallama sai ya maida martani gare shi da wannan aya wacce ke nuna cewa farin ciki yake yi da abinda ya faru ga iyalan gidan Annabi (A.S). Yake cewa;
وَمَآ أَصَٰبَكُم مِّن مُّصِيبَةٖ فَبِمَا كَسَبَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَيَعۡفُواْ عَن كَثِيرٖ ٠٣
" KUMA ABINDA YA SAME KU NA MUSIBA SAKAMAKON ABINDA HANNAYENKU SUKA AIKATA NE, KUMA (Allah) NA YIN YAFIYA GA (wasu laifuffuka) MASU DAMA."
(Suratul-Shurah:30)
Saboda haka idan kaji wani na cewa abinda ya sami wane (mumini) laifinsa ne, to, wannan jinin gidan Umayyawa ne masu son daukar fansar jinanan da aka sheqar na iyayensu a yaqoqi na Badr da Uhud d.s.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
24th August, 2021/ 16th Muharram, 1443.