Sakon Sahabi Abubakar (Ra) Zuwa Ga Usama Bayan Yayi Qwacen Jagoranci !!!

 



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


RADDIN DA USAMATA BN ZAID YA YIWA IBN QUHAFATA


Kamar dai yadda aka sani ne mafi yawan Sahabbai sun juyawa Annabi (S.A.W.W) baya game da jagorancin da ya nada musu suka dora abinda zuciyarsu ta riya musu, to, an sami misayar yawu tsakanin Abubakar da Usamatu Bn Zaid.


Ga yadda abin ya kasance 


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


رُوِيَ عَنِ الْبَاقِرِ عَلَيْهِ السَّلَامُ: أَنَّ عُمَرَ بْنَ الْخَطَّابِ قَالَ لِأَبِي بَكْرٍ: اكْتُبْ إِلَى أُسَامَةَ يَقْدَمُ عَلَيْكَ، فَإِنَّ فِي قُدُومِهِ قَطْعُ الشُّنْعَةِ عَنَّا.


An riwaito daga Baqir (A.S) cewa; Lalle Umar Bn Khaddab ya cewa Abubakar: " Ka rubuta zuwa ga Usamatu yazo gare ka, domin zuwan nasa shi zai yanke abinda aka aikata a kanmu."


فَكَتَبَ أَبُو بَكْرٍ إِلَيْهِ: مِنْ أَبِي بِكْرٍ خَلِيفَةِ رَسُولِ اللَّهِ إِلَى أُسَامَةَ بْنِ زَيْدٍ، أَمَّا بَعْدُ: فَانْظُرْ إِذَا أَتَاكَ كِتَابِي فَأَقْبِلْ إِلَيَّ أَنْتَ وَ مَنْ مَعَكَ، فَإِنَّ الْمُسْلِمِينَ قَدِ اجْتَمَعُوا [عَلَيَ‏] وَ وَلَّوْنِي أَمْرَهُمْ، فَلَا تَتَخَلَّفَنَّ فَتَعْصِيَ وَ يَأْتِيَكَ مِنِّي مَا تَكْرَهُ، وَ السَّلَامُ.


Sai Abubakar ya rubuta zuwa gare shi: " Daga Abubakar Khalifan Manzon Allah (S.A.W.W) zuwa ga Usamata Bn Zaid, bayan haka: Ka duba yayin da rubutuna yazo maka, kazo gare ni kai da wadanda ke tare dakai. Domin musulmai sun taru a kaina sun dora min al'amarinsu, (saboda haka) kada ka saba sai kayi sabo (sin) kuma abinda ba ka so yazo maka daga gare ni, da aminci ."


قَالَ: فَكَتَبَ إِلَيْهِ أُسَامَةُ جَوَابَ كِتَابِهِ: مِنْ أُسَامَةَ بْنِ زَيْدٍ عَامِلِ رَسُولِ اللَّهِ (ص) عَلَى غَزْوَةِ الشَّامِ، أَمَّا بَعْدُ، فَقَدْ أَتَانِي [مِنْكَ‏] كِتَابٌ يَنْقُضُ أَوَّلُهُ آخِرَهُ‏ ذَكَرْتَ فِي أَوَّلِهِ أَنَّكَ خَلِيفَةُ رَسُولِ اللَّهِ، وَ ذَكَرْتَ فِي آخِرِهِ أَنَّ الْمُسْلِمِينَ اجْتَمَعُوا عَلَيْكَ فَوَلَّوْكَ أُمُورَهُمْ وَ رَضُوا بِكَ‏ وَ اعْلَمْ، أَنِّي وَ مَنْ‏ مَعِي مِنْ جَمَاعَةِ الْمُسْلِمِينَ وَ الْمُهَاجِرِينَ، فَلَا وَ اللَّهِ مَا رَضِينَا بِكَ‏ وَ لَا وَلَّيْنَاكَ أَمْرَنَا، وَ انْظُرْ أَنْ تَدْفَعَ الْحَقَّ إِلَى أَهْلِهِ، وَ تُخَلِّيَهُمْ 

وَ إِيَّاهُ، فَإِنَّهُمْ أَحَقُّ بِهِ مِنْكَ.

فَقَدْ عَلِمْتَ مَا كَانَ مِنْ قَوْلِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ فِي عَلِيٍّ عَلَيْهِ السَّلَامُ يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍ‏، فَمَا طَالَ الْعَهْدُ فَتَنْسَى.


انْظُرْ بِمَرْكَزِكَ، وَ لَا تُخَلِّفْ‏ فَتَعْصِيَ اللَّهَ وَ رَسُولَهُ وَ تَعْصِيَ [مَنِ‏] اسْتَخْلَفَهُ رَسُولُ اللَّهِ 

صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ عَلَيْكَ وَ عَلَى صَاحِبِكَ، وَ لَمْ 

يَعْزِلْنِي حَتَّى قُبِضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ، وَ أَنَّكَ وَ صَاحِبَكَ رَجَعْتُمَا وَ عَصَيْتُمَا، فَأَقَمْتُمَا فِي الْمَدِينَةِ بِغَيْرِ إِذْنِي‏.


Yace: Sai Usamata ya rubuta masa amsar rubutunsa. 


" Daga Usamata Bn Zaid ma'aikacin Manzon Allah (S.A.W.W) a yaqin Shaam, bayan haka. Haqiqa rubutu daga gare ka ya zo min wanda farkonsa ke warware qarshensa (saboda rashin hikima) . A farko ka ambaci cewa kai Halifan Manzon Allah (S.A.W.W) ne, sannan a qarshe kace ka ambaci cewa mutanene suka taru a kanka suka dora maka al'amarinsu (jagorancinsu) kuma suka yarje maka. To, ka sani, lalle ni da jama'ar musulmai da Muhajirai, to, wallahi bamu yarje maka ba (kan wannan matsayi da ba naka ba), kuma ba za mu miqa maka al'amarinmu ba. Ka duba ka mayar da haqqi zuwa ga mai shi, kuma ka tubu jagorancinsu da kuma shi, domin su suke da haqqinsa a kanka.


Haqiqa kana sane cewa da maganar Manzon Allah (S.A.W.W) game da Aliyu (A.S) ranar Ghadeer Khum, wannan alqawari baiyi nisa ba ballantana ka manta !


Kayi dubi da matsayinka (na babba a shekaru), kada ka saba (wannan alqawari) har ka sabawa Allah da Manzonsa (S.A.W.W), kuma ka sabawa wanda Manzon Allah (S.A.W.W) ya Halifantar dashi a kanka da kuma abokanka, kuma ni ban gushe ba har aka karbi ran Manzon Allah (S.A.W.W), kuma kai da abokanka kuna kwadayin (wannan matsayi) kuma kuna sabawa (Manzon Allah), ku kayi taro a Madinah ba tare da iznina ba."


قَالَ: فَهَمَ‏ أَبُو بَكْرٍ أَنْ يَخْلَعَهَا مِنْ عُنُقِهِ، قَالَ: فَقَالَ لَهُ عُمَرُ: لَا تَفْعَلْ قَمِيصٌ قَمَّصَكَ اللَّهُ لَا تَخْلَعْهُ فَتَنْدَمَ، وَ لَكِنْ أَلِحَّ عَلَى أُسَامَةَ بِالْكُتُبِ، وَ مُرْ فُلَاناً وَ فُلَاناً وَ فُلَاناً يَكْتُبُونَ إِلَى‏ أُسَامَةَ أَنْ لَا يُفَرِّقَ 

جَمَاعَةَ الْمُسْلِمِينَ، وَ أَنْ يُدْخِلَ يَدَهُ‏ فِيمَا صَنَعُوا.


Yace: Sai Abubakar ya himmatu ya tube ta (Halifancin) daga wuyansa . Yace: Sai Umar yace masa;


" Kada ka aikata, rigar da Allah ya sanya maka ita kada ka tube ta sai kayi nadama (daga baya). Sai dai ka juyar da hankalin Usamata ta hanyar rubutu. Ka umarci wane da wane da wane su rubuta zuwa ga Usamata cewa kada ya (fa) ya rabu da jama'ar musulmai , kuma har ya sanya hannunsa cikin abinda suka aikata (na yi maka tawaye)."


قَالَ: فَكَتَبَ إِلَيْهِ أَبُو بَكْرٍ، وَ كَتَبَ إِلَيْهِ أُنَاسٌ‏ مِنَ الْمُنَافِقِينَ: أَنِ ارْضَ بِمَا اجْتَمَعْنَا عَلَيْهِ، وَ إِيَّاكَ أَنْ تُشْمِلَ‏ الْمُسْلِمِينَ فِتْنَةً مِنْ 

قِبَلِكَ، فَإِنَّهُمْ حَدِيثُو عَهْدٍ بِالْكُفْرِ.


Yace: Sai Abubakar ya rubuta zuwa gare shi, kuma mutane daga munafukai suka rubuta zuwa gare shi:


" Ka yarda da abinda muka hadu a kansa, muna haninka kada fitina ta taso daga gare ka  cikin musulmai, domin su sun qirqiro wani alqawari na kafirci."


فَلَمَّا وَرَدَتِ الْكُتُبُ عَلَى أُسَامَةَ انْصَرَفَ بِمَنْ مَعَهُ حَتَّى دَخَلَ الْمَدِينَةَ، فَلَمَّا رَأَى اجْتِمَاعَ النَّاسِ‏ عَلَى أَبِي بَكْرٍ انْطَلَقَ إِلَى عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ فَقَالَ‏: مَا هَذَا؟


Yayin da suka maimaita rubutu zuwa ga Usamata sai ya tafi tare da wadanda ke tare dashi har suka shiga Madinah. Yayin da su kaga mutane sun taru kan Abubakar sai suka tafi zuwa ga Aliyu Bn Abiy 'Dalib yace: " Menene wannan ?"


فَقَالَ لَهُ‏ عَلِيٌّ: هَذَا مَا تَرَى! قَالَ لَهُ أُسَامَةُ: فَهَلْ بَايَعْتَهُ؟


Sai Aliyu yace masa: " WANNAN SHINE ABINDA KA GANI."


Sai Usamata yace masa: " Shin, mubaya'a suka yi masa ?"


فَقَالَ: نَعَمْ.


Yace: " EH !"


فَقَالَ لَهُ أُسَامَةُ: طَائِعاً أَوْ كَارِهاً؟


Sai Usamata yace masa: " Bisa yarda ko bisa dole (tilas) ?"



قَالَ: لَا، بَلْ كَارِهاً قَالَ: فَانْطَلَقَ أُسَامَةُ فَدَخَلَ عَلَى أَبِي بَكْرٍ، فَقَالَ‏: السَّلَامُ عَلَيْكَ يَا خَلِيفَةَ الْمُسْلِمِينَ.


Yace: " A'A, BISA TILASCI !"


Sai Usamata ya tafi ya shiga wajen Abubakar yace; " Aminci ya tabbata a gare ka yaa Halifan musulmai !"


قَالَ: فَرَدَّ أَبُو بَكْرٍ وَ قَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكَ أَيُّهَا الْأَمِيرُ.


Yace, sai Abubakar ya mayar yace:


" Aminci ya tabbata a gare ka yaa kai amintacce ."


(Wato a qarshe shi ma Usamata ya warware akqawarin nasa yayi tarayya da Abubakar alhali har yana qalubantarsa).


(1) الاحتجاج 1- 87 [طبعة النّجف: 1- 114- 115]


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏29، ص: 92-94



Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da Ado Isah Guda.


       (08137925034)


3rd August, 2021/  24th Zul-Hijjah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post