@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MATSALAR MUTUM KAWAI ITA CE IDAN YANA YIWA HARKA ZAGON QASA
Sayyid Zakzaky (H) rahma ce ga al'umma, saboda haka ba zai taba zama fitina ga wani dan Adam ba ballantana mai shaidawa da LA'IHA ILLAL-LAH MUHAMMADAR-RASULULLAH !
A koda yaushe kira yake yi azo a dunqule guri guda a yiwa muslimci aiki ba tare da nuna bambancin fahinta tsakani ba. Za mu iya ganin haka yayin da ya kasance jigo Mu'assasi na shirya makon hadin kai wanda ake yi a watan Rabi'u Awwal na kowacce shekara dake tattara masu bambancin fahintu ko aqidu don kowa ya bada tasa gudumawar wacce za ta amfanar da al'ummar musulmi.
Idan muka gangaro kan mabiya za muga kowanne dan'uwa da irin tasa gudumawar da yake bayarwa don taimakon Harka Islamiyyah, da za ayi rashin sa'a ace an rasa irin wannan bangare da za a sami matsala cikin tafiyar Harkar.
Wani kudi yake dashi kuma yana shirye ya bayar dasu don taimakon Harka, amma ba shi da ishasshen lokaci wanda zai iya bayar dashi wajen halartar komai na Harka kamar yarda wani zai iya bayarwa.
Wani kuma yana da kudi kuma yana da lokaci wanda zai iya yin tarayya da kowa cikin ayyuka ko halartar taruka mabambanta. Irin wannan shine mai cin riba biyu, domin zai iya bada lokaci kuma ya bada dukiyarsa fiye da yadda za ka iya. Irinsu ne aka samu cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W.W) wadanda har wasu suka kai kokensu ga Manzon Allah (S.A.W.W) kan cewa masu hanu da shuni sun tafi da lada, domin suna sallah da azumi kuma sunyi fifiko akan 'yan'uwansu wajen dibar dukiyarsu suna taimakon addinin Allah.
Akwai kuma wasu wadanda suke bayar da ilimi wanda shine jigon tarbiyya da sanin yadda ake bautar Allah ta hanyar bin abinda yayi umarni dashi ko kuma nisantar abinda yayi hani a kansa.
Sannan kuma ana samun wanda yake bayar da duk lokacinsa don yin wani aiki na taimakon Harka, amma kuma idan aka zo bangaren bayarwa (IMFAQI) sai kaga yana baya-baya saboda rashin abinda zai bayar, amma ba wai yana gudun bayarwar bace. Su ma wadannan an sami irinsu a zamanin Annabi (S.A.W.W), domin su suke yin kuka don basu sami abinda za su bayar ba.
Idan muka tattara wadannan misalai dama wadanda muka bari don gudun tsawaitawa sai muga cewa da za a rasa wani bangare daga cikinsu haqiqa da babu inda Harka za ta tafi, domin kowanne na buqatuwa zuwa ga dan'uwansa.
MISALI
_____________
Da ace lokacin da Sayyid (H) ya fara yin kiransa sai aka rasa masu amsa masa, to, da ba'a sami cigaba zuwa wannan lokaci ba, sai dai kawai ace ya sauke nauwin da Allah ya dora masa kamar yadda wasu Manzanni (A.S) su kayi.
Idan kuma aka ce an sami ma'aikata wadanda za suyi wani aiki mai muhimmanci sai kuma aka rasa kayan aiki, to, wannan aiki ba zai yiwu ba. Kamar hakane da za ace an sami kayan aiki sai aka rasa ma'aikata, to, wannan kayan aikin ba zai iya yin aikin ba dole sai an sami ma'aikata.
Saboda haka bai kamata ace wani na ganin gazawar dan'uwansa, kowa kawai ya shagaltu da irin gudumawar da yake iya bayarwa. Sannan kuma muhimmin abu cikin dukkan wadannan misalai shine ya zama cewa kowa na yi ne domin Allah. Amma duk tarin ayyukansa matuqar babu ikhlasi cikinsa ya zama aikin banza.
YAA ALLAH KA TSARE MU DAGA AIKATA WANI AIKI WANDA BA DON KAI MUKA YI SHI BA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
13th August, 2021/ 4th Muharram, 1443.