@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KOYI DA ANNABAWA SHIDA (6) NAYI IN JI IMAM ALI (A.S)
Wannan wata tambaya ce mai daurewar kai ko nace mai wuyar amsawa ga dukkan wanda bai yi zurfin karatu ko bincike ba, domin dukkansu manya ne cikin Sahabban Annabi (S.A.W.W).
Tunanin da ke yawan bijirowa mutane kenan cikin qwaqwalensu a duk lokacin da suka ji cewa Imam Ali (A.S) ya yaqi su Ummul-muminina A'isha cikin tawagar su 'Dalha da Zubair, sannan kuma ya qara yaqar Mu'awiyyah alhali bai yaqi su Abubakar da Umar ba.
Ganin wannan yasa wasu ke ganin ai rashin yaqar na farkon na nuna cewa ya yarda da ayyukansu ne, kan haka ake samun masu tuhumar dukkan wanda ke cewa su Abubakar da Umar basu cikin Khalifofi shiryayyun da aka ce muyi riqo dasu.
Bari mu kawo hujjar da Imam Ali (A.S) ya kafawa wadanda suka yi masa irin wannan tuhuma, wala-Allah ko kaima ka sami amsar bayarwa yayin da wani zai yi maka tambaya kan haka.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
رُوِيَ أَنَّ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ عَلَيْهِ السَّلَامُ كَانَ جَالِساً فِي بَعْضِ مَجَالِسِهِ بَعْدَ رُجُوعِهِ عَنِ النَّهْرَوَانِ فَجَرَى الْكَلَامُ حَتَّى قِيلَ: لِمَ لَا حَارَبْتَ أَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ كَمَا حَارَبْتَ طَلْحَةَ وَ الزُّبَيْرَ وَ مُعَاوِيَةَ؟. فَقَالَ
عَلَيْهِ السَّلَامُ: إِنِّي كُنْتُ لَمْ أَزَلْ مَظْلُوماً مُسْتَأْثَراً عَلَى حَقِّي، فَقَامَ إِلَيْهِ أَشْعَثُ بْنُ قَيْسٍ فَقَالَ: يَا أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ! لِمَ لَمْ تَضْرِبْ بِسَيْفِكَ وَ تَطْلُبْ بِحَقِّكَ؟! فَقَالَ: يَا أَشْعَثُ! قَدْ قُلْتَ قَوْلًا فَاسْمَعِ الْجَوَابَ وَ عِهْ وَ اسْتَشْعِرِ الْحُجَّةَ، إِنَّ لِي أُسْوَةً بِسِتَّةٍ مِنَ الْأَنْبِيَاءِ صَلَوَاتُ اللَّهِ عَلَيْهِمْ أَجْمَعِينَ:
An riwaito cewa Amirul-Muminina ya kasance zaune cikin sashen zama-zamensa bayan dawowarsa daga (yaqin) Nahrawan. Sai maganganu suka gudana har aka ce:
" Don menene ba ka yaqi su Abubakar da Umar ba kamar yadda ka yaqi 'Dalha da Zubair da Mu'awiyyah ?"
Sai Amirul-Muminina (A.S) yace:
" NI BAN GUSHE BA INA MATSAYIN WANDA AKA ZALUNTA KUMA MAI NEMAN TAIMAKO AKAN HAQQINA ."
Sai Ash-Ath Bn Qais ya miqe zuwa gare shi yace : " Yaa kai shugaban muminai ! Me yasa ba kayi sara da Tokobinka ka nemi jaqqinka ba ?"
Sai yace: " YAA ASH-ATH ! HAQIQA KA FADI MAGANA, AMMA KA SAURARI AMSA KUMA KA KIYAYE, HUJJOJI MASU RATSA JIKI.
LALLE NI INA DA ABIN KOYI DAGA ANNABAWA SHIDA (6) (AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SU BAKI 'DAYANSU ).
أَوَّلُهُمْ: نُوحٌ عَلَيْهِ السَّلَامُ حَيْثُ قَالَ: أَنِّي مَغْلُوبٌ فَانْتَصِرْ، فَإِنْ قَالَ قَائِلٌ: إِنَّهُ قَالَ لِغَيْرِ خَوْفٍ فَقَدْ كَفَرَ، وَ إِلَّا فَالْوَصِيُّ أَعْذَرُ.
- (1) القمر: 10، و في المصدر: ربّ إنّي ..
(1)- " Na farkonsu shine Nuhu (A.S) yayin da yake cewa;
" LALLE NI AN RINJAYE NI, KAYI TAIMAKO !"
Idan mai magana yace: Ai Shi ba don tsoro ya fadi wannan magana ba haqiqa ya kafirta. Idan kuwa ba haka ba to, wasiyyi abin yiwa uzuri ne.
وَ ثَانِيهِمْ: لُوطٌ عَلَيْهِ السَّلَامُ حَيْثُ قَالَ: لَوْ أَنَّ لِي بِكُمْ قُوَّةً أَوْ آوِي إِلى رُكْنٍ شَدِيدٍ. فَإِنْ قَالَ قَائِلٌ: إِنَّهُ قَالَ هَذَا لِغَيْرِ خَوْفٍ فَقَدْ كَفَرَ، وَ إِلَّا فَالْوَصِيُّ أَعْذَرُ.
- هود: 80.
(2)- Na biyunsu shine : Lut (A.S) yayin da yace:
" DA DAI ACE NI INA DA WANI QARFI A KANKU, KO KUWA INA DA GOYON BAYA DAGA WANI RUKUNI MAI QARFI?"
Idan mai magana yace, lalle Shi ya fadi hakan ne ba don tsoro ba to, ya kafirta. Idan kuwa hakane to, wasiyyi abin yiwa uzuri ne.
وَ ثَالِثُهُمْ: إِبْرَاهِيمُ خَلِيلُ اللَّهِ حَيْثُ قَالَ: وَ أَعْتَزِلُكُمْ وَ ما تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ. فَإِنْ قَالَ قَائِلٌ: إِنَّهُ قَالَ هَذَا لِغَيْرِ خَوْفٍ فَقَدْ كَفَرَ، وَ إِلَّا فَالْوَصِيُّ أَعْذَرُ.
- مريم: 48.
(3)- Na ukun su shine: Ibrahim Badadanin Allah (A.S) yayin da yace:
" KUMA INA NISANTARKU DAGA ABINDA KUKE KIRA KOMA BAYAN ALLAH."
Idan mai magana yace, ai lalle shi ya fadi wannan ne ba bis tsoro ba, ya kafirta. Idan kuwa ba haka ba, to, wasiyyi abin yiwa uzuri ne.
وَ رَابِعُهُمْ: مُوسَى عَلَيْهِ السَّلَامُ حَيْثُ قَالَ: فَفَرَرْتُ مِنْكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ. فَإِنْ قَالَ قَائِلٌ: إِنَّهُ قَالَ هَذَا لِغَيْرِ خَوْفٍ فَقَدْ كَفَرَ، وَ إِلَّا فَالْوَصِيُّ أَعْذَرُ.
- الشّعراء: 21.
(4)- Na hudunsu : Musa (A.S), yayin da yace:
" SAI NA GUDU DAGA GARE KU YAYIN DA NAJI TSORON KU."
Idan mai magana yayi magana cewa, ai shi ba don tsoro ya fadeta ba ya kafirta, idan kuwa ba haka ba, to, wasiyyi abin yiwa uzuri ne.
وَ خَامِسُهُمْ: أَخُوهُ هَارُونُ عَلَيْهِ السَّلَامُ حَيْثُ قَالَ: ابْنَ أُمَّ إِنَّ الْقَوْمَ اسْتَضْعَفُونِي وَ كادُوا يَقْتُلُونَنِي. فَإِنْ قَالَ قَائِلٌ: إِنَّهُ قَالَ هَذَا لِغَيْرِ خَوْفٍ فَقَدْ كَفَرَ، وَ إِلَّا فَالْوَصِيُّ أَعْذَرُ.
- الأعراف: 150، و في المصدر: يا ابن أم ..
(5)- Na biyar dinsu shine: 'Dan'uwansa Haruna (A.S) yayin da yace;
" YAA 'DAN'UWANA ! LALLE MUTANEN SUN RAUNATA NI, HAR MA SUNYI KUSA SU KASHE NI !"
Idan mai magana yace; " Ai shi ya fadi hakan ne ba don tsoro ba, to, ya kafirta. Idan kuwa ba haka ba, to, wasiyyi abin yiwa uzuri ne.
وَ سَادِسُهُمْ: أَخِي مُحَمَّدٌ سَيِّدُ الْبَشَرِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ حَيْثُ ذَهَبَ إِلَى الْغَارِ وَ نَوَّمَنِي عَلَى فِرَاشِهِ، فَإِنْ قَالَ قَائِلٌ: إِنَّهُ ذَهَبَ إِلَى الْغَارِ لِغَيْرِ خَوْفٍ فَقَدْ كَفَرَ، وَ إِلَّا فَالْوَصِيُّ أَعْذَرُ.
(6)- Na shidansu shine: 'Dan'uwa Muhammad (S.A.W.W) yayin da ya tafi zuwa ga Kogo kuma ya kwantar dani kan shimfidarsa (S.A.W.W).
Idan mai magana yace: Ai shi ya tafi zuwa ga Kogon amma ba don tsoro ba, to, ya kafirta. Idan kuwa ba haka ba, to, wasiyyi shine abin yiwa uzuri.
فَقَامَ إِلَيْهِ النَّاسُ بِأَجْمَعِهِمْ فَقَالُوا: يَا أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ! قَدْ عَلِمْنَا أَنَّ الْقَوْلَ قَوْلُكَ وَ نَحْنُ الْمُذْنِبُونَ التَّائِبُونَ، وَ قَدْ عَذَرَكَ اللَّهُ!.
Daga nan sai mutane suka miqe zuwa gare shi (A.S) baki dayansu suka ce:
" YAA SHUGABAN MUMINAI ! HAQIQA (yanzu) MUN SANI CEWA MAGANA (ta gaskiya) ITA CE MAGANARKA, MU KUMA MASU ZUNUBI NE MASU TUBA. HAQIQA ALLAH YA YIMA UZURI !"
-
- الاحتجاج: 1- 189- 190 طبعة مشهد [1- 279- 280 النّجف الأشرف] باختلاف يسير.
- بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج29، ص: 419
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
8th August, 2021/ 29th Zul-Hijjah, 1442.