Hukuncin Yaron Da Ya Yi Zina Da Mace !



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

WANNE HUKUNCI NE YAHAU KAN YARINYAR DA AKAYI ZINA DA ITA ? 

Bisa tunani za ka iya cewa ai duk yaron da yayi zina da mace ya mallaki hankalin kansa, saboda haka za a iya hukunta shi kamar yadda za a hukunta babba ko kuma dai ayi masa hukunci gwargwadon yadda ya dace don tsoratarwa.

Amma abin nazarin shine, ai shi yaron za a iya lallabarsa don neman biyan buqata, ita kuwa mace bisa son ranta ne za tayi zina da yaro. Saboda haka ga hukuncinsu nan biye cikin hadisi daga Limamin shiriya.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

 قرب الإسناد عَنْ عَلِيٍّ عَنْ أَخِيهِ ع قَالَ: سَأَلْتُهُ عَنْ رَجُلٍ وَقَعَ عَلَى صَبِيَّةٍ مَا عَلَيْهِ قَالَ الْحَدُّ[1] وَ سَأَلْتُهُ عَنْ صَبِيٍّ وَقَعَ عَلَى امْرَأَةٍ قَالَ تُجْلَدُ الْمَرْأَةُ وَ لَيْسَ عَلَى الصَّبِيِّ شَيْ‏ءٌ[2]

Ya zo cikin Qarrabul-Isnaad, daga Aliyu daga dan'uwansa (A.S) yace:

An tambaye shi game da hukuncin mutumin da ya afkawa qaramar yarinya, menene hukuncinsa ? Yace:

" HADDI ."

Kuma aka tambaye shi game da yaron da ya afkawa mace. Yace;

" ZA A YIWA MATAR BULALA, KUMA BABU KOMAI AKAN YARON ."

قرب الإسناد ص 148 و في ط 111

Yadda za muyi sauqin fahintar wannan hukunci shine, babu hukunci kan yaron da bai zama mukallafi ba, wato yaron da bai balagha ba bai mallaki hankalin kansa ba.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

30th August, 2021/ 22nd Muharram, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post