@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SABANI CIKIN KALAR ABUBUWAN DA AKA TSINTA
Ita tsintuwa ita ce dukkan wani abinda ya shigo hannunka ba ta hanyar mallakarsa kamar saye ko sadaqa ko kuma kyautar da wani ya yi ta gareka ba. Duk wani abinda ka same shi a hanya ko kasuwa ko gona ko da kuwa a cikin gidanka ne mutaqar ba naka bane, to, sunansa tsintuwa.
To, idan ya kasance kayi tsintuwar wani abinda ba naka ba, akwai hukuncin da yahau kansa kamar haka:-
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
(1)- قرب الإسناد عَنْهُمَا عَنْ حَنَانٍ قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع عَنِ اللُّقَطَةِ قَالَ
تُعَرِّفُهَا سَنَةً فَإِذَا انْقَضَتْ فَأَنْتَ أَمْلَكُ بِهَا.
Ya zo cikin Qarabul-Isnaad, daga gare su Hanaani yace: Na tambayi Abu Abdullah (A.S) game da tsintuwa, yace;
" ZA AYI CIGIYARTA (na tsahon) SHEKARA (guda), IDAN (shekarar) TA CIKA (ba tare da an sami mai ita ba), TO, KAI KE DA MALLAKINTA."
(2) - ب، قرب الإسناد عَلِيٌّ عَنْ أَخِيهِ ع قَالَ: سَأَلْتُهُ عَنِ اللُّقَطَةِ إِذَا كَانَتْ جَارِيَةً هَلْ
يَحِلُّ فَرْجُهَا لِمَنِ الْتَقَطَهَا قَالَ لَا إِنَّمَا يَحِلُّ لَهُ بَيْعُهَا بِمَا أَنْفَقَ عَلَيْهَا.
Cikin Qarabul-Isnaad, daga Aliyu daga dan'uwansa (A.S) yace: An tambaye shi game da tsintuwa idan ta kasance kuyanga ce (slave), shin farjinta ya halatta ga wanda ya tsince ta? Yace;
" A'A, ABINDA KAWAI YA HALATTA GARE SHI SHINE SAYARWA SABODA ABINDA ZAI CIYAR DA ITA."
(3) - قَالَ: وَ سَأَلْتُهُ عَنِ اللُّقَطَةِ يُصِيبُهَا الرَّجُلُ قَالَ يُعَرِّفُهَا سَنَةً ثُمَّ هِيَ كَسَائِرِ مَالِهِ وَ قَالَ كَانَ عَلِيُّ بْنُ الْحُسَيْنِ ع يَقُولُ لِأَهْلِهِ- لَا تَمَسُّوهَا.
Yace, kuma an tambaye shi game da tsintuwar da wani mutum ya same ta. Yace:
" ZAIYI CIGIYARTA SHEKARA GUDA, SA'AN NAN (idan ba a sami mai ita ba) TA KASANCE KAMAR SAURAN DUKIYARSA CE (yana da ikon yin komai da ita)."
Kuma yace, Aliyu Bn Husaaini (A.S) ya kasance yana fadawa iyalinsa:
" KASA KU SHAFE TA ."
(1) قرب الإسناد ص 58.
(2) قرب الإسناد ص 115.
Cikin wadannan riwayoyi na sama za mu iya fitar da hukunci biyu, wato idan ya kasance kaddara ce aka tsinta ana yin cigiyarta ne tsahon shekara guda, idan ba a sami mai ita ba ta zama mallakin mutum, zai iya yin abinda yaga dama da ita.
Ita kuwa tsintuwar Baiwa/Kuyanga ana iya sayar da ita saboda nauyin ciyar da ita, amma haramun ne a taki farjinta.
A cikin wata riwaya ta gaba kuma wacce ta fitar da wani hukunci sabanin wadanda suka gabata ba tare kuma da cin karo da hukuncinsu ba ita ce kamar haka;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
نَوَادِرُ الرَّاوَنْدِيِّ، بِإِسْنَادِهِ عَنْ مُوسَى بْنِ جَعْفَرٍ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ: سُئِلَ عَلِيٌّ ع عَنْ سُفْرَةٍ وُجِدَتْ فِي الطَّرِيقِ فِيهَا
لَحْمٌ كَثِيرٌ وَ خُبْزٌ كَثِيرٌ وَ بَيْضٌ وَ فِيهَا سِكِّينٌ فَقَالَ يُقَوَّمُ مَا فِيهَا ثُمَّ يُؤْكَلُ لِأَنَّهُ يَفْسُدُ فَإِذَا جَاءَ طَالِبُهَا غُرِمَ لَهُ فَقَالُوا لَهُ يَا أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ- لَا نَعْلَمُ أَ سُفْرَةُ ذِمِّيٍّ أَمْ سُفْرَةُ مَجُوسِيٍّ فَقَالَ هُمْ فِي سَعَةٍ مِنْ أَكْلِهَا مَا لَمْ يَعْلَمُوا.
Ya zo cikin Nawadir na Rawandi, da isnadinsa zuwa kan Musa Bn Ja'afar, daga iyayensa (A.S) yace: An tambayi Aliyu (A.S) game da qunshi (roll) da aka samu akan hanya wanda cikinsa akwai Nama mai yawa da Gurasa mai yawa da kuma Qoyi tare da Wuqa a cikinsa. Yace;
" YA TANTANCE ABINDA KE CIKINSA SANNAN YACI, DOMIN SHI YAKAN IYA LALACEWA. IDAN KUMA MAI NEMANSA YAZO ZAI BIYA SHI."
Sai akace masa: " Yaa shugaban muminai ! Ai bamu sani ba, qullin na ma'abota addini ne ko kuma na Majusawa ne." Sai yace;
" SU A LOKACIN ZA SU IYA CINSA MATUQAR DAI BASU SANI BA."
نوادر الراونديّ ص 50.
Cikin wannan hadisi kuma yana nuna mana ne cewa duk wani abu naci wanda aka san yana iya baci/lalacewa ba a ajiye shi don yin cigiya. Ya halatta aci don kada a barshi ya lalace. Amma saboda shi ba a cigiyarsa kuma ana biya, shi yasa akace a tantance menene-da-menene ke cikinsa, domin in mai shi yazo za a biya shi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
12th August, 2021/ 3rd Muharram, 1443.