@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RASHIN YARDA DA WANNAN YA JEFA AL'UMMAR MUSULMI CIKIN RUDANI
Ni dai banga girma ko daraja ba ga wanda zaiyi kunnen uwar shegu game da maganar fiyayyen halitta (S.A.W.W), alhali koyi dashi da kuma bin umarninsa shine imani.
Al'ummar musulmi sun fada cikin wani mummunan yanayi mai halakarwa ba wai na quncin rayuwa ba, domin sun sami kansu cikin gaba da juna da kuma yaqar gaskiya da ma'abotanta. A duk lokacin da wata murya ta taso mai qoqarin rayar da tafarkin Allah na gaskiya wanda fiyayyen halitta yazo mana dashi kuma ya barmu a kansa sai kaji ko kaga miyagun mutane wadanda suka shiga rigar addini kuma suke gani tamkar sune addinin suna yaqar masu yin addini na gaskiya ta kowacce fuska.
Annabi (S.A.W.W) ya tabbatar mana da cewa Khalifofi a bayansa wadanda za su jagoranci wannan al'umma su goma sha biyu (12) ne.
Amma wani abin takaici mafi yawan mutane sun tafi ne kan cewa su hudu (4), domin cutar da muslimcin da magabata suka yiwa addinin. Wannan kuwa shine cin amanar Manzon Allah (S.A.W.W) da kuma yin tawaye ga Allah wanda ya umarci Annabi (S.A.W.W) da ya sanar da al'ummarsa wannan al'amari.
Ya zo cikin riwayoyi ingantattu dake tabbatar mana cewa Halifofi 12 ba 4 ba a bayan Manzon Allah (S.A.W.W), gasu kamar haka:-
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
باب الْمَهْدِيِّ:
4281- حَدَّثَنَا عَمْرُو بْنُ عُثْمَانَ حَدَّثَنَا مَرْوَانُ بْنُ مُعَاوِيَةَ عَنْ إِسْمَاعِيلَ- يَعْنِي ابْنَ أَبِي خَالِدٍ- عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَابِرِ بْنِ سَمُرَةَ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: ((لاَ يَزَالُ هَذَا الدِّينُ قَائِمًا حَتَّى يَكُونَ عَلَيْكُمُ اثْنَا عَشَرَ خَلِيفَةً كُلُّهُمْ تَجْتَمِعُ عَلَيْهِ الأُمَّةُ)). فَسَمِعْتُ كَلاَمًا مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمْ أَفْهَمْهُ قُلْتُ لأَبِي مَا يَقُولُ قَالَ: ((كُلُّهُمْ مِنْ قُرَيْشٍ)).
Iman Dawud yace, Amruu Bn Usmana ya bamu labari, Marwan Bn Mu'awiyyata ya bamu labari daga Isma'il, yana nufin Ibn Abiy Khalidin, daga babansa, daga Jabir Bn Samrata yace: Naji Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;
" WANNAN ADDINI BA ZAI GUSHE BA YANA TSAYAYYE HAR SAI KHALIFOFI 12 SUN KASANCE A KANKU, DUKKANSU AL'UMMU ZA SU HADU A KANSA ."
Sai naji wata kalma daga Annabi (S.A.W.W) wacce ban fahinceta ba, sai na cewa banana, me ya fada ne? Yace:
" DUKKANSU DAGA QURAISHAWA SUKE."
(Sunan Abu Dawud, hadisi mai lamba 4281)
Cikin wannan hadisi za mu fahinci cewa, Khalifofin muslimci dai guda 12 ne, duk wanda yace 4 ne, to, ba na muslimci bane.
4282- حَدَّثَنَا مُوسَى بْنُ إِسْمَاعِيلَ حَدَّثَنَا وُهَيْبٌ حَدَّثَنَا دَاوُدُ عَنْ عَامِرٍ عَنْ جَابِرِ بْنِ سَمُرَةَ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: ((لاَ يَزَالُ هَذَا الدِّينُ عَزِيزًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً)). قَالَ فَكَبَّرَ النَّاسُ وَضَجُّوا ثُمَّ قَالَ كَلِمَةً خَفِيَّةً قُلْتُ لأَبِي يَا أَبَةِ مَا قَالَ قَالَ: ((كُلُّهُمْ مِنْ قُرَيْشٍ)).
Imam Abu Dawud ya qara cewa; Musa Bn Isma'il ya bamu labari, Wuhaibu ya bamu labari, Dawud ya bamu labari saga Ameer daga Jabir Bn Samrata yace: Naji Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;
" WANNAN ADDINI NA ZAI GUSHE BA YANA MADAUKAKI HAR ZUWA KAN HALIFOFI GOMA SHA BIYU (12)."
Yace, sai mutane suka yi kabbara suka jinjina ! Sa'annan ya fadi wata kalma boyayyiya (gare ni). Sai na cewa babana, yaa banana ! Me ya fada ne? Yace:
" DUKKANSU DAGA QURAISHAWA NE ."
(SUNAN ABU DAWUD, BABUN MAHDI, HADISI MAI LAMBA 4282)
To, ni dai a yanzu ban san wata hujja wacce zan bawa wani ba in har nace Khalifofi hudu (4) a bayan Annabi (S.A.W.W), sannan kuma banga wata hujjar da wani zai bani ba in yace ba goma sha biyu (12) bane Halifofin Manzon Allah (S.A.W.W).
Wannan dalili na kaucewa maganar Annabi (S.A.W.W) ne yayi sanadin cewa al'ummar musulmi cikin rudani. Da ace kowa ya yarda da maganar tasa haqiqa da babu wannan sharrin daya addabi al'ummar musulmi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
27th August, 2021/ 19th Muharram, 1443.