Daga: Faruq Sani Kudan (Aba Jidda)
To shi kuma Bature loƙacin da ya zo, waɗansu sun yi murna da zuwansa, ganin cewa ya hana zalunci na sarakuna. Amma ba su san ya zo da zaluncin da ya fi na wanda ake musu ba. Na'am ana zaluntar su, amma Allah (T) yana cewa; "Innal shirka la zulmin azim" wannan wasiyyar wani babban Malami Hakim, ga ɗan sa, "Ya bunayya la tushrik billah, innas shirka la zulmin azim" ainihin kafirci ya fi zalunci ƙarfi, saboda shi kuma asasin sa rashin yarda da Allah ne.
Saboda haka shi kuma Bature ya zo da wani asasi ne na rashin ruwa da addini, na kawar da addini a asasin da yake. Da yake shi a can a in da yake, ya samu juyi, wanda ya yi wa sukurkutaccen addininsa tawaye, ya ɓalle, sannan ya samu kansa. Saboda haka, bayan ya ɓalle daga addinin ne, don da can su ma addinin ne ke mulki, amma addinin wanda yake fanɗarrare,.
Saboda haka, sai ya zama ya kafa musu ƙaimi, sai da suka yi tawaye gare shi. Su kuma sai ya zama yanzu, an raba addini da Siyasa, mulki daban, addini daban. To a shigen irin wannan ya zo mana da shi, kuma ko shakka babu, babban abin da yake tsammani, imma akwai 'Danger' da zai fuskanta shi ne daga Musulunci. Saboda haka shi yana ganin lallai ne, ya danne musulunci nan, ya gama da shi.
Yadda ba zai taɓa ɗagowa ya zama ya yi mulki ba. Shi ma mulkin ya dame su, kamar yadda su ma waɗannan sarakai mulkin ya dame su, to shi kuma dama yana da jin tsoron addini. Alal misali, akwai misalsalsi da zan iya bayarwa, kuma da yake dai nan ba muhallin su bane.
''Muna so mu dawo gida ne. Amma za mu iya bada misali, akwai batun da aka ce, wani Baturen mulkin mallaka, Yana rangadi akan Doki a ƙasar Misira, to sai ya wuce Masallaci, ta gaban Masallacin yana wucewa, sai Ladan ya kwantsama kisan sallah. An ce ya tsorata sosai, ya firgita sosai. Sai ya ce ma ɗan Jagoransa, wannan me yake cewa? Sai ya ce yana kiran mutane su zo su yi sallah ne.
Sai ya ce, ya shafi mulkin mu? Ya ce a'a, kawai yana kiran mutane su zo su yi sallah ne, ya ce tun da bai shafi mulkin mu ba, shikenan. Ko menene ya je ya yi ta yi.
Cikin Jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da ya yi fira da wasu yan Jarida