Wata Sabuwa:- Wasu Abubuwan da Suka Biyo Baya a Bayan Zaman Mukabala da akayi a Kano..!!

 


KO KUNSAN ABUBUWAN DA SUKA BIYO BAYA A BAYAN ZAMAN MUKABALA DA AKAYI? KUBIYONI



Akwai tambayoyin da wasu al'umma ke yi kamar haka:


*Me yasa Malaman jahar kano sukaki yarda ayi zaman mukabar tun farko? Haka kuma Meyasa gwamnati taki yarda ayi zaman mukabala shima tunda farko kamar yadda aka tsara za ayi?*


*Me yasa gwamnati zata sa alkalin mukabala wanda akasan yana da bangare?* Bayanai sun tabbatar cewa alkalin dan izalane basalafe shin meyasa gwamnati bata sa dan ba ruwan muba kamar yadda suma bazasu yarda asa dan shi'aba? Me yasa za asa shi shikai dai me makon ace rukunin maluma?(that is injustice)


Shin meyasa gwamnati bata cika alkawarin da ta daukarwa al'umma cewar zata Yada abun anan kai tsaye karshe akaki yin haka?.


Haka kuma wasu naganin cewar mutum zai iya karanta tambaya a minti biyu amman amsar tambayar zata iya kaiwa muntina talatin ko sama da haka kamar yadda aka saba a makarantu. meyasa basu kara masa muntina ba? Wasu na ganin cewar da malaman jahar kano sun san sunfishi gaskiya da su da kansu zasu karawa masa lokaci sukuma dauki mas'alar nan daya bayan daya kamar yadda malamin ya bukata amman suka kaki domin wasu naganin cewar lallai sungama tsaretsarensu yadda ya kamata.


Haka kuma wasu naganin cewar maganar malam abdullajabbar gaskiyane akwai miyagun hadith acikin litattafan musulmi domin mlmin ya kawo wasu hadith amman malaman duk sukarsu basu musuntaba duba da cewar malaman hadith nai wanda a wajan maluma sun inganta.


 sai Wasu mutane kecewa ai shi korewa yake ba tabbatarwa da annabi yakeba. Bakamar yadda aka gayamusu da farkoba. Da hakane kamata yayi ace dashi ya gyara usulubin ko yarwarsa amman ba a ce yana zagin annabiba.


 Haka kuma wasu nacewa ai babu inda mlmin yace wadannan kalmomi da ya ambata babu inda yace ya na cikin wadannan hadiths da malamai masu wakiltar malaman kano suka karanta babu inda malamin yace su wadannan kalmomi na ciki wannan hadith da malamai suka ambata a wajan zaman.


Abu na karshe kamar yadda akaji malamin abdljabbar yana fada yace da yasan yadda aka tsara mukabalar nan kuma a minti goma za'abashi dama yayi magana ba zai dauko littafai sama da 500 ya taho dasu wajan mukabalar nan ba Da kawai sai ya takaita abubuwan a takarda.


Sabo da haka kamata yayi ace anbawa malamin ishasha lokaci dan idan har bashi da gaskiya a kuremasa gudu idan kwanikan sunyi kadan akara saka wannnan rana domin har yau su maluman jahar kano babu wanda ya musanta cewar hadith ba wai babu subane akwai su kuma sun inganta to sabo da haka kamatayayi a zauna a fitar da wadannan muyagun hadiths domin samarwa da addini mafita domin girmama annabi (sawa)


By Habibu Rabiu Nasrallah.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Kaunarsa suka Kara Mana Kuma wallahi tallahi shine ya kaisu kasa game ilimi ko mai hankali saboda su bayaddar Allah suke nemaba yaddarsu tanaga awamu shikuma me gaskiya Kuma yafi karkatane zuga yaddar Allah, wallahi tallahi bazan kasance mabiyin San zuciyaba ko masu kulla makirci domin nasara

    ReplyDelete
Previous Post Next Post