Daga shafin, Umar Hassan Gololo
Yadda muke jin muryar Miyagun Malamai makiya Allahu Ta'ala kuma karnukan azzaluman Nigeria suna nuna bakin ciki da takaicin yadda Almajiransa suke bayyana zaluncin da aka masa a Zaria, haka suka rinka bada fatawar a dirarwa Malam Zakzaky(H) da Almajiransa saboda a dakatar da yaduwar Shi'a a Nigeria.
Wadannan Miyagun Malaman sun nuna zunzurutun kiyayya da hassada akan Malam Zakzaky(H) da da'awarsa, sun bayyana takaici da ganin yadda al'umma suke tururuwa garin Zaria domin gudanar da Mauludi da Tattakin Arba'in da sauran tarukan Ashura.
Duk mai arzikin hankali da tauhidi ya san lamarin Malam Zakzaky(H) daga Allahu Ta'ala ne ba wayo ko dabara ba.
Don haka muke yiwa azzaluman Nigeria da karnukansu Wallahi duk mai yunkurin ganin bayan Malam Zakzaky(H) da da'awarsa sai ya riga rana faduwa Insha Allahu Ta'ala.
Muna rokon Allahu Ta'ala ya gaggauta kawo karshen azzaluman Nigeria da karnukansu Miyagun Malamai, alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi wa Sallam...