@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DOLE KA YABI WANDA ALLAH DA MANZONSA (S. A. W. W) YA YABE SHI
A cikin kowanne irin yanayi sai Allah (T) ya bayyanar da wani matsayi ko karamci ko fifiko na wasu daga cikin bayinSa.
Yaqin Badr shine yaqi na farko wanda aka fare shi cikin muslimci yayin da Allah (T) ya umarci musulmai da cewa su tashi su kare kansu daga yaqar da kafirai ke yi musu.
Yana daga cikin dabi'ar larabawa na yaqi a duk lokacin da suka fuskanci juna (physical combat) akan sami jarumai ne na yankan shakku su fito daga kowanne bangare a gwada qarfi, daga nan ne ake iya gane nasara ko rashin nasarar yaqin.
Abinda ya faru kenan ma cikin wannan yaqi kamar yadda za mu kawo muku cikin nassi.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
باب في الْمُبَارَزَةِ:
2667- حَدَّثَنَا هَارُونُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ حَدَّثَنَا عُثْمَانُ بْنُ عُمَرَ أَخْبَرَنَا إِسْرَائِيلُ عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ عَنْ حَارِثَةَ بْنِ مُضَرِّبٍ عَنْ عَلِيٍّ قَالَ تَقَدَّمَ- يَعْنِي عُتْبَةَ بْنَ رَبِيعَةَ- وَتَبِعَهُ ابْنُهُ وَأَخُوهُ فَنَادَى مَنْ يُبَارِزُ فَانْتَدَبَ لَهُ شَباب مِنَ الأَنْصَارِ فَقَالَ مَنْ أَنْتُمْ فَأَخْبَرُوهُ فَقَالَ لاَ حَاجَةَ لَنَا فِيكُمْ إِنَّمَا أَرَدْنَا بَنِي عَمِّنَا. فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((قُمْ يَا حَمْزَةُ قُمْ يَا عَلِيُّ قُمْ يَا عُبَيْدَةُ بْنَ الْحَارِثِ)). فَأَقْبَلَ حَمْزَةُ إِلَى عُتْبَةَ وَأَقْبَلْتُ إِلَى شَيْبَةَ وَاخْتُلِفَ بَيْنَ عُبَيْدَةَ وَالْوَلِيدِ ضَرْبَتَانِ فَأَثْخَنَ كُلُّ وَاحِدٍ مِنْهُمَا صَاحِبَهُ ثُمَّ مِلْنَا عَلَى الْوَلِيدِ فَقَتَلْنَاهُ وَاحْتَمَلْنَا عُبَيْدَةَ.
Haruna Bn Abdullahi ya bamu labari, Usmana Bn Umar ya bamu labari, Isra'ila ya bamu labari daga baban Ishaq, daga Harithata Bn Mudharrabi, daga Aliyu yace : Ya gabata, yana nufin Utbata Bn Rabi'ata, sai dansa da dan'uwansa suka bi shi. Sai yayi kira da cewa; " Wanene zai iya qwamawa dasu ?"
Sai wasu matasa daga mutanen Madinah (Ansar) suka miqe. Sai yace: " Ku su waye ?" Sai suka ba shi labari (suka ambaci kansu). Sai yace : " Ba mu da buqata daku ! Abinda muke buqata shine 'ya'yan Ammominmu (don su muka san jaruntakarsu) . "
Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" MIQE YAA HAMZA ! MIQE YAA ALIYU !! MIQE YAA UBAIDATA BN HARITH !!! "
Sai Hamza ya fuskanci Utbata (ya kashe shi) , ni kuma na fuskanci Shaibata (na kashe shi) . Shi kuwa Ubaidata da Walid aka sami sabanin sara guda biyu , kowanne daga cikinsu ya imma dan'uwansa, sannan nakai farmaqi akan Walid na kashe shi ! Kuma dauki Ubaidata (cikin mummunan rauni wanda yayi sanadin shahadarsa) ."
(SUNAN ABU DAWUD, KITABUL-QITAL, BABI WANDA YAYI MAGANA KAN QWAMI (mubaraza), HADISI MAI LAMBA 2667)
Wadannan mutane uku sune jaruman da Annabi (S. A. W. W) ya yarda da jaruntakarsu wadanda za su fitar musulmai da muslimci daga cikin qasqanci.
Tun daga wannan qwami ne aka sami budi yadda a qarshe aka kashe mutane 70 aka kama 70 daga cikin kafirai a matsayin fursunonin yaqi.
YAA ALLAH KA BAMU JARUNTAKA DA MAKOMA IRIN TASU 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda
(08137925034)
24th June, 2021/ 14th Zul-Qadah, 1442.