@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @
WANDA YA RIYA CEWA ALIYU NE YAFI CANCANTA DA WILAYA NA NUNA CEWA ABUBAKAR DA UMAR SUNYI KUSKURE
Mafi yawan maganganun magabatan malaman Sunnah babu hikima ko nazari, shi yasa kake ji ko kake ganin tufka-da-warwara cikin maganganun nasu dake fitowa cikin manyan littattafan da suka inganta su.
Yanzu za kaji sun fadi magana sun ingantata, san nan ka qara ji sun kawo wata magana wacce ke cin karo da wannan maganar tasu kuma su qara ingantata ba tare da nazarin rushe maganar farkon da suka yi ba.
Idan kuwa ya zamana mutum zai yi magana sannan yazo ya rusa ta da bakinsa za mu iya cewa ba shi da nazari. Sun kawo cikin littafan nasu cewa Annabi (S. A. W. W) yace Khalifofi a bayansa 12 ne, amma kuma sai su kawo 4 wai cewa sune shiryayyu, kenan 8 din da ya fada ba shiryayyu bane a wajen su.
Ban taba ji ko ganin inda aka ce wai Khalifo 5 bane cikin littafan Sunnah sai yau da nake nazari cikin Sunan na Abu Dawud sannan naci karo da wasu hadisai kamar haka.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
4632- حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ مِسْكِينٍ حَدَّثَنَا مُحَمَّدٌ- يَعْنِي الْفِرْيَابِيَّ- قَالَ: سَمِعْتُ سُفْيَانَ يَقُولُ مَنْ زَعَمَ أَنَّ عَلِيًّا عَلَيْهِ السَّلاَمُ كَانَ أَحَقَّ بِالْوِلاَيَةِ مِنْهُمَا فَقَدْ خَطَّأَ أَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ وَالْمُهَاجِرِينَ وَالأَنْصَارَ وَمَا أُرَاهُ يَرْتَفِعُ لَهُ مَعَ هَذَا عَمَلٌ إِلَى السَّمَاءِ.
Muhammad Bn Miskin ya bamu labari, Muhammad ya bamu labari, abin nufi Al-Firyaabiyyi yace : " Na ji Sufyan yana cewa;
" DUK WANDA YA RIYA CEWA LALLE ALIYU AMINCI YA TABBATA A GARE SHI SHINE MAFI CANCANTA DA WILAYA DAGA CIKINSU (Abubakar da Umar), TO, HAQIQA YA NUNA CEWA ABUBAKAR DA UMAR DA MUHAJIRUNA DA ANSAR SUNYI KUSKURE (da basu bashi wannan haqqin nasa ba), NI KUWA BANA GANINSA (mai wannan ra'ayi ko fahinta) ZA A 'DAUKAKA MASA (ayyukansa) TARE DA WANNAN AIKI (da yake riyawa) ZUWA SAMA ."
Abin nufi anan shine, shi Safyanul Sauri yana nunawa ne cewa duk wanda yayi wannan furuci na cewa Imam Ali (A. S) shine da haqqi, to, ba za a daukaka ayyukansa na aikhairi zuwa sama ba. Idan kuwa ya zamana haka, to, ya nuna cewa kashi 90% na Sahabbai ba za a karbi ayyukansu ba, domin kuwa sun san wannan haqqi na Imam Ali (A. S) ne, su dai kawai suna ga cewa shi yaro ne bai kamata ya jagoranci Dattawa ba.
Cikin hadisi na gaba kuma ya qara cewa;
4633- حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ فَارِسٍ حَدَّثَنَا قَبِيصَةُ حَدَّثَنَا عَبَّادٌ السَّمَّاكُ قَالَ: سَمِعْتُ سُفْيَانَ الثَّوْرِيَّ يَقُولُ الْخُلَفَاءُ خَمْسَةٌ أَبُو بَكْرٍ وَعُمَرُ وَعُثْمَانُ وَعَلِيٌّ وَعُمَرُ بْنُ عَبْدِ الْعَزِيزِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ.
Muhammad Bn Farisi ya bamu labari, Qabisata ya bamu labari, Abbadu As-Sammaku ya bamu labari yace; " Na ji Safyanul Sauri yana cewa;
" KHALIFOFI GUDA BIYAR (5) NE. ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN DA ALIYU DA KUMA UMAR BN ABDUL-AZEEZ. "
(Sunan Abu Dawud, Babun fee Tafdheel, Hadisi mai lamba 4632 da 4633)
Uhmm, na san ko kai mai karanta wannan magana baka taba jinta daga bakin wani malami ko ganinta a rubuce ba sai yanzu. Ga ta kuma cikin daya daga ingantattun littafai shida (6) na Sunnah aka kawo.
TAMBAYA
-------------------------------------------
Yanzu idan muka taqaita kan magana biyu, wato mai cewa Khalifofi shiryayyu guda hudu (4) ne da wannan mai cewa su biyar (5) ne, dan Allah wannene za kace gaskiya daga cikinsu ?
Menene hujjarka daka zabi daya (1) daga cikinsu kace shine gaskiya alhali dukkansu babu wanda yazo daga Manzon Allah (S. A. W. W) ?
Bamu yi tambaya game da wanda yace su sha biyu (12) ne ba saboda mun san shi daga Annabi (S. A. W. W) ya fito.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
1st June, 2021/ 21st Shawwal, 1442.